Babi Na Daya

3.4K 148 93
                                    

A duk lokutan yanayi na shekara, babu irin wanda Fatima ta tsana irin wanda a ke ciki a lokacin, wato yanayin zafi musamman idan ta na garin Gombe ne.

Duk da cewar a garin Bauchi ta ke da zama, ta kan kiyaye zuwa Gomben ne musamman a watan Afirilu.

Karfe tara ne da kwata na safe, amma wani irin tiririn dake hade da iska mai zafi-zafi suka buso. Fatima ta samu kan ta cikin fifita da jakar fayel din da ke hannun ta. Yanzu ma ke nan. Anjima kam sai dai a gasa naman saniya a waje idan rana ta haura tsakiya.

Kai tsaye ta shiga fannin turanci na makarantar Gwamnatin Tarayya ta horar da Malamai da sana’a, wurin da ta ke iya ganin jerin kofofi a gaban ta har karshen ginin, wadanda ke da allon rubutun lambobi a makale ta saman su.

A can karshen kwaryar ginin ne ta lura da wadda ke bude, don haka ta nufe ta, tun da ga alamar mutum a ciki.

Babbar farfajiya ce, wadda ke dauke da kujerun zama don ma su jiran wanda su ka zo gani, gami da makeken teburin da ke girke a gefe guda.

Wurin tsit yake, idan a ka dauke wata macen da ke zaune kan kujera ta bayan teburin, ta na yankar farshen ta da abin yankawa.

Fatima ta nufi wurin ta, ta manna murmushi a fuskar ta, sannan ta gaishe ta. Matar ta dago ta kalle ta, iskar fankar tsaye ta na busa ta a hankali.

Ba za ta wuce shekaru arba’in ba ko da biyu, don ta dan manyanta. Sanye ta ke cikin atamfa mai ruwan kasa da ja a garwaye. Kan ta babu lullubi, amma ta rataye babban gyale a kafadar ta.

Fuskar ta fayau, ta tambayi Fatima, “Yes, me zan iya mi ki, ‘yan mata?” Muryar ta dauke da sassauci, don kuwa ba za a iya cewa fara’a ba ce. Hakan ya fitar da sautin harshen ta na wa ta kabila. Ko Tangale ko kuma Waja.

“Na kawo takardun da a ka bani na posting zuwa nan department din ne.”

Ta ci gaba da yankar farcen ta, “Mu ga takardun?”

Bayan Fatima ta mika ma ta ta karba, ta ci gaba da cewa, “Ina kike ne lokacin da sauran ‘yan uwanki ma su hidimar wa kasa suka zo tun makon jiya?”

Tambaya ce da Fatima ta ga babu amfanin amsawa, tun da ta yi ma ta ita ne ba tare da nuna alamar son jin amsar ba daga gare ta.

Matar ta mika mata takardun, fuskar ta fayau din dai kamar tun farko, ta ce, “Ki samu wuri ki zauna. Yau a na babban taro na wayar da kan sabbin dalibai(Orientation Programme) tare da shuwagabannin makarantar nan. Don haka kafin ki ga mai ganin ki zai dauki lokaci.”

Fatima ta gyada kan ta, sannan ta samu wuri ta zauna. Ba ta da wani zabi. Tun da matar ba ta kore ta bama ta auna arziki.

Duk da cewar ba FCE Technical, Gombe ta yi nufin zuwa hidimar kasar ta ba, ba za ta so damar ta wuce ta ba. Karewa ma, ba ta so zuwa Gomben ba ma, don ta fi son ta zauna a Bauchi, wajen Nanar ta, ta ci gaba da kula da ita.

Sai dai Yaya Bello ne ya matsa kan lallai sai ta je ta yi, cewar Bauchin da Gombe duk daya ne.

Da farko har za ta yi gardama, amma sai Nana ta saka baki kan lallai ta hakura. Ba ta son zama a gidan Yaya Bello ko da na minti daya ne. Amma bisa dole ta hakura. Ashe dai zuwan na ta zai ma sa amfani.
Don ba don ita ba, da Yayan nata ya shiga mummunar halin da ya fi wanda ya ke ciki a yanzu. Hakika ya auna arziki, kuma Allah dai Ya takaita mu su wahala baki daya.

Tun bayan komawar ta gida daga sansanin horon ma su yin hidima wa kasar da ke Malam Sidi, suka ruga da shi asibiti. Sannan duk da dai ba su kwana ba, kusan kullum suna tsaye a kan sa. Karshe ma dai likitan ya rike shi a jiya laraba a nan babban asibitin Gomben, don sanin matakan da zai dauka dangane da abin da ke damun sa.

Gurbin Zuciya Where stories live. Discover now