babi na biyar

936 83 3
                                        

A can gidansu kuma, hajiya na tsaye a kofar gida tana baza idanu ta ga ta inda zasu bullo. Daga nesa ta hangesu su uku suna tafiya, baki ta soma washewa tana tunanin murja tayo babban kamu. Ita kuma intee tana hango hajiya aka fara kidan kalangu a zuciyarta, shikenan yau nayi wa duniya adabo dan kuwa hajiya gutsuttsura nama na zata yi tayi farfesu dani, ta ayyana a ran ta.
  Suna karasawa hajiya aka hau yiwa yayan Aysha bambadanci, shi kuwa ya tamke fuskar shi kaman hadari ya hado ta gabas. Gaisheta yayi cike da ladabi ita kuma hajiya ta ansa tana cewa sannu da zuwa dai alhaji, ta dubi intee tai mata wani irin kallo tace gantalalliya ba abinda kika sani sai yawo. To sai ki wuce mu basu waje. Kan ta rufe baki ya ma yi juyawar shi. Ita kuwa murja sai tafasa take kan ta na hayaki. Ta dubi uwar tace ke hajiya kita wani yi mishi rawar jiki, akan waccan nunan ranar fa ya ringa mari na sai kace ya samu jaka. Fuskar hajiya nan da nan ta sauya kamar masifaffiyar zakanya.
Juyawa tayi ta sabi hanyar da yayi. Bin ta murja tayi tana wallahi da kin dawo kin ji da karamar alhakin can. Dan wallahi wancan yafi ki iya rashin mutunci yasin. Aikuwa juyawa tayivda sauri tai cikin gidan.
  Kina ina 'yar abu ta kazan uba (wa'iyazubillah). Bayan maita har gulma da munafurci kika iya? Hqka fa dazu kika hada ni da anas kan ya fita, yau kuwa sai kinci ubanki. Mikewa tayi daga kan yagalgalalliyar katifar ta tana ja da baya, kafin ta sake wani yunkurin ta finciko ta ta zuba mata mari, dukan ta take kamar Allah ya aikota, da kyar ta samu tai waje da gudu murja tayi wuf ta kuma tunkudeta ta fadi, hajiya kuma ta sa kafa ta take mata wuya, ta dubi murja tace karasa cin uwarta. Murja ta hau ruwan cikinta ta fara jibgarta. Ji tai an fincikota an yi gefe da ita. Kashe ta zakuyi ne? Cewar anas kenan, haba hajiya ku runga sassauta mata mana. Hajiya ta juyo a fusace ta ce mishi wannan yarinyar algunguma ce. Sa wa tayi yayan wannan figalalliyar kawarta ta yai wa murja duka. Ya juyo ya dubeta yace haj kenan! Murja ai dama bata da kunya, murja ko ta fusata tace rashin kunya a wajen uwarka na gada. Ke!!! Ya daka mata tsawa wallahi ki shiga hankalinki ko nai miki eh yane billahillaziiii... hajiya tai maza ta shiga tsakani dan ta san hali kar ya lahanta mata yarinya..ta tasa murja sukai daki. Ita kuma intee a yashe tana wani irin gunjin kuka mai ban tausayi. Duk da a cikin maye yake bai hana shi daga ta ba dan kuwa kakkarfan namiji ne. Kokarin turjewa take amman ta kasa. Ya kaita dakin ta ya kwantar da ita. Fita yayi ya je chemist din da ke kallon kofar gidansu ya siyo mata magunguna yazo ya bata ya lallabata ta sha. Suk da tsanar shi da tsoron ahi data keji sai da taji dadi..ta kalleshi ta ce nagode. Murmushi yayi yace mata baby in kika daina min rashin kunya zaki ji dadi..ki koyi yi min biyayya fyn bby, ya fada mata cikin muryarsa ta gogaggen dan shaye2

🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏🍏

Fitaccen gidan mata ne a kusa da unguwar sabon gari. Kabilu iri iri ne da mutane kala kala, gidan ya kaure da hayaniya, masu karta nayi, masu kalangu na nasu, gefe kuma dandazon maza da mata ne da maza suna aikata masha'a. Can gaba kuma wasu ne sun hadawa sararin samaniya go slow da hayaki, ana ta fesar da hayakin taba dana shisha, haka kuma, masu shan giya da sauran miyagun abubuwa nayi.

Wata matashiya baka me jiki ke tafe da ita da wani mutum dan fari haka, da ganin shi ya fara manyanta, ya riko mata kugu suna tafe suna murmusawa, masu kidan kalangu kuwa suna ganin su suka sauya kida suna wake  saratu 'yar dagwas da goganta alhaji buba. Nan ta zage tana bin kidan nan kamar anyi shawara da ita wajen tsara kidan. Rawa take tsakanin ta da Allah gwanin sha'awa ko ina na sassan jikinta tana bashi na shi hakkin. Shi kuwa gogan nata murmushi yake a yana takawa da tulelen tumbinsa da ke taya shi. Sa hannu yayi aljihu ya dibo kudin da bai san adadinsu ba ya hau lika mata, ita kuwa 'yar dagwas kamar kara zuga ta yake yi.
Shi kuwa maroki nan ya hau koda su yana cewa alhaji buba na saratu sukari ba kai farin banza ba, dawisu naman ka sai sarakuna buhun qaya dannaka sai an shirya, buhun barkono ko wa ya rungumoka ya ji jiki. Ai kuwa ya juya kan marokin nan yana bashi na ahi rabon. Kan ka ce kwabo kallo ya koma kan su, haka jama'ar gidan kowa ya zo yana kallon su ana ta sharholiya.
Ana cikin sha'ani biki yayi biki, sai ga wata yarinya kyakkyawar gaske, fara tas, shapr dinta shi ne wanda ake cewa coca cola shape. Ta sha wasu arnakun kanann kaya riga da wando..da kyar rigar ta rufe mata cibiyarta. Wandon kuwa dogo ne, pencil ya sha yaga. Tana shigowa gida ya hau hargowa ana fadin ga kyau a mazaunin shi. Asalin sunanta Aisha ne, amma da ta shiga bariki ta maida sunanta kyau, su kuma 'yan taya bera bari suka karasa mata da kyau a mazaunin shi. Alhaji buba kuwa nan kananun jajayen ido suka zazzaro kamar an dora shi a shocking. Bin ta kawai yake da kallo yana ganin yanda take karya jiki. Bai san yanda aka yi ba sai ga shi a gabanta yanai mata ruwan naira. Ita kuma batai kasa a gwiwa ba ta cigaba da takawa. 'Yar dagwaa kuwa tafasa kawai ta ke tana konewa. Ta zabura ta finciko kyau ta fara jibgar ta, alhaji buba ya shiga tsakani yana ture 'yar dagwas, ruwan balai kawai take tana ci musu mutunci.
Alhji buba ne ya daka mata tsawa yace ke!!! Ji nan, bana son hauka fa. Kin ci naki rabon a yanda kike din nan sai ki bari yarinya ma ta ci nata. Asali ma dai na ga ta fiki cancanta a wannan matsayin ita kuwa kyau sqi tauna cingam take tana yatsine da harare2, ta dube shi tace baby mije ka kyale kucakar nan. Kaima ka san tun farko ba ajinka bace. Ya sake washe bki yace rabu da ita muje hotel sai mun fi hutawa. ( bariki kenan! Dazun nan da 'yar dagwas ake yi yanxun nan kuma an canja) ita kuwa sai tafarfasa take tana huro hanci. Ta dubi yarinyar tace da ita zaki sani ne sai kin san ni kika taka.
Wannan kenan!
❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Hello lovey dovies, da fatan labarin yana dadi. Ayi hakuri da rashin ji na da ba ayi..in shaa Allah zan dinga updating akai akai..pls keep voting and commenting.

DUNIYA MAKARANTAWhere stories live. Discover now