Misalin Karfe Hudu da rabi Habeeb da Kannensa Ihsan da Nusaiba ne a zaune Suna fira, yana tambaya gameda karatunsu. Nusaiba dai tana ajin karshe ne a babbar makarantar sakandare tana S.S III. ita tana karatu ne a makarantar gwannati, Su kuwa Ihsan da Affan suna karatu a makarantu masu zaman kansu. Affan ne karaminsu ita kuwa Nusaiba itace ke biwa Habeeb. Baifi tsawon dakiku goma sha biyar da fara firan nasu ba sai sukaji alamar ana sallama a cikin gidan Ihsan itace ta tashi domin ganin wanda yake sallamar. Tana fitowa sukai arba da Zahra'uh. Ruguwa tayi a guje tare ambaton "Oyoyo anty, Oyoyo...", suka rugume juna cikin farin ciki. Ina fatan ummah na ciki ko?, Ihsan tace ah'ah ta dan shiga makauta amma yanzu tana hanyar dawowa, Amma yaya Habeeb yana ciki. Yaushe Ya habeeb din yazo?, inji Zahara. Sannan Ihsan tace about Two weeks. Jim kadan Ihsan ta dauki kayan anty Zahra'uh suka shiga ciki. Kowa yayi murna da zuwan Zahra'uh, musamman Ummah data dawo.
Washe gari Nusaiba ta hada masu tea sukai karin kumallo, sannan ta sanya uniform don zuwa makaranta, umma ce ta bata kudin taxi domin a kwai nisa makarantar. Ita kuwa Ihsan zumudin anty zahra'uh ya hanata shakat akan gudanar da aiki kamar yadda ta saba, don haka ko shirin zuwa school batayi ba. Akwai shakuwa mai yawa tsakanin Zahra'uh da Ihsan fiyeda kowa. Ko shima Habeeb dole yabasu fili a yanzu. Duk da cewa Habeeb da Zahra'uh sun shaku matuka, amma yanzu sai Ihsan ta soma mamaye zuciyar zahra. Soyayyar Habeeb tana kokarin shammatar zuciyar zahra'uh, amma taki bayyana hakan. Habeeb Ya cika mako ukku a gida kuma yanason komawa makarantar su mako mai zuwa.
YOU ARE READING
KAINE MURADINA
General Fiction#KAINE MURADINA. Labarine akan wasu masoya guda biyu wayanda soyayya ta rusa dasu a sanadiyar rayuwar makaranta. Habeeb Saurayi matashi, yanada kannai guda ukku, wato Ihsan, Nusaiba, dakuma Affan. A bangare daya kuwa, Elizabeth Joshua matashiya ce...