41: Haske maganin duhu

6.9K 645 65
                                    


"Duk labarin da ka bani ban ga kwakkwaran dalilin da zai sa ka saki matarka ba." Fad'an Baban Anwar kenan cikin fushi.
"Baba tun ba yau ba Nazifa take min rashin kunya take min duk abunda ta ga dama. Haka zata fita unguwa ba da sanina ba, idan na mata magana sai ta biyoni da bak'ar magana. Tun kafin wannan abun ya faru na mata katanga da gidan amma haka ta tsallake umarnina ta fita." Anwar ya fad'a duk don kare kanshi saboda yanda ya ga Babanshi ya fusata.
"Yaushe abun ya faru?" Baba ya tambayeshi.
"Jiya da yamma ne."
"Kuma a lokacin kace ta bar maka gida ko? Shin baka san nisan da ke tsakanin Bauchi da Sokoto bane? Yanzu kasan wani hali take? Ta isa gida lafiya ko bata isa ba?. Kar ka manta har gobe akwai wasu nauyinta dake kanka har sai ta gama maka idda. In an bi ta musulunci a gidanka zata zauna har ta gama idda. Kana sane da cewa ka sa6a a addinance?" Baba ya fad'a yana kallon Anwar da dukkan alamu baya son wannan zama.
Anwar ya k'ara dukar da kai yace,
"A yi hakuri, raina ne ya 6aci, sai da ta tafi naga ban kyauta ba, dana barta har sai washegari da safe."
Girgiza Kai Baba yayi cikin fushi yace,
"Yayi kyau, baka ji sanda nace a gidanka ya kamata tayi Idda ba? Yaushe ka koyi taurin Kai ne? Ka kirata ka ji ko ta sauka lafiya. Ka sani in har wani abu ya sameta zan yi fushi da kai fushi mai tsanani Anwar. Sannan ka saurari hukuncina na gaba." Da cewar haka Baba ya saka takalmanshi ya shiga falonshi ya bar Anwar nan kan tabarma a varenda.
Anwar sosai ranshi ya 6aci da fad'an Baba, a tunaninshi murna zasu yi da ya rabu da wannan matar amma sai gashi a kanta Baba na masa fad'a wanda rabon da a masa har ya manta.

Nazifa ce zaune gaban Mamanta tana kuka tana fad'a mata abunda ya faru, bata 6oye mata komai ba har kamata da yayi a gidan suna ta yi satar fita.
Wayarta dake kusa da ita ya fara kuka tayi saurin duba screen d'in. Sunan Anwar da ta gani yasa tayi saurin d'auka tace,
"Hello."
"Kin isa gida ne?
"Eh na isa. Ina kwana Baban Laila?"
Tit ya kashe wayarshi, da mamaki ta ciro wayar daga kunnenta tana kallon Mamanta da ta yi kasake itama tana kallonta.
"Mama kashe wayar yayi." Ta fada hawaye ha gangarowa kan kumatunta.
Girgiza kai Maman ta yi ta fara magana,
"Nazifa nasan ban baku tarbiyya mai kyau ba dalilin neman kud'i da na saka a gaba, sannan kuma na d'auraku a kanta. Na d'auka wadatan da zan samu shi zai sa ku taso ba tare da tangard'a ko maraici ba. An sha fad'a min 'yayana basu da tarbiyya amma sai nake ganin bak'in ciki ake mini don an ga na tashi da k'afafuna. Nazifa rashin baku tarbiyyar da nayi bai kamata ya baki lasisin da zaki na mugun hali a gidan mijinki ba, bayan Allah ya rufa miki asiri ya baki miji nagari wanda ni mahaifiyarki nasan ke ba ajinshi bace. Nasan nice silar halin da kike ciki yanzu, amma yanzu ina kokarin gyarawa sauran k'annenki tarbiyarsu ko don kar suma watarana a koro mini su. Lokaci bai k'ure ba Nazifa, ko yanzu kina da damar canja halinki saboda ki samu ingantacce zaman lafiya a gidan aurenki na gaba. Allah ya fito miki da miji nagari."
Nazifa da ke kuka sanin cewa gidan Anwar ya mata nisa har abada tace,
"Ameen Mama."

*Bayan kwana 3*
A ranar Anwar ya cika sati ciff a d'akin Sa'adatu kamar yanda Addini ya shar'anta. A wad'annan kwanakin Anwar ya samu kulawa da tattali gurin Amaryarsa har ba ya son ya tuna kwanakin da suka rage masa a d'akinta.
A yau ya kasance ranar da Adama zata kar6i girki, hakan yasa tun da rana Sa'adatu ta tattare 'yan abubuwan da zata buk'ata a part d'in Anwar don kar tana shigo musu.
Da dare bayan sallah isha Anwar ya kira matan nasa falonshi ya dubesu d'aya bayan d'aya, idanunshi ne suka tsaya kan Sa'adatu da kwalliyarta yayi mugun tafiya da imaninshi, sake take da Atampa riga da siket d'inkin yabi jikinta sosai ya fitar da sirrin halittarta. Ba wani shahararren kwalliya bane a fuskarta amma hakanan kwalliyar ta k'ayatar dashi. Dubu biyar ya ciro a aljihunshi ya manna a goshinta yana cewa,
"Na biya kud'in wankan nan."
D'an russunawa tayi tana dariyan jindad'i tace,
"Nagode Habibi."
Adama da ke gefe sake da doguwar riga irin na mata masu ciki, mai suna (labour uniform) ta dubesu zuciyarta na suya, numfashinta har k'okarin seizing yake yi.
Sai da ya gama kalle Sa'adatu ya dubesu dukansu yace,
"Alhamdulillah. Yau na cika kwana bakwai d'akin Sa'adatu, so yau Adama kece da girki. Kwana nawa zaku saka yanzu da kuke ku biyu?"
"A barshi a kwana d'ayan, ko ya kika ce Maman Laila?" Fad'an Sa'adatu da murmushi a fuskarta tana kallon Adama.
"Idan hakan ya muku shikenan." Ta bata amsa ba yabo ba fallasa.
"Hakan yayi, Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kuma kauda fitina." Anwar ya musu addu'a, suka amsa da Ameen.
Sa'adatu ta musu sai da safe ta fita, Anwar da bai gaji da kallonta ba yaja siririyar tsaki, sannan ya maida dubanshi kan Adama da fara'a yace,
"Ki bani abinci kar na miki kukan yunwa."
Dinning table ta nufa ta fara zuba mishi abinci amma shi yana can falo yana jiran ta zo ta masa iso irin yanda Sa'adatu ke masa.
"Na gama saka maka abincin." Tace dashi daga can in da take.
Tunawa da halinta na rashin kula da soyayya yasa ya taso jiki a mace ya zauna yana kallon abincin da ya matuk'ar burgeshi amma something is missing, that is gabatar mishi da abincin cikin k'auna.
"Ki zauna a nan." Yace da ita ganin tana shirin tafiya.
Zama ta yi tana kallon gefe shi kuma ya fara cin abincin.
"Kin san me? Daga yau tare zamu dinga cin abinci kina bani a baki, haka Sa'adatu take min kuma ina jin dad'in hakan." Anwar ya fad'a don ya motsa kishinta ko itama zata ce zata koya.
Sai dai bata ji zata koya ba illah gani da tayi wannan cin fuska ne da kaskanci. Nan da nan hawaye ya taru a idonta ta yi saurin mayar dasu gudun kar ya gani.
Bayan ya gama cin abinci ta d'auki kwanukan zuwa kitchen ta ajiye ta dawo.
"Ki koma ki wankesu yanzu. Barin kwanukan da aka ci abinci yana jawo insects." Yace da ita yana janta zuwa kitchen d'in.
Adama da zuciyarta ke rad'ad'i ta shiga kitchen d'in ta fara wanke-wanke. Tana gamawa ta juya zata tafi yace,
"Baki goge gurin nan ba, gashi ruwa ya 6ata."
Yau kuma me yake damunshi ne? Ko dai so yake ya k'ureta ya sakata kuka kamar yanda ya saba? Ko dai hanyar da zai koreta yake nema kamar yanda ya samu hanyar koran Nazifa?
A hankali ta koma ta fara gogewa yana cewa 'Nan bai yi ba' ko 'Ki goge nan ma'.
Tana gamawa suka dawo falo anan yace ta mishi matsa, (massage).
Zuwa tayi ta tsaya akanshi ta rasa ina zata matsa mishi k'afa ne ko kafad'a.
"Ina jiranki fa." Yace da ita yana lumshe kyawawan idanunsa.
"Ina zan matsa maka?"
"Ko'ina." Ya fad'a yana narkewa cikin kujeran yana mata wani bahagon kallo, don ji yayi yana son kad'aituwa da ita.
Bayan kujeran da yake zaune ta koma ta fara massagin kafad'unshi tana sosa kai a lokaci guda.
Shi kuwa lumshe ido yake yi yana tuno surarta haka nan. Basu yi minti biyu cikekke ba ya jata sama in da d'akinta yake.
Seconds biyar da shigansu ya dakata yana kallonta kamar wani maraya.
"Adama na d'auka mun wuce nan gurin, na d'auka a yanzu kinyi hankali kin fara tsaftar jikinki. Yanzu fisabilillahi yau kin yi wanka? Ki duba dottin da na tsakulo k'asan kirjinki. Don girman Allah ki fad'a min laifin da na miki kika maida kanki k'azama haka." Ya fada tamkar yayi kuka.
Adama da tunda ya fara maganan ta fara hawaye tana jin zafin kalamansa a kanta. Ita bata san dalilin da yasa duk lokacin da ta so yin tsaftar ba sai ta ji ta kasa, dalilin tuno da zaginta da yayi a gaban abokinshi alhali yasan lalura ce ta maida ita haka.
"Adama ki duba abokiyar zamanki wallahi sam ba haka take ba, ga Nazifa da kuka yi dogon zama ita ma ba haka take ba. Meyasa sai ke kad'ai? Sam da ba haka kike ba Adama, kinada matuk'ar tsafta amma na rasa gane me ya canja miki d'abia. Sa'adatu kullum cikin gyara gurinta take, kullum part d'innan cikin tsafta yake. Sa'adatu koyaushe jikinta fitar da daddad'an kamshi yake. Sa'ad...."
"Ya isa haka Anwar, naji cewar ni k'azama ce Sa'adatu kuma mai tsafta, shin akwai wani abun da zaka k'ara fad'a mini bayan haka?" Tace dashi muryanta na rawa.
Shiru yayi bai ce komai ba don ya matuk'ar mamakin maganarta wanda wannan karo na biyu kenan.
Kawar da kanta ta yi gefe tana share hawayen da suke ambaliya a fuskarta tace,
"Kasan me kishi yake nufi? Kasan ya mace take ji in an kusheta kuma a yabi kishiyarta a gabanta? Baka tunanin zafi nake ji a zuciyata? Ko kana tunanin k'azantata ta kai misalin da dotti zai toshe min feelings d'ina akan ka? Ko kuma kana tunanin bani da zuciya ne kamar yanda sauran matanka masu tsafta suke dashi."
Runtse idonta tayi wasu sabbin hawayen na zubowa a fuskarta. Ta ja ajiyar zuciya ta sauk'e kana ta mik'e ta d'auki rigarta zata fice daga d'akin ya dakatar da ita.
"Kar ki fita."
Anwar da jikinsa yayi sanyi da maganganun Adama, ya jingina da kan gadon ya dafe kanshi yana tunanin abubuwan da ya yiwa Adama don kawai ya motsar da kishinta ta daina k'azanta, bai ta6a tsayawa yayi lissafin zafin da zata ji a zuciyarta ba balle yayi tunanin hakan bai dace ba. Idanunshi sun rufe na ganin ta canja hali bai san cewa a kowanne dak'ika shak'uwar dake tsakaninsu tana k'ara raguwa bane.
"Adama ban ta6a tsayawa nayi tunanin ya zaki ji ba idan na miki irin haka, ina cutar da zuciyarki don ki gyaru bansan hakan na nisantaki da abunda nake so ki zama ba. Wace hanya zan bi in ga kin gyaru Adama? Don Allah ki fad'a min kowacce hanya ce zan bi don ki canja wannan halin da kika arawa kan ki."
Bata ce komai ba sai shesshekar kuka da take yi, zai k'ara magana ta fice daga d'akin yana kiranta tak'i tsayawa.
Mikewa yayi da azama yana binta a baya, a kofar fita ya tarda ita, bai damu da yadda take zubar hawaye ba, ya manta da yanayin da ya samu jikinta ma Sam. Hannu ya mika ya kama tsintsiyar hannunta, da duk karfinsa ya sa yana janta zuwa jikinshi, hannuwanshi biyun ya sa yana tallabe ta, sosai ya kwantar da ita saman faffadan kirjinshi, ya na shafa kanta alamar rarrashi.
"Na sani, na kasance mai son kaina fiye da komai. Ban duba halin da zuciyarki zata kasance ba, na yanke hukuncin da nike ganin kamar shine zai taimaka ki gyara rayuwar aurenmu. Ki sani Adama, ke keda babban kaso a gaba d'aya birnin zuciyata, me yasa kike son horar da mu ta hanyar da ko alama bai kamata ba?"
Hawayenta da take jin suna kara zubowa ta fara gogewa, wata sabuwar natsuwa ta samu, kasantuwarta a kan kirjin mijinta. Tana son shi sosai Allah Ya san da wannan, sai dai bata san ta ya zata fara gyaran rayuwar da ta riga ta gurgunce musu ba. Kuka ta kara fashewa da shi, tana kara shigar da gangar jikinta a duk jikinshi, a lokaci guda ya sa hannu yana shafar gashin kanta ba tare da wannan karon ya damu da dottin jikinta ba, can cikin makoshinta yake jin tana cewa
"A ganinka ina yin hakan da son raina ne nima? A ganinka zan za6i in azabtar da zuciyoyinmu bayan na san kana da bukatata irin haka? Kai ka jaza komai Abban Laila, kai ka maida ni abun da kake korafi a yanzu. Baka san da wannan ba?"
"Idan na fahimce ki, kina nufin nike da alhakin canjawarki kenan? Ta ya hakan sai kasance? Ta ya zan mayar da rayuwar matata irin haka, bayan na san ba hakan nike da bukata ba."
"Na ji komai Ya Anwar. A wannan ranar na ji komai da kunnena!"
Ta fada tana kara sautin kukanta da sheshshekar mai zafi sosai.

Comment, share and vote dearies😍

Ya kuke ganin za'a kare a next page?
Bari mu ga ko zaku tsumayi page na gaba.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now