BAKAR ZUCIYA
TRUE LIFE STORY
NA
Basira Sabo Nadabo
Shafi Na Biyar
Haka wunin ranar mukayi ta zugun-zugun kowa da abinda ke ƙulle cikin zuciyar sa, donko abinci ranar babu wanda yaci haka duk muka kwana, yau ɗan sai da safen da mama kaka takemin ban samu ba sai dana leƙa ɗakin naga harta kwanta amma nasan ba bacci takeyi ba nice bata son gani, haka na juya ɗakina raina babu daɗi, sai juye-juye nakeyi don bacci yaki kawo min ziyara sai gabda asuba na samu nayi bacci, ana kiran sallar farko kuma na tashi ina idar da sallar mama kaka ta shigo ɗakin tare da zama a gefen gadona sai da tabari na idar da addu'oina sannan tace "Amatul'kareem magana nazo muyi kuma ina son ki buɗe kunnuwarki kijini da kyau ba wasa nazo dashi ba zuwa nayi akan maganar makarantarki, inaso ki shirya ki koma makaranta saboda bana son ganinki a zaune cikin gidan nan kuma idan harna isa dake to ki tashi kiyi wanka kizo kiyi kumallo ki shirya zuwa makaranta amma fa sai in harna isa dake kenan"
Da kyar na iya ɗago kunburarrun idona tare da cewa "kiyi hakuri mama kaka wallahi bawai bana jin maganarki bane kuma bana bin maganarki bane, wallahi a duniyar nan bani da wanda zai faɗamin naji sama dake, kuma ke kike da alhakin cemin nayi koda bana so kuma ki hanani koda ina so sannan nayi biyayya a gare ki, mama kaka kawai bana son fita ne mutanen unguwar nan su cigaba da tsangwama da hantara na suna guduna ko wanne da irin bakar addu'an da yake tofamin yara da manya kowa guduna yakeyi, kina kallo fa ranar da mukaje ta'aziyar gidan su aunty sa'a kowa guduna yakeyi wanda bai san abinda yafaru ba a wannan ranar sun sani hatta aunty sa'a kyamata takeyi da muka dawo gida sanadiyyar abinda aunty sa'a tamin kema saida kika zubar da kwallah wai itama kenan da take ƴar uwan Abbana, gashi ko shago naje har mazan anguwan nan basu barni ba sai habaice-habaice suke jefamin, wallahi mama kaka duk randa na fita ni kaɗai nasan irin bakin cikin da nake haɗiya shiyasa bana sha'awar fita koda ƙofar gida ne", taja hanci ta cigaba da cewa "amma yanzu zan tashi na shirya na fita kodan farin cikin ki kuma daga yau bazan ƙara saki kuka ba zan kasance mai biyayya aduk wani maganarki" haka hawayen ya cigaba da tsiyaya kamar lalataccen panpo"Kiyi hakuri Amatul'kareem ke taki kalar kaddarar kenan Allah ya baki ikon cin jarabawarki amma kam ke abar tausayawa ce a rayuwa, tunda Allah ya halicceni ban taɓa ji ko ganin irin wannan iftila'in ba sai dai naji a maƙota ko a gidajen radio, wai yau gashi a gidana har gadon baccina oh Allah ka yafe mana munanan aiyukanmu amma kam gaskiya babu zuciyar da zai iya aikata hakan sai bawa mai BAKAR ZUCIYA irin na ubanki amma bakomai Allah yana kallo kuma yana sane da halinda kike ciki kuma shine zai yaye miki tare da bi miki hakkinki, ki daure ki shirya ki tafi makarantar kibar kukan nan haka karya saki ciwon kai kinji jikalle na"
"Toh mama kaka mama kaka bari na ɗan watsa ruwa saina tafi"
"Yauwa ƴar albarka Allah yayi miki albarka ya kuma ya wulakanta uban daya zalinta zuciyar ƴarsa"
"Amin mama kaka ni kaina ina burin ganin ranar da Abbana zai wulakanta, ya tozarta sannan arzikin da yake taƙama dashi bazai amfane shi da komai ba, Ya Allah ka wulakanta Abbana don girman zatinka Ya Allah" ta karashe maganar cikin kuka
GIDAN ALH ALI
"Gaskiya Alhaji kasan yadda zakayi dani shikenan ni ba ɗa ba komai ɗan arzikin daka samu nace ka raba ka bani nawa kaki, koso kake ka faɗi ka mutu wa'incen yaran su kwashe komai ni subarni da ladan taƙaba to wallahi da sake Alhaji bazan iyaba sai dai ka sake ni kawai" cewar Aunty Salima
"Haba hajiyata haba ke kuwa ya kike son nayi ne, nace miki mun gama magana da lauya na lokaci kawai muke jira na zartar da hukuncin da kike so kuma sai yadda kika ce za'ayi, amma maganar cewa inna faɗi na mutu yaran nan zasu kwashe min dukiya a barki da ladan taƙaba to bari kiji lokacin dana ke tara kuɗina babu ko kwabon uwarsu a ciki balle suyi tunanin wawashe min kuɗina duk abinda na tara naki ne ke ɗaya ko yan uwana ban yarda ki basu ba, don haka ki kwantar da hankalinki kinji ko gudaliya na" ya karashe maganar cikin rarrashi
"Shikenan Alhaji yanzu naji batu kuma nasan madafa ta a cikin gidan nan, amma ya maganar cikin dake jikin ƴarcen ina gudin karya ɓata maka kujera kasan magauta fa"
"Lallai kinyi tunani mai kyau kuma In Shaa Allahu zanyiwa tufkar hanci karki damu babu uban da zai hanani hawa kujerar nan dole kujerar dana ke nema ya zama nawa dole ne ma kawai" haka ya cigaba da kumbar baki kamar zai ari baki
Ni Basiratu na kuma cewa uhmmmmmmmmmm, ayi dai mugani
Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce
Basira Sabo Nadabo
Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo
YOU ARE READING
BAKAR ZUCIYA
Historical FictionLabari ne daya faru a gaske wato TRUE LIFE STORY, ga kadan daga ciki Ya Allah ka wulakanta Abbana, ka tozarta shi kasa shi a kasan su Abujahal a wutar jahannama Ya Allah ka amsa min addu'a na Ya Allah Kudai ku gazarya ku biyo Yar Nada...