LAST PAGE

349 20 3
                                    

BAKAR ZUCIYA


TRUE LIFE STORY


              NA

Basira Sabo Nadabo

ƘARSHE

ALHAMDULILLAH!!! ALLAH ina ƙara godiya a gareka daka bani sauke nauyin dana ɗauka ma kaina Allah ka shaida na faɗawa duniya abinda aka umurce ni dana faɗa, Ya Allah abinda na faɗa kuskure aciki Allah dani da masu karantawar Allah ka yafe mana, Ya Rabbi abinda yake dai-dai acikin abinda muka karanta dani da masu karantawa Ya Allah ka anfane mu dashi. Amin Ya Allah,, kuyi hakuri wallahi nima ba haka naso labarin ya kasance ba naso labarin yakai pages hamsin amma saboda wani uzuri wanda daga ni sai Namecy Na wato Cutie Pie ne muka san wannan dalilin amma kuyi hakuri don Allah na yanke labarin kuma na haɗa shi duka a cikin wannan pagin na dunkule shi gaba ɗaya kuma don kuma in taƙaita muku wahalar neman littafin, Nagode Sosai Readers in babu ku babu writers haka in babu writers babu readers kudai ku cigaba da zubawa wutar fuel. Ƴar Nadabo Na Godiya.



Shafi Na Goma Sha Biyar

Tunda daddare na faɗawa Mama Kaka da Oppa na gobe zan faɗa musu uban cikina, da fargaba na kwana tare da faɗuwar gaba saboda bana son tuna abinda ya faru na rayuwata daya gabata, karfe goma a gidan mu yayi wasu H. Hasheem bayan mun gama barkwancin mu na kawayen da suke amintarsu don Allah, na kirq Mama Kaka da Oppa na don tun jiya yazo gidan duk muka haɗu a falo, falon yayi tsit sai karar a.c dake aiki na zauna shuru na kasa magana sai zubar da hawaye nane ya yawaita, Mama Kaka ce tayi karfin halin cewa

"Ke wani irin shashanci ne wannan Amatul'Kareem kin ajiye mu kuma kin zauna kina kuka, in kinsan kuka zakiyi to aida baki taramu anan ba saiki bari in kin samu jarumtar faɗa mana saiki tara mu" cikin ƙaguwa da son sanin waye uban ɗan cikin dake cikinta take magana

"A'ah Mama Kaka kibarta ta zubar da hawayen ta domin na tabbata babu komai a cikin labarin sai tarin bakin ciki" cewar H. Hasheem

Don Allah duk kuyi hakuri yanzu zakuji tarihin rayuwata da kuke ta magiyar na baku naki toh gashi yanzu zakuji, taja hanci tare da cewa kamar yadda kuka sani ne

         "Sunana Amatul'Kareem Ali ni ƴar haifarfiyar garin nan ne, Ammina da Abbana sunyi auren so da kauna ne domin Abbana mutun ne mai tsoron Allah ga ibada a kullun zaka ganshi cikin masallaci gurin neman Allah ya biya masa bukatun sa ne kuma cikakken ɗan boko ne amma duk son karatunsa na boko baya hanashi bin hukuncin Allah a lokacin bashi da komai ko gidan da suke zaune Mama Kaka da Baba Kaka ne suke biya masu kasancewar Ammina ita kaɗaice a gurin iyayenta sun ɗauki son duniya sun ɗaura akanta, Ammina malamar wani islamiya ce kuma suna biyan ta dai-dai gwargwado da wannan albashin take ciyar dasu har subiya wa kansu bukatar da batafi karfin samun suba, suna zaune cikin kwanciyar hankali har Ammina ta haifi Oppana Abdul'Kareem, kwatsam Abbana ya samu aiki a wani babban company a garin nan abubuwa sun fara warware Ammina saboda yanzu abinda yafi karfin su yanzu sunfi karfinsa har ɗan gida Abbana ya siya saboda suna biyansa da tsoka, saboda tsoron Allah da rikon amana har matsayi ya samu a gurin kuma suka kara masa albashi mai tsoka ga gida da manyan motocin da suka mallaka masa halak malak domin sun ɗauki yardan su gaba ɗaya dun ɗaura akan Abbana, da kuɗi suka zauna masa sai ibadarsa ta fara rauni saboda haɗuwa da mugayen abokai da yayi, ana cikin haka Ammina ta kara samun cikina lokacin oppana yana firamiri skul shekarar sa goma oppa da Ammina ne sukayi rainon cikin harya girma saboda Abbana bashi da lokacin da zai zauna ya kula dasu, har Ammina ta haifi santaleliyar yarinyar ta kyakkyawa yan barka sai zuwa sukeyi saboda yanzu Abbana yana dashi har ranar suna ya zagayo yarinyar taci sunan Amatul'Kareem, na taso cikin gata dajin daɗi tun ina ƴar shekara takwas Abbana ya fara futa dani kasar waje amma bada son ran Ammina ba, Ammina macece tsayayyiya akan tarbiyar yaranta saboda duk yadda naso na ɗauki al'adar turawa ta hanani kuma bata yarda da muna wulakanta ɗan adam ba koya yake sannan ta bamu tarbiyar da addini ta koyar damu, a ɓangaren Abbana kuwa arziki sai buɗuwa yakeyi domin shima sunan sa ya fara yawo a faɗin kasar nan namu harda wajen kasar sannan addininsa yana kara rauni saboda yadda ya damu da bautar Allah ba dare ba rana sai ya zama sallar ma da kyar Ammina take sashi yayi tun sunayi a boye harya kaiga mun fuskanci halinda suke ciki alokacin ina aji shida a sakandiri mune masu rubuta jarabawar barin makaranta, munyi jarabawa kuma nafito da sakamako mai kyau harna samu gurbin karatu a jami'ar garin nan kwatsam muna zaune Abbana ya kawo mana zancen zai kara aure ba karamin tashin hankali muka shigaba dajin kalar matar dazai aura duk son da Abbana yake min amma ya toshe kunnuwar sa da irin magiyar da nake masa, saboda Aunty Salima macece ƴar duniya wanda su kawai su samu duniya shine burunsu, aka ɗaura aure amarya ta tare a ɗaya ɓangaren na gidan tun daga wannan ranar ibadar Abbanmu ya samu babban rauni kamar yaddana faɗa muku abayane na gane hakanne inaje ɗakinsa, inna tambaye sa mai yasa yake haɗa sallah sai yace aiki ne suke masa yawa, abubuwa sunata faruwa ciki harda dawowar oppana daga karatu, Ammina tagaji da lamuran Abbana saita zuba masa ido sai dai tunda nazama budurwa ta hana Abbana fita da yakeyi dani kasan waje saboda na zama cikakkiyar budurwa kuma su turawan nan inhar suka kyallah ido sukaga abu suna so tofa kota wani hanya ne zasubi don su sami wannan abin toh saboda irin hakane yasa Ammina take kin yarda Abbana ya fita dani kenan, rayuwa tayita tafiya har muka shiga aji na uku a jami'a kwatsam Ammina ta tashi da ciwon ciki wanda mukayi gaggawan kaita asibiti amma kafin mu karasa Ammina ta rasu haka muka ɗaukota muka dawo gida nayi kuka nayi ihu amma Ammina bata dawo ba ta tafi kenan, ta ɗan tsaya da labarin saboda kukan dayazo mata da karfi ta cigaba da cewa mun shiga tashin hankali da bakin ciki ba kaɗan ba Mama Kaka taso na koma gurintq amma Abbana yaki, Ammina ta rasu babu daɗewa Baba Kaka shima yarasu mutuwar Baba Kaka ya dawo min da mutuwar Ammina sabo haka muka ɗauki hakuri da dangana, bayan mutuwar Ammina Basira sai Aunty Salima ta ɗauko wasu halaye wanda bata dasu, bata damuwa damu, kona na kwana a gidan ko karna kwana babu abinda ya dameta, sannan Abbana ya tsuro min da wasu halaye wanda ban sansa dasu ba ada kullun sai yazo ɗakina ya dubani kafin nayi bacci ko kuma innaje ɗakinsa sai yayita kallona musamman kirjina don naga nan ne yafi maida hankali, ni kuma ban taɓa kawo wani abu a raina ba saboda ubana ne sannan yanzu duk wata kasa da zashi tare muke zuwa kuma baya barina nasa kayanmu na al'ada sai dai ya siyo min kananun kaya wai anan shi mutane ke sawa kuma in anga ƴarshi da wannan kayan hausawan za'a ɗauke shi bagidaje wanda bai waye ba, duk sona da kananun kaya sai naji bazan iya sawa ba saboda Ammina tana yawaita faɗa min duk inda mace musulma take toh ta rike darajar ta na addini kuma ta kare mutuncinta don inya tafi babu abinda zai dawo dashi, domin mutuncin ƴa mace yafiye mata duk wani kyale-kyale na duniya kuma wasu kayan basu dashe mace tasa a gaban iyayenta ko ƙannan ta musamman iyaye maza da ƙanne maza, gashi yanzu ya sake min kuɗi wanda ada tun rasuwar Ammina ya daina bani, gashi duk basu damu da tarbiyata ba ga samari sai ɓulɓulowa sukeyi wasu don kuɗin Abbana wasu kuma don surar jikina, guda ɗaya ne masoyina na gaskiya saboda yardar da nayi masa har gidansa nake zuwa amma wallahi duk zuwa da nakeyi bai taɓa nuna min sha'awar wani abu na jikina ba, kuma ina zuwa tun safe sai dare nake dawowa amma bance bamajin wani abuba daga ni harshi kawai daurewa mukeyi tare da neman tsarin Allah daga faɗawar mu halaka, Aunty Salima tasha kamani na dawo daga gidansa da daddare amma bata taɓa min faɗa ba sai dai nice nayiwa kaina faɗa saboda bani da mafaɗi, hausawa nacewa wanda ya rasa mafaɗi yayi kuka saboda duk abinda nayi dai-dai ne a gurinsa, haka rayuwa tayita tafiya aciki kuwa harda yanayin da Abbana yake nuna min wanda bai dace ba sai dai na lura yana cikin damuwa musamman idan ya ganni duk sai naga ya ɓata rai baya son ina zuwa gurinsa, watarana na shiga ɗakin Abbana da daddare bayan ya dawo daga aiki don in tambaye shi kona masa laifine yake fushi dani, ina shiga ɗakin naji Abbana yana cewa a gaskiya Alhaji mudi bazan iyaba wannan tsananin yayi yawa ƴatace fa da cikina na haifeta gaskiya ka faɗawa mallam na hakura ajanye aikin domin bazan iya aikata abinda yace ba, ban san me akace a ɗaya ɓangaren ba amma naji Abbana yana ce masa kuma kana da gaskiya don bazan yarda nayi asarar abinda na daɗe ina nema ba kuma bazan iya aikatawa ba amma zanyi tunani akai, na karasa cikin ɗakin na zuna bayan ya gama amsar wayar ya lura dani a gurin da halamar tsoro a tattare dashi amma bansan na menene ba, bayan mun gaisa nake bashi hakuri inna masa wani abu ya yafemin, yace ban masa komai ba kuma na shirya zan rakashi spain wani aiki na nuna masa bana son zuwa amma ya keƙashe kasa wai dole sai naje, ni kuma bawai zuwanne bana soba sai dan wannan ƴan iskan kayaɓ da yake bani na saka ne bana so, bayan haka da sati biyu Abbana yace na shirya gobe da yamma zamu tashi washe gari da safe naje gidan Mama Kaka domin yi mata sallama, bayan na faɗa mata maganar tafiyar nagq ta ɓata fuska, na tambaye ta lafiya tace wallahi Amatul'Kareem zuciyata ce bata amince da wannan tafiyar ba kuma na rasa dalili, nace wallahi kaka nima hakan nakejin rashin son tafiyar a zuciyata ammq bazan iya cewa Abba bazani ba saboda ransq ɓaci yakeyi, wani irin ɓacin rai ana dole ne bari ni zan kirasa a waya na faɗa masa tunda yanzu ya daina zuwa dubani yayi kuɗi, kiyi hakuri kaka karki kirashi bana son abinda zai ɓata masa rai zan bishi mu tafi kawai, kibini da addu'a amma har yanzu banajin tafiyar a raina sai nakeji kamar wani abunne zai sameni acen, In Shaa Allahu babu abinda zai sameki sai alkhairi kuma addu'a kullun acikinyi muku nakeyi, oppanki ma kullun yana gidan nan ranar ya kawo min matar dazai aura wallahi baki ganta ba ɗiyar mutunci, Mama kaka rabu da oppa ni fushi nakeyi dashi nace ya canja min mota yaki, haka muka cigaba da hira na kaka da jika har oppa yazo na faɗa masa shima da farko bai yarda ba, nice na dinga kwantar musu da hankali na rasa me yasa duk kanmu bamu son tafiyar nida ya kamata su karfafawa zuciya sai nice na koma karfafa musu zuciya har zuwa ƙarfe uku na koma gida domin na shirya kayana wanda zan bukata acen don konaje da kaya masu mutunci Abbana bazai yarda nasa ba, ina gamawa na kira Abbana na shaida masa na gama yace na fito kawai zai biya wani gida kafin mu tafi, yanayin dana ganshi duk sai naji na damu da halinda yake ciki kwana biyun nan a haka dai muka isa gidan yace na jirashi yana zuwa bayan shiganshi gidan da ƴan mintuna ne suka fito shida wani mutun daga ganin sa kasan mutumin da babu Allah a zuciyar sa haka kawai naji na tsana mutumin har suka karaso gurin motar amma ko arzikin gaisuwa bai samu a gurina ba sai wani lashe baki yakeyi kamar tsohon maye, suka gama maganar su shida Abba, har muka isa filin jirgin zuciyata ta kasa nutsuwa da wannan tafiyar namu, wannan ranar shine ranar da nayi bankwana da duk wani farin cikin rayuwata kuma wannan ranar shine ranar da yakafa mummunar tarihi a rayuwata, bayan mun isane naga Abbana ya kama mana ɗaki ɗaya ni dashi acewar sa shi bazai dinga kwana ba saboda yanayin aikin dayazo yi, abinda ban sani ba shine ashe bayan na kwanta yana shigowa ɗakin yana ƙaremin kallo saboda nasha kamashi inna farka sai yace ai yazo ɗaukan wasu fayal ne ban taɓa kawo wani abu a raina ba saboda shi mahaifina ne, watarana mun dawo daga yawo kwanar mu huɗu a spain bayan mun dawo daga yawon ne Abbana ya ɓallo wasu magugguna guda uku ya bani wai nasha saboda kar kafata tayimin ciwo ko kuma ta kumbura saboda yawon da mukasha yau na amsa maganin nasha, aiko inasha da ƴan sakwanni naji kaina yana juyawa gashi bana gani da kyau jiri sai ɗibana yakeyi nan da nan bacci mai karfi yayi gaba dani, wani hukuncin Ubangiji duk karfin maganin nan Allah ya bani ikon gane abinda ke faruwa dani wasu sabbin yanayi nakeji a jikina ina buɗe idona naga Abbana yana aikata alfasha dani ƴarsa ta cikinsa ni Amatul'Kareem jininsa"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 07, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAKAR ZUCIYA Where stories live. Discover now