SHAFI NA TARA

222 12 5
                                    

BAKAR ZUCIYA

TRUE LIFE STORY

NA

Basira Sabo Nadabo


Shafi Na Tara

Haka mukayi alwalar tare da shiga cikin masallaci babu kowa a ciki saboda an rigada har an idar da sallah saura mune yanzu zamuyi namu, mukayi sallar ina idarwa na ɗaga hannuna sama tare da cewa

"Ya Allah, Ya Ubangijin sammai da ƙassai Ya Rahman, Ar-Rahim, Al-Malik, Al-Quddus, As-Salam, Al-Mu'min, Al-Muhaymin, Al-Aziz, Al-Jabbar, Al-Mutakabbir, Al-Kaliq, Al-Bari, Al-Musawwir, Al-Gaffar, Al-Qahhar, Al-Wahhab, Ar-Razzaq, Al-Fattah, Al-Aleem, Al-Qabid, Al-Basit, Al-Khafid, As-Sami, Al-Basir Ya Allah, Ar-Raqib, Ash-Shahid Ya Allah ina rokon ka da cikakkiyar sunayen ka Ya Allah, don tsarkin Kurdiyyun ka Ya Allah, don darajar cikakkiyar maganar ka (Al'Qur'ani), Ya Allah ka wulakanta Abbana ka tozarta shi Allah ka hanashi rahamar ka Ya Allah ka tabbatar da duk wani nau'ikan azabar ka a gareshi, Ya Allah ka wulakanta rayuwar shi ka azabtar dashi, Ya Allah ka yalwata duhu a kabarin sa, kunamu, macizai tare da jahannama ka yalwata masa su a cikin kabarin sa Ya Allah ka amsa min addu'a na mana Allah" ta fashe da kuka mai tsuma zuciya har saida masallacin ya amsa, da gudu H.Hasheem taje ta rungumrme ta suka cigaba da kukan duk da Ha.Hasheem bata san musabbabin mugayen addu'oin nan ba amma ta yarda cewa koma menene Abban ta yayi mata ba karamin abu bane, ta ɗago daga jikin Amatul'kareem tare da cewa

"Bazan hanaki ba kuma bani da ikon hanaki yin duk addu'ar da zakiyi wa mahaifinki amma ki sani wannan addu'oin sunyi tsauri suna rikita hankalin mai sauraronki ki tuna kina yiwa Allah laifi mai girma wanda yafi wanda Abbanki yayi miki amma ki sani Allah Gafurur-Rahiem ne tome yasa kema bazaki zama mai gafara da neman wa Abbanki rahama gurin Allah ba sai kece mai nema masa azaba a gare shi, Amatul'kareem bance ki faɗa min danuwarki ba amma don Allah ki sassauta wannan mugayen addu'oin akan Abban ki don kema ki tsira ranar gobe al'kiyama kinji" duk cikin kuka take magana

"Amatul'kareeem maganar Hajara gaskiya ce kuma wallahi kisani muma da muke tare da ke zunubinki zai iya shafan mu, mu bamu ce ki daina ba saboda bamu san abinda yayi miki ba amma ki rage saboda ba haka addini ya koyar damu ba, don Allah ki rage Amatul'kareem badan muba sai don Allah" itace kawai tayi dauriya bata tayasu kuka ba

Ta share hawayen ta tare da goge jajayen idanun ta cikin dashashshiyar murya tace

"Hakika ku kawaye ne nagari wanda Annabi yace mu kasance tare dasu saboda zama cikin inuwar Allah ranar sakamako, kuyi hakuri bazan iya faɗa muku abinda Abbana yamin ba amma ku sani harda hannun Abbana a shigata cikin wannan mummunar halinda nake ciki don da bai kore ni a gidan saba da bana cikin gararin rayuwa yanzu, H. Hasheem, F. Ahmad wallahi ina alfahari da kasancewar ku a tare dani kuma nayi muku alkawari zan baku labarin abinda ya faru dani tun daga farkon rayuwata har zuwa abinda yafaru dani bazan ɓoye muku komai ba amma ba yanzu ba in lokaci yayi zan kiraku da kaina ranar da zan faɗawa kowa uban cikin dake jikina a ranar Abbana zai san waye uban jikan shi da baya son ya taka ƙasa, amma karku tambaye ni yaushe in lokaci yayi zan faɗa muku kunji kawaye na" ta karasa maganar da murmushi tare da hawaye

Haka taciga da kai kukanta gurin da za'a share mata hawayenta ba tare da an amsa mata ko kwabo ba, babu wanda yayi niyyar hanata har tayi shuru don kanta, kuma fito tare da zuwa gurin da aka kafa mana tam tebur duk zuciyoyin mu babu daɗi kowa da abinda yake sakawa a ransa da ganin idon mu nida Hajara ansan koba'a tambaya ba kuka mukayi muka koshi har mukayi shuru don kanmu, bayan mun gama kwafowa mukayi musayar lambar waya, motar ɗaukan mu yazo munyi-munyi Amatul'kareem ta shigo mu rage mata hanya amma taki haka muka hakura badan ranmu soba, suna tafiya nima na hau a keke napep harna isa gida raina babu daɗi, da sallama na shiga gidan

"Lale-lale Amatul'kareem aina faɗa miki babu abinda zai faru dake, ilai gashi kin dawo babu abinda yafaru" cewar mama kaka

Uhummm kawai na iya cewa saboda bana son tuna abinda yafaru da safe kafin naje makaranta

"Yauwa Ama ɗazu Abbanki yazo dubaki da abinda ke cikin ki kuma yabar min sallahun cewa ki daure kije kiga likitan dake dubaku wai akwai abinda zai miki kum......"

"Ya isa ya isheni," ta katse mama kaka "Mama kaka bana sonjin sunan makiyin Allah wanda ya kada yarda da kaddarar daya faɗawa ƴarsa ta cikin sa, mama kaka na tsene shi na tsana duk wani abinda zai fito daga gare shi, wallahi mama kaka duk ranar da mutumin nan ya kara nunawa shine ubana saina wulakanta shi tunda baya kishina kuma wallahi babu inda zani na gwammace na mutu gurin haihuwar abinda yake gudu da naje neman taimako a gurin sa, ada yaso mutuwa gurin dagewa da saiya cire cikin dake jikina saboda yana gudun abin kunya toya makaro ɗan dake cikina sai ya fito duniya da yardan Allah kuma har ya kirashi da kaka, In Shaa Allahu saiya tsinewa uban da yayi sanadiyyar zuwan shi duniya" ta karashe maganar tare da zubewa a kujera tana gunjin kuka mai ban tausayi

Ni Basiratu da take bani labarin saida kwalla ya saukan min


Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce

Basira Sabo Nadabo



Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo

BAKAR ZUCIYA Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ