Kafin kace kwabo gabaki d'aya k'asar LU'AL BIYAL ta dauka da mutuwar Sarki zurural har nan fa aka shiga murna da kad'e-kad'e, kasancewar kowa yasan zurural har baya da wani magadi sai aka miqa ma waziri sarauka akayi masa nadi da komai an shafe kwanaki bakwai Ana shagulgula,a kwana na bakwai dinne sabon sarki ya hau karagar mulki sai dai nan take ya tarwatse yayi daga-daga naman jikinsa ya rarrabu nan fa kowa ya cika da alhini hadi da tsoro, bayan shud'ewar waziri sai akayi ma d'an waziri na farko sarauta shima anyi shagali kafin ya haye bisa kujerar ta sarauta abunda ya faru da mahaifinsa shine ya faru ga wannan matashin yaro nan kau gabaki d'aya k'asar ta gauraye da surutai iri-iri kowa dai da abunda zaice, washegari aka buk'aci mai bi masa yazo ayi masa sarauta yace shi Sam ya yafe, nan galadima ya hau dariya dama abunda yake jira kenan, nan yahau fadin tunda yaro baya so to shi ayi masa sarautar shi babu abunda yake ji ma tsoro, to da yake galadima irin mutanen nan ne marasa imani shiyasa kowa yake shakkarsa, nan take aka soma masa nad'i yace shi babu wani shagali da za'ayi kawai zai hau kujerar mulki ba tare da anyi wata bidi'a ba. Babu wanda ya tanka masa yana dariya ya haye kujerar take shima ya watse nan fa kowa ya soma gudu ana iface-iface nan wani ya lura da wani ganye da alqalami a ajje ya dauko sai ga rubutun sarki zurural har ya bayyana inda yake bayanin babu wani mahaluki da zai k'ara sarautar k'asar ta LU'AL BIYAL face Wanda ya nemo hatimin kujerar sarautar wanda akafi sani da LU'U LU'UN SARAUTA idan ba haka ba ko iyakar mutanen k'asar zasu hau a rana d'aya to sai dai labarinsu, nan fa mutane kowa ya fara tofa Albarkacin bakinsa nan manya masu fad'a aji suka shiga shirye-shiryen rufe masarautar gabaki d'aya sannan sukasa akayi shela kan cewa duk wani mai son yayi sarautar LU'AL BIYAL to yaje ya nemo LU'U LU'UN SARAUTA.
Take aka siyar da bayin dake cikin masarautar sauran kuma dukiyar tare aka rufe da ita idan ka fidda dawakai da aka barma jaruman garin masu fita yak'i. Tun daga wannan lokaci jamaar cikin k'asar suka fara fita domin neman lu'u lu'un sarautar sai dai har kawo yanzu da nike baka wannan labarin babu wani mahaluki da ya samu nasara hasalima duk wanda ya tafi ba lallai bane ya dawo da rai saboda namun daji dake farautar mutane"
Wata sanyayyar ajiyar zuciya Yarima shahidul Islam ya ajje a dai-dai lokacin da mahaifinnasa ya gama basu labarin asalin k'asarsu ta LU'AL BIYAL,
Sarki sharahudden ya cigaba da fad'in"ya kai wannan jarumin d'a nawa, a iyakar sanin da nayi kaf k'asarnan ta lu'al biyal bama iyakar yankinnan namu ba na baitul islama babu wani jarumi Sadauki kamarka saiko d'an uwanka ZULUM ZUBI da nike tunanin zaku zo d'aya da shi"
Yarima shahidul Islam ya d'ago ya kalli mahaifinnasa sakamakon jin ya ambaci cewa zulumzubi danuwansa ne,
"Don haka ina mai baka umarni a matsayina na mahaifinka kuma sarkin wannan yanki namu na ka fara shirin fita domin ka shiga cikin jerin masu zuwa neman lu'u lu'un sarauta"
Sarauniya zulzulatu tare da d'iyarta gimbiya silirat da sauran dakarun dake tsaye suka saurin kallon sarkin nasu cikin matuk'ar kad'uwa tare da mamaki daya bayyana a fuskokinsu.
Shiko Yarima shahidul Islam ko d'ar baiyi ba in banda tunanin daya zurfafa na yanda yaji mahaifinsa ya ambaci zulumzubi a matsayin d'an uwansa tabbas wannan ba shi bane karo na farko da mahaifinnasa ya furta magana makamanciyar haka sai dai wannan karon yana mai kwad'ayin son jin yanda akayi wannan furuci ke fita daga bakin mahaifinsa, sanin kowa ne Yarima zulumzubi shine d'an sarkin yankin K'URUZUN NAJ wato sarki k'arkil k'usumi wanda gabaki d'aya mutanen yankin ma'abota bauta ma gumaka ne wasu wuta wasu itatuwa, gabaki d'aya jama'ar dake yankin basu da takamaiman abun bauta sakamakon mutanen yankin baitul Islam wanda kowa yasan ma'abota addinin musulunci ne gabaki d'ayansu hatta dabbobinsu sun fita daban.
Muryar mahaifinsa ya tsinkaya yana fad'in"don haka inaso ka soma shiri asabar d'in k'arshen wata zaka tafi, makonni biyu masu zuwa, yakai d'ana inaso kayi sani cewa aduk inda mutum yake kada ya kusa ya nisanta kansa da Allah, ka kasance mai tsoron Allah da tuna Allah sai kaga kayi nasara a rayuwarka kuma ina kayi sani cewa a duk inda kake zan kasance mai yi maka addu'a, Allah ubangiji yayi maka Albarka"
Ya amsa da"amin ya mahaifina, Allah ya k'ara tsayin kwana"
Gabaki d'aya wajen suka amsa da"amin"
Sai ya cigaba da magana"akwai abunda ya shige min duhu game da maganar da kayi d'azu yakai mahaifinka, kace zulumzubi d'an uwane a gareni wanda ni a iyakar tunanina banga ta yanda alaqar yan uwantaka ta had'ani da shi ba hasalima ba abu bane mai yiwuwa"
Wani k'ayataccen murmushi dattijon ya saki kafin yace"idan ya rage sauran kwana biyu kayi wannan tafiya mai Albarka to kazo ka sameni zan sanar dakai alak'arka da d'an uwanka zulumzubi d'an sarki k'arkil k'usumi"daganan ya d'aga masa hannu alamar ya gama magana yana buk'atar hutu. A tare suka fita inda gimbiya silirat taja numfashi tare da cewa"ya kai d'an uwana ka sani wannan tafiyar da zakayi tafiya ce mai matuk'ar had'ari ina mai baka shawarar kaje ka sanar da Abbanmu bazaka iya ba tun kafin lokaci ya k'ure"
Murmushi yayi wanda ya k'ara ma fuskarsa kwarjini gami da dafa k'anwar tasa yace"kada kisa komai a ranki ya ke y'ar uwata, ki sanj cewa tafiyar nan da zanyi ko kad'an banyi d'ar ba hasali ma ji nike kamar in janyo ranan tafiyar, kedai kawai ki dage da taya ni rok'on ubangijin mai kowa mai komai"
Itama murmushin tayi tace"in sha Allah a duk inda zaka shiga kana tare da addu'ata" daganan Tabi bayan mahaifiyarta wacce tun fitowarsu tayi Hanyar shiyyarta.
Shiko Yarima Shahidul Islam dakatar da masu tsaronsa yayi ya doshi barca, kai tsaye wajen da yaje ajje dokinsa ya nufa kasancewar a ware yake daban da saura, tunda ya doso y'an barga ke faman zubewa k'asa suna kwasar gaisuwa hannu kawai yake d'aga masu har ya isa ga dokin nasa dan-danan ya haye ya sakar masa linzami suke fice daga masarautar masu tsaya ko ina ba sai gaban rafin zural har inda ya kasance masa gurin zuwa ya sha iska a duk sa'adda yake cikin damuwa ko kuma wani abu ya shige masa kai yana so yayi tunani akai.
Rafin na Zural har babban rafi ne da girmansa ya kai girman gari ukku sannan cikinsa akwai zurfi sosae marar misaltuwa, a cikinsa ne ke akwai SARKI SHANZILU Wanda shine ke sarautar y'an ruwa baki d'aya, Sarki shanzilu yana da d'iya guda d'aya tilo GIMBIYA LARITA wacce duk duniya babu abunda sarki shanzilu yake so sama da ita, idan kana so kaga 6acin ran sarki shanzilu to ka taba gimbiya larita wannan yasa tun tana k'arama ya d'akko mata masu koya mata fad'a da ko wane Irin makami sai gashi a halin yanzu gabaki d'aya duniyarsu ta y'an ruwa ba Wanda zai iya karo da gimbiya larita, harta maza shakkarta suke saboda k'arfin da ke gareta sannan, gimbiya larita kyakkyawa ce ta k'arshe wacce duk cikin yankin nasu babu Wanda yayi ko da rabinta a kyau.
Gabaki d'aya y'an yankin sun kasance basu da tsayayyen Addini kowa da irin abunda yake bauta mawa.inda yawancinsu sun kasance masu bauta ma wani k'aton gunki na kifi Wanda duk k'arshen shekara ake sadaukar masa da kifaye dubu d'ari,Sarkin yankin nasu wato mahaifin Gimbiya Larita ya kasance d'aya daga cikin ma'abota bautar wannan gunki.
**********
Yarima shahidul Islam ne Zaune a inda ya saba zama idan ya fito shan iska a bakin teku,hannunsa rik'e da k'ananun duwatsu Wanda yake jefawa a ruwa sai kifaye su taso sama suna zaton Abinci ake watsa masu Wanda ya gansa nan sai ya rantse ba abunda ke damunsa a fad'in duniyannan. Yarima Shahidul Islam ya kasance kyakkyawan saurayi mai jini a jika idan ka masa kallo d'aya sai ka d'auka ba daga jinsin bil adama yake ba saboda kyawun da Allah yayi masa,sannan k'ak'k'arfa ne na gaske saboda tsananin k'arfinsa idan ka dakesa da katako a take zai dare,gashi mutum ne mai cikar zati da cika ido sai dai Yarima Shahidul Islam ya kasance baya son magana yafi so ya samu guri ya ke6e shi kad'ai kamar yanda yake zaune a bakin teku yanzu.
Cikin tafiyar k'asaita Gimbiya Larita tazo wucewa domin tafiya wajen shak'ataqarta kamar kullum ta kasance ma'abociyar son hutu wannan yasa kullum take fita domin shan iska gurare daban daban.
Tazo wucewa ne ta ci karo da k'ananan kifaye sunayin tsalle suyi sama su dawo cikin tsananin fusata ta daka musu tsawa tuni suka shiga hankalinsu sai dai har yanzu mai jefo dutsen bai daina ba,ranta idan yayi dubu ya 6aci ta soma huci duk duniya bata tunanin akwai mahalukin da take shakka don haka na tare da 6ata lokaci ba tayo sama domin ta hallaka ko ma waye.
Sai dai tun kafin ta k'ara ta fara yin tozali da fuskar kyakkyawan Saurayi Wanda tunda take bata ta6a ganin namiji mai kyawun halitta ba kamar sa,tuni ta shagala wajen kallonsa batayi aune ba sai jin saukar dutse tayi a saman kanta ,cikin rad'ad'i tayo k'asa ba tare data shirya ma hakan ba, ranta a matuk'ar bace ta k'ara yin sama inda ta nemi saurayin ta rasa,inda shiko Yarima Shahidul Islam ganin kifayen sun daina tasowa yasa ya tashi domin ya zaga.
Cike da jin haushi ta koma fad'ar mahaifinta ba tare da taje wajen shak'atawar ba,sai dai da isarta mahaifinnata ya tareta da maganan fita Neman LU'U LU'UN SARAUTA Wanda a cewarsa Yana zaune labari yazo ya rizk'esa na cewa Yarima Shahidul Islam d'an sarki Sharahudden sun soma shirin fita domin nemo lu'u lu'un sarautar.
"Yake y'ata nasan cewa bazaki bani kunya ba kasancewarki jaruma a wannan yankin namu sai dai inaso ki Sani cewa Yarima Shahidul Islam k'ak'k'arfa ne shi sai dai shi baya da k'arfin tsafi kamar yanda kike dashi wannan yasa nike so karki bi hanyar da zata sada ki dashi,ko da ace ko kun had'u a hanya ki tabbata kin nuna bajintarki na ganin kin hallaka sa dashi da tawagar tasa kiyi amfani da k'arfin tsafin dake gareki"
A fusace tace"ya Abbana shin ina dalilin da zaisa kace karna bi hanyar da ya bi bayan ka yarda da jarumtaka ta"
Murmushi yayi tare da dafa kafad'arta yace"bani so kuyi karon da zaisa a raunata ki shiyasa Amma tunda ya kasance haka kije babu damuwa,sannan ki tabbata kin yo nasarar samo Lu'u Lu'un Sarauta domin ki zama mai mulkar wannan k'asa ta lu'ar biyal gabaki d'ayanta,ki shirya tafiyar nan da makonni biyu ne masu zuwa" daga haka bai sake cewa komai ba.
Gaban wani akwati taje na lu'u lu'u mai kyawun gaske wanda tunda tazo duniya take ganinsa a gurin,mahaifinta yasha fad'a mata nan ciki gawar zurural har take.
Tsaye tayi tana mai murmushi har ta hango ta zama Sarauniyar Lu'al biyal,a nan take ta d'auki alwashin inhar tayi ido biyu da Yarima Shahidul Islam sai dai uwarsa ta haifi wani.
Sai dai wani 6angare na zuciyarta yana muradin sake yin tozali da kyakkyawan saurayin da ta gani dazu Wanda duk kyawun da take dashi sai taga kamar yaso ya kamota koma suzo d'aya dashi. Fadarta ta juya ta nufa yau kowa ya kalli Gimbiya Larita yasan cikin farin ciki take da isarta ta nufi inda take zuwa domin koyar da fad'a ta iske duk an taru ita kad'ai ake jira nan ta d'auki takobinta mai zanen kifi wacce take an tsafeta sosai kallonta take tana murmushi inda wani k'aton kifi yazo wucewa ta d'ora takobin a jikinsa take ya k'one k'urmus ta d'auki dariya a gurin ji kake"hahahahaha" tasan kowa yay karo da ita sai dai uwarsa ta Haifi wani......
YOU ARE READING
LU'U LU'UN SARAUTA
AdventureSun kasance masu neman Sarautar Lu'al Biyal wannan yasa suka fita neman Lu'u Lu'un Sarauta....