Sautin duma ne ke tashi tare da na kalangu wanda ya had'e ya bada wani sautin kid'a mai dad'i ga ma'abota sauraren sauti,gefe guda Kuma wasu tsadaddun giyoyi ne ajje a gaban kowane teburi tare da tsadaddun abinci nau'i daban daban sai y'ay'an itatuwa babu irin Wanda babu a ajje,ga mata a tsaytsaye babu suturar kirki a jikinsu gefen kowane mutum dake zaune a wannan katafaren wurin shek'e ayar Sarki tare da d'ansa.Sai wasu kyawawan mata Kuma masu kyawun sura a tsakiyar fili suna rawa mai ban sha'awa ga mutanen dake zaune Wanda yawancinsu sun kasance manyan attajirai ne yankin,gabaki d'aya gurin babu abunda ke tashi sai dararrakun jama'ar dake wurin Wanda ke nuni da tsantsar farin cikin da suke ciki.
Sarkin yankin K'URUZUN NAJ ne wato Sarki K'ARKIL WAISU zaune tare da fadawansa da duk sauran masu fad'a aji a yankin nasu ke taya tilon d'an Sarkin murnar zagayowar ranar haihuwarsa wato Yarima Zulum Zubi wanda ya kasance shine d'an sarkin yankin ma'abota bautar gumaka da wuta,Zulum zubi ya kasance d'a d'aya tilo a wajen mahaifinsa wannan yasa yake a sake ba kyara balle hantara.
Zulum Zubi azzalumi ne na k'arshe gashi k'ak'k'arfa baida imani ko kadan. Yi ma mata fyad'e a wajensa ba komai bane,Sarki k'arkil waisu shine ya kashe mahaifiyar Zulum Zubi da kansa lokacin da Zulum Zubi na k'arami sakamakon kar6ar musulunci da tayi inda yay rantsuwa da wuta cewa duk Wanda yay gigin musulunta a yankin to ya tabbata yay bankwana da duniya kenan,hakan ya matuk'ar tsorata yan yankin shiyasa har yanzu babu Wanda ya k'ara marmarin shiga musulunci.
Zulum Zubi ya taso da tsanar mahaifinsa a cikin ransa tun sa'adda ya kashe mahaifiyarsa sai dai dai-dai da rana d'aya bai ta6a nuna hakan ba,a zahiri nunawa yake ba Wanda yake k'auna sama da mahaifin nasa,yayi k'udurin cewa shine ajalin mahaifin nasa duk ko da irin soyayyar da Sarki K'arkil Waisu yake nuna wa ga Zulum Zubi.Cikin kakkausar Murya Sarki Qarkil waisu ya soma magana hannunsa riqe da kofin barasa"ya Ku jama'ata ta wannan yanki, Ku Sani babu abunda yafi dad'i a duniyar nan sama da wannnan barasar da ke hannuna,hahaha"sai ya kwashe da dariya wacce ke nuna alamar ya soma buguwa,suma jama'ar gurin dariya suka kwashe da ita,ya cigaba"saboda haka kusha barasa kawai hahaaha
Domin taya wannan kyakkyawan Sadaukin d'an nawa Zulum Zubi murnar cika shekara talatin a duniya" nan guri ya kaure da hayaniya kowa na yabon Yarima Zulum Zubi.
Shiko Yarima Zulum bata su yake ba domin hankalinsa ya koma ga karuwan da suka sashi tsakiya yanata faman shafa su yana nishad'i da alama ya soma buguwa da barasar shima.Ana cikin haka mutane duk sun Gama shagala sai ga d'an sak'on sarki mai kawo masa ruhoto daga yankin darul islam ya iso da sarsarfa Kai tsaye ya nufi gurin bafade na hannun daman sarki ya rad'a masa magana a kunne,shima Wanda aka rad'a mawa ya nufi gurin sarki ya duqa ya nemi izinin fad'a ma sarkin Wanda tun kafin ya k'arasa sanar da sarkin tuni Sarki Qarkil waisu ya fusata har wani huci ke fita daga bakinsa,saboda tsananin fusata sai da kofin dake hannunsa ya tarwatse ya fashe,nan hankulan mutane ya dawo kan sarkin domin ganin abunda ya harzuqa sarkin nasu a dai-dai wannan lokaci da yake cike da nishad'i.
Mik'ewa yayi a matuk'ar fusata, take ya zare takobi daga jikin jibgegen dogarin dake gefensa ya fed'e wuyan d'an saqon,
"ZULUM ZUBI!!!" Ya kira sunan d'an nasa cikin kakkausar murya wacce ta gigita duk d'aukacin jama'ar dake gurin da Kuma ganin abunda sarki yayi ma d'an sak'o,nan take kowa ya shiga taitayinsa a San tabbas sarki ya fusata balle yanda yayi kiran sunan d'an nasa cikin k'araji haka yasa duk suka soma zarewa suna ficewa daga cikin fadar,ya rage daga Sarki sai zulum zubi Wanda yake a bige da giya sai kuma wasu samudawa guda biyu da ke tsaye a bayan sarki.
Sai da Sarki K'arkil Waisu ya d'auki fiye da dak'ik'a biyar kafin ya d'ago idonsa ya kalli Zulum Zubi Wanda shima shi yake kallo cike da kosawa da son jin Abunda ya fusata mahaifinnasa,sai dai kuma a wani 6angare na zuciyar tasa tsanar mahaifinnasa ce tsantsa,ji yake ina ma su biyu ne a fadar a dai-dai wannan lokacin to babu abunda zai hana yayi masa gunduwa-gunduwa.
![](https://img.wattpad.com/cover/127014428-288-k163161.jpg)
YOU ARE READING
LU'U LU'UN SARAUTA
AventuraSun kasance masu neman Sarautar Lu'al Biyal wannan yasa suka fita neman Lu'u Lu'un Sarauta....