BABI NA UKU

3.2K 223 2
                                    

Nayi zama na kusan mintuna biyar kafin naji muryar Hajiya tana cewa "ďazu Adamu ya kirani a waya ya kuma sanar dani abinda ke faruwa. Banji daďi ba Khadija, kin kuma bani kunya. Kin saka mini tsoron ďan yau a cikin zuciyata domin kuwa kin aikata abinda bamu taba zaton faruwarshi daga gareki ba.

Ashe ďan yau ba abin yarda bane tunda har zaki iya ture kyakkyawar tarbiyyar da iyayenki suka yi tsayin daka suka ďora ki akai, ina wayonki yake ina hankali da tunaninki ya tafi a lokacin da kika amincewa zakin baki da yaudarar ďa namiji kika yadda ya sanki ďiya mace ba tare da aure ba. Yanzu wa gari ya waya? Ina wanda yayi miki cikin yake a lokacin da kika fi bukatar kasancewar shi tare dake?

Yayi miki nisan da ba zai dawo ba don kuwa ya samu abinda yake nema a tare dake. Ina mamakin yaran yanzu da soyayya ke rufe muku ido kuje ku aikata abinda ba shi kenan ba. Ai duk namijin da zai nemi ki bashi kanki tun a waje to Wallahi ba sonki yake yi ba. Idan har yana sonki da gaske zaiyi kokarin ganin ya kare miki martabarki da kimarki ne."

Tunda Hajiya ta fara magana nake aikin kuka don kuwa nasan dukkanin maganarta gaskiya ne don tun ranar da abin ya faru har zuwa yau Faruk bai nemeni ba. Kenan yaci moriyar ganga ne, tunda kuwa ya samu na sarayar mishi da abu mafi daraja a tare dani. Sai dai kuma har yanzu na kasa yardarwa zuciyata cewa Faruk zai yaudareni gani nake yi akwai uzurin daya hana mishi nemana amma ba wai yayi da gangan bane tunda ma dai kuďin aurenshi ya daďe a gidanmu hannun iyayena.

Cikin shakakkiyar muryar da ta sha kuka nake cewa "kiyi hakuri Hajiya, wallahi ba halina bane, tsautsayi ne ya kaini ga aikata hakan amma wallahi ba halina bane". Na kifa kaina akan cinyata ina cigaba da yin wani irin kuka mai cin zuciya.

Nq daďe ina kukan. Hajiya bata katseni ba har sai da nayi shiru don kaina sannan tace mini na tashi na tafi ďaki.

A wannan daren ko da wasa ban samu na runtsa. A yadda naga rana haka naga dare, dalilin da yasa na tashi da matsanancin ciwon kai. Bayan munyi wanka mun karya ne Hajiya ta jagorance ni zuwa wurin Baba Sule don na gaishe shi.

Yana zaune a kasa hannunshi rike da remote yana canza tashar talabijin zuwa BBC world, tire ďin kayan abinci ne a gefenshi. Ga dukkanin alamu yanzu ya gama karyawa. Daga bakin kofa na durkushe ina gaishe shi cikin rawar murya. Bayan ya amsa gaisuwar da nayi mishi ne ya umurceni dana karasa cikin parlour.

A ďarare na shiga cikin parlour na zauna a kusa da Hajiya kaina a sunkuye. A cikin kakkausar murya naji ya ambaci sunana "Khadija!" Cikin sarkewar murya na amsa da "na'am Baba" yaci gaba da cewa "na samu labarin abinda ke faruwa da kuma dalilin barowarki gida, anan sai nace kinyi kyaun kai da kika zo nan baki shiga duniya ba. Sai dai kuma ki sani amincewata da zamanki anan bashine zaisa ki dauka zamu zuba miki idanu bane kiyi duk irin rayuwar da kike so dole ne mu saka miki idanu don inganta tarbiyyar ki, bazan ďauki sakarci da shashanci ba. Dole ne ki nutsu ki gyara rayuwarki har zuwa lokacin da Mallam Hashimu  zai huce sai ki koma gida don zamanki haka ba'a gabanshi ba ba karamin batanci bane a gare ki da shi baki ďaya, tashi ki tafi".

"Nagode Baba, Allah ya kara girma. In Sha Allahu zaka sameni mai bin maganarka". Tashi nayi na fita ina goge hawaye.

Bayan fitar Khadija daga sitting room ďinne Hajiya ta kalli maigidanta tace "amma dai Alhaji ba da gaske kake yi ba da kace zata koma gida idan an kwana biyu, iyayen ne fa suka koreta suka kuma ce basu yarda ta je gidan dangi ta zauna ba. Idan banda Allah yasa Goggonsu tayi tunanin turota nan da Allah kaďai yasan inda zata shiga".

Kallonta yayi yace "eh haka kika gaya mini amma ni a tunanina na nemi Mallam Hashimu na bashi hakuri ta koma gabanshi ta zauna, hannunka ai baya rubewa ka yanke ka yar. Ya zaiyi da ita ai dole ya karbi kaddara".

Hajiya tace "ba wai naki taka ba Alhaji amma ni a ganina mu kyaleta ta zauna anan ďin har zuwa lokacin da zasu nemeta da kansu, don wallahi da Adamu yake sanar dani wai iyayen sun koreta ba kaji yadda raina ya baci ba nace ina ganin dai 'ya'yan ne suka yi musu yawa shi yasa har suke neman kai dasu, nasan dai duk lokacin da hankalinsu zai dawo jikinsu sai sunyi nadamar korarta da suka yi kada ma dai uwar taji labari".

Murmushi yayi yace "Hafsatu tawa, a takaice dai kina so kice mini sai iyayenta sun wahala kafin ki bayyana musu 'yarsu, a ina kika taba jin anyi haka?" Dariya tayi tace "Allah kuwa Alhaji abin ne ya bani haushi, ai bai kamata ba a matsayinsu na iyaye su yanke wannan ďanyen hukuncin akan 'yarsu, to yarinyar da tayi haka a gabansu ma ya kake tunanin rayuwarta zata kasance a bayan idonsu. Ai korar nan da suka yi mata tamkar sun bata wani lasisi ne na kara lalacewa, shi yasa nace ka kyalesu har sai sun gano kurensu na korarta da suka yi, ai ba lallai bane sai ta hanyar kora ne zasu hukuntata akan laifin da tayi ba".

Yace "haka ne kuma fa sai dai kin san tunani ne kowa da irin nashi amma dai nima ban goyi da bayan ka kori ďanka ba a zuwan hukunci, sam hakan ba zai haifar da ďa mai ido ba. Allah dai ya rufa mana asiri ya kuma shirya mana zuri'a, yanzu dai dubi yarinyar nan irin bakin cikin data kunsa wa iyayenta. A yadda take ďinnan wa zaice zata yi abinda tayin?"

Hajiya tace "ai ka bar ďan yau kawai Alhaji amma ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, Allah dai ya shiryar mana da su" yace "Ameen" tare da mikewa yana cewa "bari na tashi nayi shirin fita kuma". Itama Hajiya tashi tayi ta ďauke tiren kayan abincin daya ci ta fita dashi.

Ina shiga ďaki na tarar da Humaira tana shiri ga alama dai fita zata yi. Nace mata "sai ina kenan?" ina mai kwanciya akan gado. "School zani, kinsan muna lesson saboda gabatowar waec. Ku ai kunji daďinku 'yan boarding babu ruwanku da wani lesson, a sanyin nan mutum yana so ya kwanta ya huta amma babu dama. Tashi muje ki rakani".

Kara lafewa nayi akan gadon nace "a'a jeki abinki don bacci nake ji, amma school ďinne kika yiwa wannan kwalliyar Humaira?" Dariya tayi tace "to menene, kinga tafiyata kada nayi latti" nace to sai kin dawo.

Tun bayan tafiyar Humaira makaranta nake kwance akan gado ina tunanin makomar nawa karatun, shikenan nasan yasha ruwa. Koda yake ana ta kai ma waye yake ta kaya, a halin da nake ciki yanzu wane karatu zan iya yi. Wannan wacce iriyar mummunar kaddara ce ta faďo mini haka da rana tsaka, wayyo Allahna wayyo ni Khadija yaya zanyi da rayuwata. Faruk  me ka sakani na aikata, gashi yau a sanadin bin son zuciya na aikata abinda yayi sanadin rabuwata da iyayen da 'yanuwana.

Kuka nake yi babu kakkautawa don gaba ďaya rayuwata a kuntace nake jinta. Na daďe ina kukan kafin na samu wani nannauyan bacci yayi awon gaba dani dama kuma jiya ban samu nayi baccin ba.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now