BABI NA ASHIRIN DA TARA

2.6K 197 21
                                    

Barakallu Feeki.. My baby is 8yrs old today. Happiest of birthdays Hibatullah, Allah ya raya ni naga aurenki har ma na goya 'ya'yanki. Belated happy birthday Uncle Immy Fari kyakkyawa, our one & only auta. Allah ya raya mana kai muga aurenka, a ranar akwai rawar tchounkousouma.


*29*

Ana kiran sallar Magriba Habib da tawagar abokanshi suka iso Kafin Madaki. wayarshi ya ďauko ya lalubo number Khadija don ya sanar da ita isowarshi. Tana ta ringing har kiran ya tsinke bata ďauka ba, kara gwadawa yayi nan ma shiru don haka suka wuce masaukinsu don su bada farali su kuma huta kafin su karasa wajen amaren.



Ana idar da sallah muka tafi gidan Aunty Saratu don dama na gaji da yawa, dauriya ce kawai nake yi. Muna shiga gidan na wuce banďaki don na watsa ruwa ko na samu na warware gajiya.


Doguwar rigar material na saka sai turaren cool water dana bi jikina dashi. Parlour na fito na zauna inda na samu Humaira da wata abokiyar wasanmu Zainab suna cin abinci. Zama nayi akan kujera. "Wash" nace tare da dafe kaina don wani irin sara mini ya keyi.


"Da kin daure kin ci abinci sai ki sha paracetamol ki kwanta, maybe idan kin samu bacci ciwon kan ya tafi don nasan hayaniya ce ta janyo miki shi" Humaira tace mini cikin yanayi na tausayawa.


"To" nace "amma fara bani wayata na tabo Yayanki don ya kamata ace tun ďazu sun iso gari, ban sam me ya tsaida su ba". Miko mini wayar tayi tace "ai kuwa dai naji an kira ki ďazu kafin na fito da wayar daga cikin jaka har ta tsinke shi yasa ban duba naga wanda ya kira ba".


Karbar wayar nayi na duba call ďin dana yi missing. Missed calls ďin Habib na gani har guda biyu, dialling number nayi ina jira ya ďauka. Sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ya ďauka. "Ina Sweetums ďina ta shiga tun ďazu nake kira bata ďauka ba" shine abinda yace mini bayan ya amsa wayar.


'Yar siririyar dariya nayi nace "wayar ma bata hannuna saboda hidima da tayi mini yawa, yanzu ma na ďauka don na kiraka sai naga missed calls ďinka don nayi zaton ko baku karaso bane".


Yace "mun karaso tun Magrib, yanzu haka ma na fito ne don nazo na ganki, ai kina gida ko?"


"A'a ina gidan Aunty Saratu saboda can hayaniya tayi yawa, ai zaka gane gidan ko? Ko kawai idan ba zaka gane ba ka nemi Yaya Adam sai ya rako ka".


"Ai inaga ma zan gane, don haka ki tsammace ni in like five minutes" yace tare da kashe wayar. Tashi nayi na shiga ďaki na gyara fuskata don kuwa ko mai ban shafa ba da nayi wanka.


Ina cikin ďakin naji wayata na ringing, kafin ma na taso na ďauka har Zainab ta shigo mini da ita tana cewa "Nour Ayn akan layi, oo su soyayya manya, wato hasken idaniyarki ko, babu ko kunya".


Tsaki nayi na warce wayata nayi maza na amsa don gab take da katsewa. "Fito gani a waje" yace bayan ya amsa sallamar da nayi mishi. Tashi nayi na fita. Ina jin Humaira tana cewa "ke kuwa ko ďan jan aji babu, daga kira sai fita".


Banza nayi na kyaleta don nasan neman magana ne take yi, yanzu da zan jinkirta fita da tuni ta fara mitar na shanya Yayanta a waje cikin sauro.


Yana jingine a jikin motarshi yana facing kofar gidan. Yana ganina ya saki murmushi yace "kada dai kice mini har kin cire kwalliyar bikin? Ni da nake ta faman sauri nazo naga kwalliyar biki tunda anki tura mini hotuna na gani".


Murmushi kawai nayi ba tare dana amsa mishi ba. "Ya hanya, yaya kuka baro su Hajiya?" na canja akalar maganar. "Kowa lafiya lau, Hajiya na can tana jiran zuwan 'yarta amarya" ya amsa mini cikin zoulaya.


BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now