BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

2.5K 193 16
                                    

Shirye-shirye ya kankama a gidanmu. Ni dai ido ne na nawa don kuwa a yanzu ko kawaye bani dasu sai dai 'yanuwa suma kuma dukkanin sa'annina na ďakunansu sai dai waďanda na girmewa.

Bayan dawowata dai nayi kokarin sanin inda Ramlatu take don na kai mata ziyara sai na samu labarin cewa a Kaduna take aure dole na hakura.


Shiri sosai Aunty Saratu take yi mini don a cewarta dole ne su gyarani yadda zan yi daraja a idanun mijina tunda na riga na wulakantar da 'yancina to dole ne suyi kokarin ganin sun saya mini mutunci a idanunshi duk da kuwa yasan wa zai aura ya kuma ce ya ji ya gani.


Wani magani ne Aunty Saratu ta saya mini a wajen wata kawarta mutuniyar Zamfara na sha ne dana tsarki, tace yana dawo da martabar mace ne irin waďanda akayi wa fyaďe ko wata kaddarar ta faďa musu. Idan dai har tayi amfani dashi In Sha Allahu zata haďe tamkar namiji bai taba saninta ba.


Goggo ma kuma ba'a barta a baya ba don magunguna take bani masu kyau da inganci waďanda yawanci ma da kanta take haďasu, har dahuwar kaza da kifi da kuma 'yan shila take bani. Kullum ne akwai kalar dahuwar da zata bani haďe da tsumi da kuma daka.


Ga wani fruit salad me ďan karen daďi da nake sha kullum wanda ake saka mishi zuma da ruwan zamzam a maimakon syrup sannan kuma ya haďa fruits ne fiye da kala goma. Aunty Saratu ce ta ďauki nauyin bani wannan fruit salad ďin, kullum ne sai ta aiko mini dashi ta kuma cewa Goggo ta tabbatar na shanye shi a ranar.


To ni ďinma bana kin sha saboda dama can Allah yayi ni mai son shan fruits ce. A bangaren gyaran jiki kuwa Umma ce da kanta take yi mini don dama ita ďin ma'abociyar yin gyaran jiki ne.


Har kallon kaina nake yi a madubi ganin yadda na yi wani fresh, sai kalar fata ta ta zama chocolate mai haske sosai.


Kullum ne sai mun yi waya da Habib, haka nan zuwanshi biyu bayan wancan zuwan da yayi har ma ya kawo mini invitation cards duk da ma ba wani taro zanyi ba. Kamu ne haďe da walima za'ayi a secretariat ranar alhamis, sai yini a ranar juma'a anan gida. Ranar asabar kuma za'a ďaura aure ne immediately bayan ďaurin auren kuma za'a tafi kai amarya.


Tun ranar talata Humaira ta diro Kafin Madaki da ďinkunan da zan yi amfani dasu, don dama ita nace Habib ya bawa kayan ta kai mini ďinki bayan dana ware waďanda zanyi amfani dasu daga cikin kayan lefen.


A ranar alhamis da safe mai kunshi tazo ta tsantsara mini design mai kyau na jan lalle, duk da bana son bakin kunshi sai da Humaira ta haďani dasu Aunty Saratu suka ce wai sai anyi mini don kuwa ni amarya ce, amarya kuwa da ado aka santa.


Haka nan ba don raina yana so ba na zauna aka yi mini sai don sun yi mini dole. Kasancewar event ďin namu na bayan la'asar ne yasa har muka samu muka yi kunshi a ranar. Humaira ce tayi mini kwalliya kasancewarta gwana ce kwarai wajen iya tsara kwalliya tamkar dai wacce taje tayi course akan kwalliyar.


Cod lace na saka kalar baki da aka yiwa ado da duwatsun pearl kalar silver tsalli-tsalli a jiki. Ďinkin buba ne da zani sai nayi tucking in rigar a cikin zani wato dai na ďaura zanin a saman rigar kamar yadda akasarin mutanen kudu ke yi.


Asoke nayi amfani dashi kalar silver da aka yiwa ado da beads kalar baki a jiki. A naďe Humaira tazo mini dashi, sai mayafin asoken da aka zagayo dashi ta kafaďata ta dama zuwa bayana aka makale shi da safety pin ta gefen cikin daga hagu.


Clutch bag ďina da stilettos heel ďin dana yi amfani dashi ma kalar silver ne. Katon mayafi kalar silver aka rufa mini a kaina ya rufe har fuskata sannan Humaira ta kama hannuna ta kaini wajensu Umma muka ďauki hotuna kafin muka wuce wajen kamu/walima a can secretariat ďin.


BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now