page 3

188 9 0
                                    

🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
☘☘☘☘☘☘☘
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
☘☘☘☘☘
🍁🍁🍁🍁
☘☘☘
🍁🍁
  *LABARIN RAYUWATA.....*✍🏽

Story and written by
*нαℓєємαтυѕ-ѕα'α∂ιууα*🤸🏾‍

_Sadaukarwa ga *Labarin rayuwata* fan's I hrt u big❤_


Page *3*


Farha harta mike jin datayi Baba tace mata"akwai goriba wacce uwarta tabar mata gado"Saita cigaba da wanke2 ahaka harta kusa gamawa."wllhi kiyi sauri kigama dan naga bakizo kan tukunyaba domin girki zan Dora idan kuma nagaji da jiranki to kezaki tuka tuwan dan uwarki"Tafada tana tallewa Farha keya.

    "Salamu alaikum" Jawahir tayi Sallama."wa'alaiki salam"Farha ta amsa tareda fara'a a fuskarta.
"Besty na Sannu da aiki bara natayaki" Jawahir tafada tareda sa hannunta tana taya Farha wanke2...."ki tayata uwarme ko nace uban me dallah malama tashi kibar gidan nan tunda daga ke har yar wahala ba gidan ubanku bane fita nace gadon rashin tarbiyya wllhi sai inci gidanku fitsararriya"
Duk wannan maganar da baba keyi jawahir ko kallonta batayiba dan haka ta tunkarota tana fadin"bakar muna fuka badake nake magana ba kaga yarinya Mara tarbi......ya isheki lami duk abunda zamuyi karkisa iyayena domin tunda kke mgnarki bansa  miki bakiba dan haka karki kuskura kisa iyayena."

"Kuji yarinya ya kusun uwa,wata faraha kece kika kirata tamin fitsara ko toh wllhi yau saina miki dukan mutuwa dan haka kiyafewa kanki kuma kisallama kanki dan yau babu mai karbarki sai Allah......"" Sai kuma ni" cewar Jawahir domin wllhi indai inada rai babu Wanda ya isa yadaki Farha ina wajen sai mahaifanta kuma sun mutu dan hka kema kishafawa kanki lafiya kirabu da ita domin wllhi kika daketa yau sai anyi yar kunce gidan nan"Yar kunce dani"baba lami ta nuna kanta da hannu"to wllhi nidai Saidai nayi kunce da uwarki wllhi ...."Dallah Farhaty zomu tafi akwai wani gist danakeso nabaki"waje Jawahir tajata saida sukayi nisa sosai da gida sannan tace "Yusuf ne yakirani awaya yace yanason mgna dake"Ai tun kafin jawahir tarufe bakinta Farha tawashe baki cikin fara'a tace kiraminshi,waya jawahir tadauk daniyyar kiranshi sai gashi yakira nan Farha tadauka tana fadin"Assalamu alaika ya nurul khalby"cikin wata murya da bansan Farha Nada itaba.
Chankuma takuma cewa Saikazo amma kayi sauri kasan yanxu sai baba tadakeni.

_Five minutes later_

Motace tayi parking daidai inda su Farha suke zaune hango motar datayine yasa tasaki wata ajiyar zuciya alamar jin dadi dan hka ta kalli jawahir tace"Besty wllhi Allah yataimakeni yazo da wuri da wllhi dukana baba zatai"hararar jawahir tayi tana fadin wllhi haushi kike bani akan wannan tsoran naki ai ni dayake idan tamin tasan hauka nake mata ai tana shakkata amma ke kullum cikin yimata kuka dole tadinga suburbidarki."Ai wllhi dazu dariya nakusa nayi dakikace idan ta dakeni saikin ramamin amma duk da hka gabana bai daina dukan sittin sittin ba.
"Salamu alaikum"
Yusuf yayi musu sallama cike da nutsuwa"
"Wa'alaika Salam jawahir ta amsa yayinda Farha tasakar masa murmushi mai dauke da sakonni.

" kawarmu ya kike"cewar Yusuf
"Lafiya kalau Angon Farha"
"Wai dazu yarinyar nan tacemin nayi sauri kar  baba tadaketa wllhi abun yaban haushi ace kamar ita ana dukanta bama mamantaba wata katuwa chan to wllhi nidai zan turo daga gidanmu ayi mgna da iyaye akan maganar aurenmu domin gaskiya bazan jureba adunga dukarmin Matata"
"Murmushi jawahir tayi sannan tace ai abun haushinma sai dazu wllhi sainice nashigar mata" tafada tana kwashewa da dariya,itadai Farha sai binsu take da ido Amma tunda yayi zancen aure gabanta ke faduwa kuma tarasa dalili.Ledodin dake hannunsa yabude wacce dayar aka rubuta Y&F Communication Center (Yusuf and Farha) inda dayar kuma shawarmace da yoghurt na L & Z .zaro wayar dake cikin dayar ledar wayace mai kyau kirar NOKIA X yakunna yana fadin"nasata tayi chargi sosai da sim aciki nayi Saving number na data Mamana inaso ki kirata ki gaisheta,wannan kuma kobaki fadaminba nasan yunwa kikeji kuci keda kawarmu."Ai bai rufe bakinsaba saiga jawahir da gudu takaraso tana fadin Farhaty tashi ki gudu ga baba lami nan"tashin hankali ba'asa maka rana nan da nan idon Farha yafito waje tama manta gabanwa take dan haka ta kankameshi tana fadin dan Allah karka bari tadakeni tana kuma kokarin shigewa motarsa....daidai lokacin da baba takaryo kwana,tareda rafka Salati...Yau mai zangani Farha Zina kikeyi(readers wai zina)yau nashiga uku na lalace Farha kodai mafarki nakeyi to wllhi yau asirinki ya tonu wllhi saina gayawa mamuda wllhi karuwace ke tun lafin kiyi abun kunya yamaza ya aurar dake karki lalace mutane suga laifinsa"Wllhi baba ba haka bane cewar Yusuf yarinyarnan tsorata tayi kin taho tasan dukanta zakiyi shiyasa take kokarin guduwa"duk hanyarnan bata guduba sai jikinka eyeee nace sai jikinka wllhi yaudai tafaru takare wllhi aure zai miki ko yyi sadakarki a masallaci Wllhi ki saurara indai nacika lami yau da asuba babanki zaiyi sadakarki masallaci.

   A haka Farha tabi baba lami gida ko wayar bata karbaba talkless of shawarma and yoghurt haka taci uban duka kamar zata mutu .bayan Malam Mahmoud yadawo baba lami tana kuka tana gayawa masa abunda yafaru inda tabashi shawarar a yau da asuba yayi sadakarta gamaiso a masallaci bayan ya Nada mata najaki.

     05:45AM daidai da lokacin da ake shiga sallah dan haka kowa ya hallara a masallaci kamar sun San da wani Abu dan haka ana idar da sallah Malam Mahmoud yace yanada magana dan Allah kowa ya saurareshi nan kowa yabada hankalinsa Malam Mahmoud yafara magana kamar haka"Idan yarinya mai suna Farha dafatan kun shaidata"nan kowa yabude baki yace eh munsanta nan take wasu daga cikinsu suka fara fadin halayenta na gari"Dan Allah Ku saurara"Malam Mahmoud yayi magana "Dan Allah idan damaiso yafada zan bashi ita kyauta" Nan masallaci yayi shiru sai wata murya tace"inasonta kuma zan aureta....


Reader wai wannan muryar waye

LABARIN RAYUWATAWhere stories live. Discover now