page 4

161 5 0
                                    

  LABARIN RAYUWATA

PAGE 4

   Ina Santa kuma zan aureta.....gaba daya mutanan dake masallacin saida suka juyo suka kalli Mai maganar Wanda kanaji kasan Yusuf ne.
"Kanasanta?" Malam Mahmoud yamaimaita "Eh ina Santa"
"To ai bakajira nagama magana ba dan saurayi,ina nufin a yanxu za'a daura auren yau da asuban nan kadauketa kutafi" Na yadda kuma na amince"inji Yusuf.
Toh jama'ar masallaci zaku zama shaidu yaro wani waliyyinka"Ni Alhaji Muhammad Abubakar nine Alwalinshi"Cewar wani mutum dake zaune kusa da Yusuf yafada.cikin mintuna da basu Gaza 10 ba aka daura auren Yusuf Muhammad Abubakar tareda Matarsa Farha Mahmoud  Muhammad akan Sadaki dubu 100.

   Tunda baba lami takasa kunne tana sauraron masallaci Take murna domin tana tunanin tagama wulakanta farha har aka fara daura aure murna take sai lokacin dataji an ambaci sunan uban Mijin Farha wato Muhammad Abubakar taji gabanta yafadi domin tasan hamshakin mai kudine sosai ansanshi wajen taimakon marasa karfi.Tuni jikinta yayi sanyi.

   Ana gama daurin aure Malam Mahmoud yafara kame kame domin baizata haka abun zai kasanceba zancen zuci kawai yake  sai ji yayi Alh.Muhammad yace Adauko mana amaryar mutafi da ita domin sauri nake yau zanbar kasar nan.Mikewa Mahmoud yayi yafita daga masallaci yana yin hanyar gidanshi yana shiga yatarar dasu a tsaye kowa yayi shiru ai kuwa baba lami tace "Malam haka mukayi dakai kanaji Alhj.yafadi sunanshi mai makon kace sunan yar Sa'adatu sai adaura da yarka amma sai kace Farha yanxu yarinya ta auri dan Masu kudi,yau nashiga uku na lalace"
"Malam baki shiga ukuba burinki tabar gidan kuma gashi zata bari ai shikenan Farha fito mutafi" kuka Farha tafashe dashi Wanda duk wani mai imani idan yaji saiya zubar da hawaye,sotake tayi magana amma gani take kamar idan tayi zuciyarta fitowa zataji dan haka ajiyar zuciya kawai take.ahaka yajata tabar gidan gari ko gama wayewa baiyiba yaje yamikata a hannun Yusuf tareda fadin gatanan Amana nabaka kuje Allah yayi muku albarka"Farha dagewa tayi ta kwallawa Jawahir kira,Sannan takuma fashewa da kuka.

  Jawahir kwance a gidansu tana bacci amma jitake kamar ana kiranta dan haka ta mike tsaye zata fita mamansu tariketa tana lafiyarki daga tashi zakiyi waje?"umma kirana ake muryar Farha nakeji kamar tana kirana "to bazakiba dan ubanki" bata tsaya jin sauran bayaninba ta iba da gudu tayi waje ummansu tabita amma ina tayi mata nisa in banda sunan Farha babu abunda Jawahir ke kira itama kuma kiranta tayi dan haka suka hadu tareda rugume juna abun tausayi kace rabasu za'ayi har abada daker aka rabasu aka tafi da Farha gidan MijintaYusuf baice affanba sai sharewa Farha hawaye yake haka suka isa har Shagari  quarters gidansu Yusuf Farha tana kuka ,horn akayi mai gadi yabude suka shiga driver yasamu wajen yayi parking.

   Fitowa sukayi daga motar sunayin hanyar cikin gidan,shiga sukayi suka tarar da mama akan 3seater din dake falon da murmushi ta taresu amma ganinsu da budurwa tare yasa tace "wannan pretty din kuma daga ina zo yan mata wllhi harta shiga raina " tafada tana karasowa inda Farha take tareda rike hannuntaYan Mata yasunanki?"Sunana Farha"masha Allah Farha Alhaji a ina kasamo mana wannan pretty din hka"Murmushi yayi yana azuciyarsa yace Alhamdulillah da alama tanason yarinyar dama matsala daya itace kuma gashi cikin sauki tana sonta"Surukarkice matar Yusuf.
Cika hannun Farha tayi tana fadin Badai Yusuf dinaba wllhi ....

LABARIN RAYUWATAWhere stories live. Discover now