GAMON JINI 55 to 60

195 11 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

5⃣5⃣ to 6⃣0⃣

Qarasawa sukayi wajen masu daura auren,maganganu suka yi, amma abin mamaki maimakon a dakatar da daurin auren sai naji ana sanar da daurin aure a speaker har an daura.

Bayan gama daurin auren su dad suka pito ana ta gaishe gaishe tare da sallamar baqinsu,mubarakh duk hankalinshi ba'a kwance yake ba rashin ganin abdul a wajen,a haka dai suka shiga mota domin tapiya gida,gidansu fadeelah suka qarasa da yake ba nisa da masallacin da aka daura auren.

Ganin hadda su dad akazo gidan yabawa mubarakh mamaki,bai qara tsinkewa da lamarin ba sai da yaga  kabeer yashiga cikin gidan tare da su dad.

Fadeelah da tunda aka tapi daurin auren take daki tana ta kuka,ta para jiyo hayaniyar maza,hakan ya tabbatar mata da an daura an dawo,wani irin kuka ta qara pashewa dashi na rabuwa da ummanta,salamatu ce matar kabeer da matan qannen babanta suke rarrashinta,jin angwayen sun iso ne yasa suka tashi suka pito tsakar gida.

Wata shadda ta saka hot pink,wacce tasha aikin riga da zani,tana cikin kayan da mubarakh ya dinka mata sanadin ba'ai mata lefe ba,sky blue din mayafi aka yafa mata mai duwatsu,tayi kyau sosai cikin shigar sai dai idanunta da suka kumbura saboda kukan da tasha.

Kasancewar ba 'yan uwan ummanta a gidan ya zamana sai tsirarun mutane ne a gidan,don maqota basu para shigowa ba,kabeer ne ya para shigowa gidan dad yana biye dashi sai mubarakh.

Umma tana tsakar gida wajen da ake girkin daurin aure,sallamarsu dad ce ta sata waigawa wajen qopar don a tunaninta kabeer ne da yayyenshi,ganin dad da tayi ne yasa ta pirgita,sulalewa tayi a qasa,da sauri yazo ya tareta ya dauketa cak,kabeer ya nuna masa dakin da zai kaita ya nupi daki da ita.

Ganin daukar da dad yai mata shi ya qara bawa mubarakh mamaki,yana da tambayoyi da yawa acikin ranshi amma yanxu ba lokacin tambayar bane.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Abdul tun da yaxo wajen daurin auren yaji kanshi ya tsananta ciwo,duk da kusan kullum yana tare da ciwon kai amma nayau ya tsananta da yawa,mota ya koma ya zauna,sai yaji alamun jiri na diban shi,tayar da motar yayi cikin ikon Allah ya isa gida lapiya,hidimar da ake a cikin gidanne yasa ba wanda yasan da shigowarshi,a daddafe ya shiga part finshi ko takalmi bai cire ba ya pada kan gado yana jin wani tuquqi a qirjin shi,daga nan bai qara sanin abinda ya paru ba.

Hanan kuwa tana nan a daki ba yadda ba'ayi da ita ba ta pito taqi pitowa,in banda kuka ba ba abinda take,tana jin zuciyarta kamar zata pasa qirjinta ta pito sbd son mubarakh da kuma kishinsa.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Dad ne ya qarasa da ita cikin dakin ya kwantar da ita,bin dakin yake da kallo hawaye yana saukowa daga idonshi,kabeer ne ya miqo masa ruwa ya shafa mata a fuska,take ta sauke ajiyar zuciya idonta ta bude ta saukesu akan dad adai dai lokacin da wani kuka ya qwace mata,kuka take iya qarpinta ta kasa cewa komai haka shima dad ya kasa cewa komai,mubarakh yana tsaye yana kallon ikon Allah fadeelah ta fado dakin da gudu tazo ta tsugunna akan ummanta ba tare da ta kula da kowa a wajen ba har dad.

"Ummata ki tashi dn Allah,ki tashi,bani da wani gata saike sai Allah,ke kadai nake dashi a duniyarnan,ki tashi umma" ta fada cikin sautin kuka tana qara rungume ummantata.

Mubarakh ne ya qaraso inda take ya durqusa a hankali dai dai kunnenta.

"Gimbiya ki yi haquri,ummanki lapiyarta qalaw,ki tashi"

A hankali ta dago fuskarta ta kalleshi,ta koma kan ummanta ta kalleta,kukanta takeyi har yanxu,dad ne yace

"Mubarakh dauki fadeelah ku tapi gida"

Cikin rashin pahimta yake kallon dad,ganin hakan da dad yayi ne yasa ya qara cewa

"Ku tapi gida muma yanxu gamu nan xuwa"

Fadeelah ce ta cigaba da kukanta jin ance a tapi da ita,ji tayi umma ta riqo hannunta,kallon ta tayi ta gyada mata kai alamar ta taje,miqewa tayi mubarakh ya riqe hannunta suka pito yasa ta a mota suka dau hanyar gidansu.

Bayan tapiyarsu ne dad yace ma umma itama ta taso su tapi,ba musu ta tashi ta maida mayapinta suka pito waje,cikin motar dad ta shiga su ka bi bayansu mubarakh.

Kabeer ne ya tsaya don yiwa matarshi bayanin abinda ya paru,girkinsu suka cigaba dayi ba tare da wata matsala ba,nan aka cigaba da gaishe gaishe amma ba amarya ba ango ba kuma uwar amarya.

Mubarakh da tunda suka taho ba mai magana a cikinsu,fadeelah kukanta kawai takeyi inda shikuma rashin pahimtar abubuwan da suke paruwane ya dameshi,ko da yazo gida kasa shiga gidan yayi ya samu waje yayi parking a waje yana jiran su dad su qaraso.

Sun dan dauki lokaci a wajen kapin suka qaraso,a tare motocin suka shiga gidan,suka pito dukansu,dad ne ya nupo part dinshi da umma,ganin haka yasa mubarakh ma suka bisu da fadeelah.

Shiga sukayi har yanxu idon umma bai daina pitar da hawaye ba,zama sukayi akan kujerun parlon inda ita kuma fadeelar ta zauna a qasa kan carpet.

A part din mommah ba wanda yasan da shigowarsu,dad ne ya aika mubarakh ya kira mommah,pitar da yayi ya shiga cikin part dinta nan pa aka para tsokanarshi ango ango,can idonshi ya gane mishi ita,yaje ya sanar da ita saqon dad,yana pitowa maimakon ya koma sai ya nupi part dinsu,shigarsa ya tarar da abdul a kwance,murmushi yayi yace

"Mr rashin son jama'a,daurin auren nawa ma kasa zama kayi"

Takalmin  da ya gani a qaparshi ne yasa ya dan qarasa da mamaki akan puskarshi,tashinshi ya para yi sai sannan ya gane cewar a sume yake,da gudu ya koma parlor ya bude fridge ya dauko ruwa ya dawo ya shafa mai a fuska,bude idonshi yayi a hankali mubarakh ya para tambayarshi

"Me ya sameka abdul,ciwon kan ne??"

Gyada masa kai kawai yayi,pita yayi don ya sanar da su dad abdul bashi da lapiya.

Yana zuwa ya tarar da mommah a kusa da umma,itama tana hawaye sosai,qarasa shigowa yayi yace

"Dad dama abdul ne ba lapiya"  cike da tashin hankali dad yace

"Me ya sameshi,ba tare kuke a wajen daurin auren naku ba??"

"Dad tun da mka je na neme shi na rasa sai yanxu da na shiga na tarar ya suma,amma......"

,ai dad bai tsaya jin qarashen abinda mubarakh zai ce ba ya pita daga dakin,bin bayanshi mubarakh yyi suka pita,basu jima ba sai gasu tare da abdul sun dawo,saboda sunyi sunyi akaishi asibiti yace a'ah,qarasowa sukayi suma suka zauna a qasan kujerar da dad ya zauna.

Marriam mayshanu 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now