GAMON JINI 98

215 12 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽
                   *GAMON JINI*
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

_May this day be the beginning of another beautiful year for you. May there be pleasant surprises, loads of joy and infinite happiness.Wish you a very happy birthday,happy birthday adamsyy #long life and prosperity,kayi girma irin na dabino_🎂🎂🎂

9⃣8⃣

A kwana a tashi ba wuya yau monday da ta kama fadeelah zata para zuwa makaranta,tare suka shirya da rukhy cikin uniform dinsu riga ash da wando baqi,baqar socks sai hijabi shima ash amma na fadeelah yafi na rukhy sauka sosai,fitowa sukayi parking lot suka nupi motar da ake kaisu skuul,horn sika jiyo daga bayansu suka juya suka hango shi zaune cikin mota kasancewar shima yau zai koma aiki,rukhy ce ta juya ta koma inda motarshi take inda ita kuma fadeelah ta tsaya a wajen tana jiran ta dawo,dawowa tayi taja hannunta suka tafi wajenshi,tana zuwa ta bude gaban motar ta tura ta ta rufe ta koma cikin motar drivern da yake kaisu skuul.

Dai daita zamanta tayi cikin motar ta juya inda yake sai a lokacin taga ita yake kallo,dauke kai tayi sannan tace

"Ina kwana"

Bai amsaba yace "uniform dinnan sun miki kyau sosai,anya baxa'a fasa zuwa skuul dinnan ba"

Dago kai tayi ta turo baki gaba amma ta kasa cewa komai

"Maida bakin toh" ya fada da 'yar dariya ciki ciki ya tada motar suka fito daga gidan,hanyar skuul dinsu ya dauka suna tafe yana mata surutu,itama sakewa tayi dashi suna ta hira har sukazo qofar skuul din,parking yayi ta bude qofa zata fita ya riqo hannunta,tana juyowa sukai ido cikin ido kasa dauke idonta tayi yayin da shima kuma ya dage yana aika mata sakonnin soyayyarshi ta cikin idonta,horn din wata mota da ke wucewa ne ya dawo da ita cikin hayyacinta ta zare hannunta cikin nashi ta fita daga motar,ganin ta fita shima ya fito xuwa inda take suka fara tafiya tare har sukaxo gate din ya tsaya,itama tsayawar tayi,hannu yasa a aljihu ya ciro bundle din 50naira ya miqa mata

"For d week" bata karba ba ta girgixa kai

"Mommah ta bamu"

"Na sani,wannan daga wajen mijinki ne,kafin ta qara cewa komai ya bude skul bag dinta ya jefa mata kudin yace

"Gobe ma kar kibi driver ni zan dinga kawoki" ya juya ya shiga mota ita ma ta shiga cikin skull din,tayi sa'a tana shiga rukhy ta hango ta ta fito suka koma klas din tare.

Ba Sosai take gane karatun da akeyi ba,tana da qoqari amma matsalar ta turanci,don malaman makarantar da tayi ba sosai ake musu turanci ba,kuma wannan skuul din tasu hausawan teachers din basu da yawa,sai turawa da larabawa,hakan ne yasa bata ganewa sosai,amma taji dadin zaman ajin ko dan rukhy har aka tashi suka fito tare driver ya dawo daukar su,kafin su shiga motar ne suka hango shi yana qarasowa wajen, parking yayi ta wuce ta shiga ya kaita gida

A hanya ya ke tambayar ta ya skuul din ko taji dadin ta,alhamdulillah dai tace mai,itama ta mai ya aiki,hira suka dan taba kafin nan suka qarasa gida ya sauke ta ya koma office.

Bayan ta shiga gidan ta tarar da rukhy har tayi wanka ma,ta sa uniform din islamiyya ta fito dining cin abinci,zaro ido tai tace

"Sis har kinyi me??"

"Har na shirya tunda ni ba soyayya na tsaya yi ba" ta fada mata tana mata dariya,hade rai tayi tace

"Waye ya tsaya soyayyar??"

"Nima ai ban fadi suna ba"

"Za ma ki fada ne" ta fada tana shigewa daki,itama wakan tayi ta dauko qaton hijabinta kalar uniform din islamiyayr su rukhy don ita bata sa uniform sai hijabi kadai ta fito rukhy har ta gama cin abinci,zama tayi itama taci abincin sannan suka fara zuwa dakin ummanta suka gaisheta,sukaje wajen mommah ma suka gaisheta suka fito tafiya makaranta,a waje fadeelah ce ta tsaya rukhy ta shiga part dinsu khadija ta kirawo su ganin basu fito ba,tare suka fito da khadija,fareedah,nabeelah,nabeel sai rukhyn,qarasowa sukayi inda fadeelah take khadija tace mata

"Yau yaya ya hana mu ganinki,tunda ya hanaki bin motar mu"

Dariya tayi tace

"Gashi nan ai kun ganni yanxu tunda zuwa islamiyya tare"

Fita sukayi da yake makarantar ba nisa da gidansu suna hirarsu har suka je,kasancewar fadeelah ita hadda takeyi yasa ba ajinsu daya ba,khadija da ruky ajinsu daya sai fareddah da nabeelah aji daya,nabeel kuma shi kadai ajinsu daban.

Bayan sun dawo daga islamiyya da daddare, fadeelah bata ji kunyar ta fadawa rukhy cewar ba sosai take gane turanci ba shiyasa yau a skuul ba soaai take gane me ake ba,don yanxu sun zama daya sosai kamar uwarsu daya ubansu daya suna taimakon juna,hakan ne yasa rukhy tace zasu dinga yi a gida,har ta koyi turanci.

Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,inda abdoul tunda mommah ta mai kashedi bai qara jan fadeelah dakinsa ba,kuma yanxu tana zuwa makaranta shima yana zuwa aiki saboda hka sai da safe wajen tafiya makaranta da wajen dawowa suke haduwa.

❣❣❣❣❣❣❣❣

Mommah ce a dakin dad ta ke mai maganar tarewar su abdoul da fadeelah,dad cewa yayi sai ta yi candy,akan hakan suka tsaya don bata son yai magana tai masa musu,suna zaune suna hira wayar dad ta dauki qara dubawa yai yaga sunan *Dr abdulmaleek* murmushi ne ya sauka kan fuskarsa ya daga wayar ya ce

"Likitan likitoci"

gaisawa suka fara yi sannan ya bawa abdullahi wayar shima suka gaisa,albishir din gama skuul dinsu sukai mai nanda wata daya,fatan alkhairi yai musu da alqawarin zuwa cyprus don bikin convocation dinsu,cikin farin ciki ya gama waya da 'ya'yan nasa ya ajiye wayar yake sanar da mommah yadda sukai da yaran,itama farin ciki tayi da fatan alkhairi.

Marriam mayshanu  👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now