GAMON JINI 25 to 30

197 10 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽 *GAMON JINI*💃🏽❤💃🏽
❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽

         By miss_marriam⚜
Dedicated to *phaty danlawan*

_ina kuke fa'iza getso, maman ashkur,wannan page din naku ne,nagode da qaunar book dina da kuke,Allah ya bar zumunci_ ILYSM

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

2⃣5⃣ to 3⃣0⃣

A haka dai mubarakh ya dauki hanyar gida ba don yaso ba,suna shiga gida abdul ya pito da qyar yake jan qaparshi ya shiga part dinshi ya kwanta akan gado yana jin kanshi da nauyi,tunanin shi yadda za'ayi ya cire sonta a zuciyarshi don ya riga ya sawa ranshi ya haqura da ita.

Mubarakh kuwa yana kashe motar baibi abdul ba ya tapi part din mommah,ko da ya shiga tana kitchen,sallamarshi data jiyo ne yasa ta pito daga kitchen din.

"Mubee,kun dawo"

"Ehh mommah,sannu da gida"

"Ina abdul din na ganka kai kadai" ta tambaya

"Yana daki,baya dan jin dadi ne,abinci dama nazo daukar mai yasha magani"

"Subhanallahi,mai ya same shi??"

"Ciwon kai ne"

"Toh Allah ya sawwaqe,ga abincin nan a dining an jima zan shigo"

"Amyn"

Dining din ya nupa ya zubo abincin a plate ya rupe da wani plate din ya pita zuwa part dinsu.
Yana shiga dakin ya tadda shi a kwance ya lumshe ido kamar mai bacci amma a zahiri ba baccin yake ba,tunani yake don bai ma ji shigowar mubarakh din ba.

Ganin kamar yana bacci ne yasa shi ajiye plate din a bed side drawer ya shiga toilet,rupe qopar toilet dince ta dawo da abdul daga tunanin da yake ya bude ido.

A haka har mubarakh ya pito

"Ka tashi,ga abinci kaci sai kasha magani"

"Ban iya ci"

"magani pa zaka sha,kuma baxaka ci abinci ba"

"Ban iyawa" kawai yace a taqaice

"Zan kira mommah toh" Shiru yayi bai qara cewa komai ba,ganin haka ya juya ya pita ya bar dakin,bai jima ba suka dawo tare da mommah hankalinta a tashe ta qarasa kan gadon da yake ta dapa kanshi

"Abdul,tashi mu tapi asibiti"

Bude idonshi yayi ya rupe a hankali yace

"Mommah ciwon kai kawai nke,idan na huta zai tapi"

Ba don ta yadda ba ta janyo plate din abincin da ke gepenta

"Tashi kaci abinci toh"
ba musu ya tashi ya zauna ta dauki abincin ta para feedin dinshi,ci kawai yakeyi ba don yana jin dadinshi ba,kadan yaci yace ya qoshi,mubarakh ya miqo wa mommah magani da ruwa ta bashi ya sha,ya koma ya kwanta,sannan ta tashi ta pita.

Bai dade da kwanciya ba aka kira sallar maghrib,hakan ya tashi yai alwalaa suka pita masallaci,akan hanyar dawwarsu ne mubarakh yake ce mai

"Abdul wai wane irin so kakewa yarinyar nan ne,duk gaba daya kabii ka canxa,nasan wannan ciwon kan naka ma tunani ne ya jawo mka shi" jin yayi shiru ne ya dapa kapadarshi ya ci gaba

" gobe sai muje skul din tasu da kace mu nemeta ko in an tashi"

"Mubarakh ni ba sonta bane yake damuna pa,kawai dai rashin lapiya ce,kaga ni nama manta da ita,ka qyaleta kawai ba sai munje ba"

"Me kake nupi?? Wai kuma yanxu ka daina sonta?? Ko kuma ta daina damunka da tunanin ne?? Duk ya jero masa wa ennan tambayoyin.

Girgiza kai yayi
"No,let's keep d issue aside"

"Ohk,as u wish"

Suna qarasowa daki ya kwanta,har yanxu baya jin kan nashi dai dai,mommah ce tai sallama ta shigo dakin

"Mubee ya me jikin"

"Da sauqi mommah"

Qarasowa tayi ta zauna

"Ya jikin naka??"

"Da sawqi"

"Abbanka zaizo anjima"

"Yeah mun hadu a masallaci daxu"

"Ohk,xan aiko rukhy da abincinku yanxu sai ka qara maganin"

Ta kalli mubarakh"ka tabbatar yasha maganinshi,idan yaqi sha kazo ka fada min"

"Toh mommah" Ta juya ta pita daga dakin.

Marriam dianah 👌🏻

GAMON JINIWhere stories live. Discover now