HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI...1 BY SARATU M. SANI SERIES 1

2.7K 92 10
                                    

KANO Kyakkyawar yarinya ce cikin motar direban ta na tuki, a hankali wanda anata bangare waya ce a hannun ta tana faman latse-latse a dai-dai lokacin ne direban ya yi horn bakin gate din wani katafaren gida. Mai gadin ya yi hanzarin budewa, direban yashiga da motar ciki sosai sannan ya yi parking ya fito hadi da saurin zagayowa ya bude gidan baya ta fito. Yarinyar wacce taci sunan ta Farida za tayi kimanin shekaru shatara zuwa ashirin cif! Kyakkyawa ce a jin farko,ta na da kyawun siffa uwa uba iya tafiya, fannin magana sam-sam ba tada yawan magana, magana ma cewa kake wuyar ta ta ke idan kaga tana wani dan dogon zance, da Dad din ta take Magana ko kuma Mom din ta, sai dai tafi yawan Magana da Yayan ta. Haka ko a cikin mutane take yana da wuya kaji maganar ta, tun kawayen ta na darnuwa har suka yi sabo da halin ta, idan ana Magana cikin kawaye sai idan anyi maganar da zata bada dariya, ko shi din iya kacin ta murmushi. Duk wannan sai ka zauna da ita za kasan ba tada girman kai sam-sam, a kwai ta da natsuwa, tausayi da kuma girmama na gaban ta ko mai talaucin sa. Iyayen ta na ji da ita suna matukar kaunar ta musamman Dad din ta ya tsani abin da zai bata ma ta rai, ba halin ta ce kan ta ke ciwo yan zu kaga rudewa wurin iyayen, suna ji da ita tamkar kwai a cokali. Duka duka watan ta uku a halin yanzu da karnala first digree din ta fannin mass. corn. a jami'ar B. U. K. Alh Yahya, dattijo mai sanin ya kamata matan sa biyu, Haj. Balki it ace,,, uwar gidan sa ta na da Ya'ya takwas biyar maza uku mata.sai kuma Haj. Haulatu Ya'yan ta shida . Dattijon ya bawa Ya'yan sa gwargwado tarbiya ta gari kamin rasuwar sa, wanda daga baya itama Haj haulatu tabi bayan sa, rayuwa kenan. AIh Ibrahirn, wanda ya yi fice, a wurin naira shine da na biyu a cikin gidan yana bima yayan sa kabir kenan. Matar sa daya rak! Hajiya Amina Ya'yan su biyu Mukhtar da kuma Farida. daga baya ya gina wani ma dai- dai cin gida kusa da nashi ya saka mahaifiyar shi. Tsarin Alh sam baya ma'amala da talaka, bai dauki talaka bakin komai ba, abin da ke hada shi da Farida kenan ta cika hulda da diyan talakawa, sai dai sam baya iya hana ta gudun kada ya bata ma ta rai. Abin takaici akwai ranar daya taba fita tare da ita, lokacin tana aji shidda a secondary wata Yarinya ce dauke da ruwa ga kai, da sauri Farida ke ce ma direban ya dakata, ba musu direban ya dakata Dad din ya dube ta ya ce, "lafiya 'yar gidan Daddy? Kamin ta bashi amsa saida ta bude motar sannan ta dan yi murmushi "Dad kawata na gani zan gaisa da ita, ta yi saurin fita ta fara kiran Humaira , wacce ke kokarin tsallaka titin, ta juyo domin taga mai kiran na ta ga mamakinta sai tag a Farida , ta dakata hadi da gyara ruwan dake kanta. Farida ta iso kusa da ita tadan yi murmushi a hankahi maganar ta ta ke fitowa ," Humaira kwana biyu bamu hadu ba, ina yawan zuwa gidan ku bana samun ki," Humaira ta ce "Farida kinsan akwai sabani wurin haduwa, sai dai Mama na gayamin kin zo," Farida ta ce, "shine kuma har yan zun kin kasa zuwa gidanmu?. Sun dan taba hira sama-sama Dad ya ga alamar zata tsaida shi ya sa direban ya rika yin horn, farida ta ce,,, "sai na zo" ta nufi motar ta shiga suka cigaba da tafiyar ba halin ya yi mata Magana dole yanzu ya hakura da dabi'un ta. Wanda a yanzu bata da wata kawa da ta wuce mata Humaira har tayi aure kawancen su bai yankeba ta na yawan zuwa wajen ta, hadi da kyautata ma ta. Farida kenan. Read more @ www.share4world.com.ng

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 14, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAUSA NOVEL BOOKS: RASHIN SANI...1 BY SARATU M. SANI SERIES 1Where stories live. Discover now