بسم الله الرحمن الرحيم
اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاتهSharhi:- Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma ince bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina.
Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙiri duk wani SUNAN da na gina labarin a kai, kamar sunan makaranta, sunan kamfani da ma sunayen jaruman littafin. (Note, SUNA kawai, dan duk wani abunda ya samu jaruman littafin, zai iya samuna, ya sameka/ki idan har halin mu yazo iri ɗaya da na su)
Mas'ala ce wanda dole wurin isarwa sai ka yi takatsantsan wurin zaɓen kalmomi, hakan ya sa na ke ɗaukan kowacce kalma da na ajje da muhimmanci, gudun samun akasi, wurin neman gyara a samu ɓaraka.
Ina fata ku fahimceni, kuma ku bi ni cikin haƙuri har zuwa inda zan ajiye alƙalamina, ban ce kada a dawo dani in na kauce ba, hukunci nake son ku ajje gefe guda, har in samu damar isar da nufina.
Idan labarina ya yi shige da rayuwarki/ka, akasi aka samu, ban gina labarina ba sai da na samu cikakken haɗin kai daga wurin wacce ta bani wannan 20% ɗin da na ambata a baya.
Nagode, a sha karatu lafiya!
Page 1
Zaune yake cikin ofishinsa, wanda a kullum yake ɓata kusan rabi da kwatan ranarsa a ciki don gina duniyarsa. Kai tsaye zai iya cewa a dukkan rayuwarsa, ya fi son aikinsa fiye da komai bayan iyayensa.
Ofishi ne k'erarre, wanda ya nemi a yi masa fenti kalar blue kasancewar shine kala mafi soyuwa a k'albinsa.
Idanunsa ke yawatawa cikin ofishin, yana kallon yanda ofishin yake a shirye, ƙamshi mai daɗi na tashi. Mamakin yanda yake jin komai ba ya masa daɗi ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba yake.
A kullum in ya samu kansa cikin irin wannan yanayi, kallon katafaren ofishin na dawo dashi asalin ɗabi'arsa, barin ma ƙamshin da a kullum in ya shaƙa yake jin cikakken nutsuwa.
Ajiyar zuciya ya sauƙe, ya lumshe idanunsa a hankali tare da waresu bayan ya jingina jikin kujerar da yake zaune.
Sanyin ACn ya ji yana ratsasa, wanda ya yi sanadiyyar mimmiƙewar gashin jikinsa.
Ba tare da ya kula ba ya ɗauki wayar salular da ke ajiye saman teburin gabansa, ya danna wata lamba sannan ya kara a kunnensa.
"Coffee!"
Kalmar da ya furta kenan ya datse wayar.Hannunsa ya haɗe wuri guda a saman teburin, ya rasa gane yanayi guda da yake ciki.
Jin sanyin yana dagula lissafinsa, yasa shi hanzarin ɗaukan makunnin ACn ya kashesa gaba ɗaya.
Idanunsa ke yawo cikin ofishin, ya kasa ajiye hankalinsa wuri guda, shi karan kansa ya rasa gane matsalarsa.
"What's wrong with you Abdulwahab? (Me ke damunka Abdulwahab?"
YOU ARE READING
DUHUN DAMINA... Maganin mai kwadayi
RandomRayuwar matasa Sharhi:- Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma ince bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙiri duk wani SUNAN da na gin...