Twelve

2.1K 237 111
                                    

Wasa-wasa maganar auren Juwairiyya da Abdulwahab ya kankama, mahaifinsa da ƙaninsa suka yi tattaki aka tsayar da magana guda.

Watanni biyu kacal aka sa, duba da cewa lokacin Juwairiyya na farkon komawa makaranta, shagalin biki ba zai shafi karatunta ba.

Bayan an sa ranan aurenta sakamakon jarabawarta ya fito, kamar yanda ta yi tsammanin ganin sakamakon hakan ya kasance ko ma ince ya ɗara tunaninta.

Wacce take samun 4 points a CGPA nata, tayi ƙasa warwas zuwa 2points, ta tabbata ba dan kasancewarta hazik'a ba, bazata samu 2 ɗin ba ma.

Bata iya sanar da mahaifiyarta ba, gudun fad'a da kuma sabon zargi.

Sai dai hakan bai yu ba, yanda mahaifiyarta take tambayanta dole ta sanar da ita, hakan ya jawo mata sabon kula da sa ido daga mahaifiyarta.

Tun ranar da ta yi mafarkin nan mai rikitarwa, ta hana kanta komawa ga aikinta, ba dan komai ba sai don tsoro da kuma fargaban abun da zata iska nan gaba.

Shawarwarin malaminta ta yi ƙok'arin bi, duk da mafi yawan lokaci tana cin karo da littafan batsa a yanar gizo, ba ƙaramin artabu take yi da kanta ba kafin ta iya wucewa, wani lokacin ma wayar take ajjewa gefe guda ta koma wurin mahaifiyarta, sai wannan tunani ya bar kanta sannan ta ɗauko wayar.

Ƙawayen da take hana kanta zama da su a da, yanzu su ne mutane na uku ko ma dai tace na biyu cikin wad'an da ke ɗauke mata kewa da kuma hanata tunanin da zai iya kaita wannan aiki.

Karatun Qur'ani da littafai masu anfani kuwa, sun zame mata abokan hira da dare har bacci ya ɗauketa.

A ɓangaren rashin lafiyarta, ta ga sauyi mai yawa, duk da gashinta bai dawo yanda yake a baya ba, amma bai ci gaba da karyewa ba kamar yanda ya fara.

Ƙurajen fuskarta tuni suka daina fitowa, ruwan da ke yawan fitowa gabanta ya ragu, wanda a da, ta kan rasa gane wani irin ruwa ne, shin na wanka ne ko kuwa na tsarki ne kawai? Kowanne da kalarsa.

Hakan sosai yake rikita mata ibadarta, ita kanta bata iya gane shin tana kan daidai ko kuwa.

Infection nata kuwa, ta gama shanye magungunanta, ta duk'ufa haik'an wurin yin "Kegel exercise", wanda a ganinta zai daidaita mata tsukewar da ta san istimna'i ya bud'e.

Sai dai hakan zai yu kuwa? Ita kanta tana tambayar kanta, amma bata saduda ba, ko ba komai Allah ma ji rok'on bayinsa ne, zai gafarta mata kuma ya inganta rayuwarta tunda ta dawo daga rakiyar shaitan da kuma zuciyarta.

A ɓangaren Abdulwahab kuwa, barin wannan aiki nasa yana matuk'ar yi masa wahala, ba dan komai ba sai don kasa gane inda matsalarsa yake.

Yanda Juwairiyya ta samu cikakken bayani da kuma yanda zata yi ta daina, shi bai samu hakan ba, hasali ma, bai tab'a kula da abunda yake sa shi fad'awa wannan aiki ba bare ya hana kansa ba, tunaninsa gaba ɗaya ya zauna a kan in ya yi aure komai zai wuce.

A yanzu da yake hada-hadar biki, baya samun lokacin kansa bare ya afka, sai dai mafi yawan lokaci in ya shiga wanka, abubuwa masu yawa na faruwa, wanda shi baya ɗaukansa a laifi babba.

Ranar Asabar, ya kama daidai da ranar da za a kai kayan auren Juwairiyya. Sati biyu ya saura zuwa bikinsu a wannan lokaci.

Dangin Abdulwahab ta wurin uwa da uba suka had'u mak'il, ko wani ɓangare na ji da kud'i da wayewa.

Binciken da mahaifiyar Abdulwahab ta yi a kan Juwairiyya da iyayenta bai sa ta karaya da ƙin auren ba, sai dai ta ji dad'in irin zab'en ɗan nata, yarinya daidai da martabarsu da ajinsu a cewarta, sai dai ta yi ƙank'anta, bata so ɗan nata ya ƙare a kanta ba.

Ƙarfe hud'un yamma suka isa gidan cikin motoci na alfarma.

Surayya da ta kasance 'yar aiken mahaifiyar Abdulwahab, bata bar abu guda ya wuce ba tare da ta gani ba dan kai rahoto.

DUHUN DAMINA... Maganin mai kwadayiOù les histoires vivent. Découvrez maintenant