Garabasa

682 17 1
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Assalamu alaikum warahmatullah!

Barka da warhaka, da fatan dukkaninku kuna lafiya? Bayan haka, ƙungiyar nan mai suna a sama, na farin cikin shaida wa ɗaukacin masoyanta, ma'abota bibiyar rubututtukan 'ya'yanta, har ma da wanda ba su ta6a bibiyar ba amma suna da ra'ayi, cewa sun samo muku hanya mafi sauƙi wacce za ku samu labaransu.

Hanya ce wacce babu batun zuwa wani group kina jajen ci gaban wani littafi, ko kuma wani shafi kin rasa shi bayan kuma kin ɗauko jin daɗin karatunsa. A wannan sabuwar hanyar tamu, baki ɗaya littafinmu za ku same shi, ku karanta ba tare da jaje ba bare har a share ku idan kun nema. Idan har kuka fara karantawa to sai dai idan wani uzuri zai tsayar da ke ki ajje karatun. Daga gare mu dai kam, cikakken littafi ne za ku samu.

Hanyar da za ku bi ita ce;

Ku je *play store,* kai tsaye wurin searching za ku rubuta *Nagarta Writers,* za ku ga manhajarmu (application) ya 6ullo, sai ku danna install, a sauƙaƙe, ba ya da wani nauyin da zai zuƙe muku data.

Bayan ya gama duka, sai ku shiga a cikinsa. Za ku ga *categories* na littattafanmu baki ɗaya. Sai ku zaɓi category ɗin da kuke son dubawa, misali kina son karatun horror, a categories ɗin za ku ga horror sai ku shiga. Za ku ga littattafai sai ku za6i wanda kuke so.

Ba a nan kaɗai abun ya tsaya ba, a kusa da categories akwai inda *Authors* yake, sai ku shiga. Za ku ga jerin members na nagarta, sai ku za6i sunan wacce kuke son karanta littafinta.

Haka kuma, akwai wurin searching daga can sama, za ku iya saka #tag na littafin ko kuma sunansa, ko sunan marubuciyar, za ku ga ya ɓullo sai kawai ku shige.

Zaku iya adana littafin a ma'adanar app din, wato saved da ke rubuce, dan saukin samun littafin da kike kan karantawa.

Wannan wata hanya ce mai sauƙin gaske, wacce muke fatan dukkanin masoyanmu na gaskiya za su ji daɗinta. Za kuma su yi alfahari da wannan ci-gaba da muka samu.

Daga yanzu ba za ku sake samun wani sabon littafinmu a whatsapp ba, sai dai wanda suka riga da suka fara ne za su ƙarasa shi a nan. Daga nan kuma sai dai a app namu insha Allah.

Mun gode sosai da soyayya.
Mun gode da bibiyar labaranmu.
Muna tare da ku a kodayaushe.

Ga link na app namu dan saukin isa ga manhajar:-

https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.nagarta

Signed by NWA OFFICIALS

Kwaiseh MaryaamahWhere stories live. Discover now