CHAPTER 8

542 42 0
                                    


✨✨✨✨✨✨✨✨
*KUDURI KO MANUFA*
✨✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

©2018

FOLLOW ME ON WATTPAD @jannahjay8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

61-62

Kausar gyara kunnuwanta tayi dan taji meyasa aminiyarta ta shiga al'amuran gidan coins, sa'adarty ta fara"kausar kamar yanda kikaji alabari mahaifiyata tabi duniya an nemeta an rasa har wasu na cewa an ganta wani kauye ta haukace,naji labari daga hajju tun ranar da wasu mutane sukazo sukayi ikirarin yan uwan Alhaji khamees ne abokin babana wai ya basu sako su bata tun daga ranar tabar gida ba'a sake jin labarintaba nikuma alokacin kinsan ina makaranta, daga baya danazo sai naji labari  abakin wani yaro dake zuwa daga kano musaddiq bazaki iya tunashiba saboda sanda ya fara zuwa dutsamma kun dawo katsina shiya fadamin bakowane Alhaji khamees ba sai coins tundaga ranar na daura kudurin sai na shiga rayuwarsu kozan gano meye lakanin da suka mata akarya sannan na dau fansa, kuma an ban labari shine sanadin mahaifina adalilin aikin dayayi  karkashinsa amma bai taba takowa gidanmu ko aikeba akan halin damuke ciki, ada na dauka mahaifina  ya rasu ahanyar aikin coins sai dai kuma daga baya naji labari bai mutuba"zaro ido kausar tayi tace "sa'adarty kina cikin hankalinki kuwa kin taba ganin an mutu an dawo? Waya fada maki wannan labarin mara tushe? "Hawaye dama tuni ya wanke idon sa'adarty sa siraran yatsunta tayi ta sharesu tace "nasan bakowane zaiji ba ya yarda amma kausar wannan maganar zan iya rantse maki bata da karya ko nakasu, saboda kawu da hajju suna maganar, Ashe  mahaifina an rufeshine a kiri kiri lagos... Tuni kukanta ya fara komawa  mai sauti itama kausar  din bata san sanda hawaye ya fara saukowa daga idontaba, rike hannun kausar sa'adarty tayi tace "kausar fadamin meye aibu na sanar min halin da yake ciki, sun manta shikadai gareni da za'a haramtaman ganinshi,  ashe duk zuwan lagos da hajju keyi shi take gani kusan tsawon shekara da yan watanni, meya masu suka rufeshi ake azabtar dashi"dukansu sheshshekar kuka suke bamai rarrashin wani suna cikin maganar sai ga ummie kanwar kausar saboda haka  suka bar maganar.

Washegari sa'adarty tafito mami ta aiketa zuwa kwado zata karbo mata sako agidan kawarta tana sanye da atampa wadda kalan maroon tafito sosae jiki da black hijab ajikinta  kanta sunkuye, jad tun daga part dinshi ya gano itace zata fita alokacin  3:30 na yamma yasan takusa tashi daga aiki saboda haka ya wuce part din mamin yayi sa'a sa'adarty ta dawo dan ta dauki wayarta da ta manta, ya kalli mamin yace dan Allah inason adafamin indomie, kallonta mami tayi tace taje ta dafa sannan ta tafi haka jadar yayi ta jan magana sai past 4 tabar gidan sannan ta tafi aiken, kafin ta dawo gida magriba yakusa

Da sa'adarty ta dawo Bushe ne ya tare ta yake tambayarta yace "naji ance  dan gidanku ya dawo hakane?  Daure fuska tayi tace please bani hanya na wuce, cikin dariyar yan iska ya ce in nakifa? Tare da lashe baki irin na rikakkun mayun mata yana fada yana kara nazarin halittun kirjinta kamar tsohon maye, yanayin kallon da Bushe ke matane yasata jin matukar tsoro dan layin yayi shiru akwai hadari sannan lokacin sallane kowa yana masallaci kaiwa hannunshi yana kokarin latsa kirjinta wani irin karfi taji yazomata ta bangajeshi ta dora da gudu shikuwa biyota yayi yana cewa "kafin bataccen yaron gidan ya kwashi romonki gara nima na kwasa" tana cikin gudun taji hannu ya janyota kara tasaki kafin daga baya taji an rufe mata baki "is okay nine"taji ance muryar jaheed  ce wata irin ajiyar zuciyace ta kwace mata tsoro da karkarwar da jikinta keyi yasata kankameshi sannan sheshshekar kukanta ya fara tashi, adaidai lokacin Bushe ya karaso kan lungun da jaheed din ya jata yana ganinsa  yayi sauri ya juya dan yasan waye jaheed tsaf zaisa adaureshi, tayi minti 5 kafin ta dan nutsu inda tabar jaheed da zazzafan assignment da warmness najikinta ya sakar mashi

Bayan ya rakota gida duka jikinta yayi sanyi magana ma dakyar take iyayi, ya kwantar mata da hankalin akan zai masu warning koma waye ba abunda take sai gyada kai,sannan yavmce wai meyasa bazata daina aiki agidan coins ba, ta fada masa reason dinta, shiru tayi, haka ya rabu da ita, dama yazo ganin abokinshine shine ya fito dan zuwa masallaci sun makara

Shikanshi bakaramin tausayinta yajiba ga damuwa dan gaskiya shi yanada tsananin kishi haka ya tafi gida cike da damuwa

Cikin gida sa'adarty tunda tashiga tana ganin hajju sai wani sabon kukan ya kwace mata ita kuwa hajju dora mata ido tayi, sai da tayi mai isarta sannan ta tambayeta "cemata tayi karene ya biyota"dariya hajju tayi tace "shine zakizo ki kama yimin kukan baci"kausar ce tashigo yanayin da taga sa'adarty yasa ta tace mata bestie dan shigo daki akwai news, sa'adarty shiga tayi dakin tana shiga Kausar tace "bestie meya faru naganki cikin damuwa haka? Jan zuciya sa'adarty tayi ta bata yanda labarin ya faru sannan ta dora da cewa "bakincikina ya karu saboda gani nake duk coins ya jamun, saboda yanzun da bana aiki gidan kinsan da wuya nakai irin lokacin nan waje da har za'ayi kokarin raba ni da mutumcina"haka suka zauna suka ta maida zance akan abun

Washegari tana zuwa gidan coins fuskarta ba walwala koda ta hango jadar bata ma nuna taga zahirinshiba balle ta aika mashi hararar da tasaba yimishi, shikanshi sai da yaji ba dadi dayaganta haka, shiyasa dayazo yin break da tazo zuba mashi kunun gyadar yace mata leave it i will do myself, bata nuna taji ba kawai ta zuba mashi, binta yayi da ido koba komai jadar yana da special tausayi ga mata balle yanda yaga idonta ya dan kumbura, idon muneera kansu har cikin ranta taji haushi tace "to meye na wani kin barinta tayi, ba aikinta bane"wani kallo ya watsawa muneera na nuna warning tuni ya hade rai ya dawo mata sak dinshi, shi arayuwarshi ya tsani shishshigi baiyi counting mutum cikin abuba yasa kanshi

Da Azahar tana zaune tana yanka fruit akitchen zata hada smoothie sai ga hajiya sakeena tace mata saura kwana hudu su tafi Abuja bata saniba ko hajju zata bari atafi da ita, shiru tayi tare da yin tunanin shin tabisu ko kuwa?

BY JANNAH JAY

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now