CHAPTER 22

530 34 1
                                    

https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-Association-272714726630585/?ref_component=mbasic_bookmark&ref_page=%2Fwap%2Fhome.php&refid=8&ref=opera_speed_dial_freefb

✨✨✨✨✨✨✨✨
*KUDURI KO MANUFA*
✨✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

©2018

FOLLOW ME ON WATTPAD@JANNAHJAY8

89-90

Ta taho da wannan rangwada duk atunaninta burgeshi take saboda ganin ya kafeta da ido, shikuwa abangarensa zunzurutun bakin ciki da takaici yake sai jin hucinta yayi kusa da shi tayi dage dan bakinta yakai ga fuskarshi da niyyan yi mashi kiss

Wasu zafafan maruka ya ajiyewa kowane side na chicks dinta har saida jini ya kawo alips dinta kara tasaki  tare da dafe gefe daya na fuskarta hawayen wahala suka fara sauka afuskarta, cikin bacin rai da kankanta ido wanda tuni sun rune sun koma ja ya nuna ta da yatsa yace " MUNEERA wace iriyar rayuwa kikeson jefa kankine? Wannan ba dabi'ar zuriyar mu bace shin an fada maki sai kin gwada karuwanci namiji zai soki? To idan ma hakane ni bana daya daga cikin irinsu fara zagayeta yayi yana magana yana nuni ga surarta yacigaba da cewa

"Baki da abunda zai kai hankalina gayin zina dake, acikin mata bansan wane class zan ajiyekiba dan haka ki kiyayi kanki, idan kina takama da iskancine kinsan naga wadanda suka fiki ko? Duka yaushe kika  fara kirgan dangine amma har kika bari sukayi lakwaf kaman bread yasha ruwa" wata iriyar kunyace ta kamata tafara rufe kirjinta da hannu wanda hakan bazai rufa mata asiri ko kadanba, batasa sanda ya matso kusa da itaba ya kama gashinta dayasha tsadadden wool ya ja dakarfi ya mikar da ita dashi kara tayi hade da zubowar wasu hawayen afuskarta yacigaba da cewa " MUNEERA  wallahi ina tausaya rayuwarki, amatsayinki na mace da bata dara shekara 20 ba har kinsan kikai jikinki ga namiji baki tsoron raping? Ko ance maki ni bani da lapiya? Karki sake irin wannan gangancin, kin jini? Da karfi wannan karon yamata tambayar cikin karkarwa ta amsa sannan yayi wurgi da ita kaman kayan wanki ta buge bakinta da wani wooden table dake gefen couch din dake can gefen bed dinshi aikuwa tuni goshinta ya tashi

Cewa yayi ta fice adakin yana da uzuri, kuma ta tabbatar bayan sallan eisha yasameta aparlournshi yanason magana da ita, sumi sumi ta tashi ta fita jan tsaki yayi yace "stupid" kishingida yayi gefen gadonshi tare da tallabar goshinshi yana iya tuna sanda SA'ADARTY ta nuna bacin ranta kan taba ta da yayi ranar da ta suma amma ga wata na muradin ya tabata wannan lalacewa har ina, sai da ya sami kimanin minti biyar yana tunanin SA'ADARTY sannan ya tashi akasalance ya wuce bathroom ya zaro sabon towel na kamfanin gucci yayi shirin wanka

*KATSINA*

SA'ADARTY  ke waya da JAHEED  cikinso da kauna yana fada mata zai shigo KT week end mai zuwa tunda  tace takusa yin hutu kuma tana tunanin ABUJA zata wajan MAMI baison ta tafi basu haduba, daga gefenta MERMA ce kema TEEMAH tsifan kai sai rigiman su na kawaye suke akan ita TEEMAH na cewa MERMA na mata da mugunta can kuma suka maida hankalinsu kan SA'ADARTY da takara lafewa cikin katifa cike da jin dadin kalaman JAHEED  din, sai TEEMAH tacewa MERMA " kin lura da wani abu kuwa SA'ADARTY na masifan son JAHEED wanda hakan ina ganin zai iya kawo mana cikas cikin plan din nan" cikin gamsuwa MERMA tace " kwarai kuwa muddin son JAHEED zaiyi karfi azuciyarta zaiyi wuya ta bada hadin kai sosai awannan plan din" SA'ADARTY da ta raba hankalinta biyu tana dan tsintar maganarsu yasa tayi excuse daga wayar JAHEED tace zata mashi magana, kallonsu tayi tace

" Tabbas inason JAHEED amma hakan bazai sa na gagara bin plan din nan ba matukar zan kwatarwa mahaifina yanci, karku manta har yanzu bamu gano manufar HAJIYA SAKEENA kainaba wanda sanin kankune daga labarin da na baku kun gano akwai lauje acikin nadi game da jana ajiki da takeyi"

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now