CHAPTER 25

495 32 0
                                    

https://mobile.Facebook.com/eloquence-writers-Association-272714726630585/?ref_component=mbasic_bookmark&ref_page=XMenuController&ref=opera_speed_dial

✨✨✨✨✨✨✨✨
*KUDURI KO MANUFA*
✨✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

© 2018

FOLLOW ME ON WATTPAD@JANNAHJAY8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

95-96

Washegari da wani kwarin jiki JAD ya tashi yayi wanka tsaf cikin kafatan na wani men material navy blue bakaramin kyau suka mashi ba,  ya kafa hula tare da daura wristwatch na gucci platinium golden ya fesa turarika banda kala uku dayasa ajiki yafesa sauvage tare da wani arab mai masifan kamshi takalman kafarshima abun kallone na robert cavalli

Yana shigowa yin breakfast ya tadda MAMI taci uban dauri na wani tsadadden lace tana  sipping tea, dagowa tayi tace " *Tabarakallah  ahsanul kalikin* son yau kodai gun surikata zakaje ne?

Dan shafa goshinshi yayi yace "MAMI kaman kinsan tuni zuciyata ta samo maki surika" gabantane ya fadi amma bazaka iya ganewa ba wani gajeran murmushi tayi da ya tsaya iyakan lips dinta tace " Allah yasa tagari ce, kuma wadda zataso mu tare da danginka" zama yayi tare da daukan grape ya jefa abaki saida ya cinyeshi  sannan yace "Ai MAMI yarinyar nan nasan dakinsanta zakiji farin ciki da annashuwa kuma zaki tayani murna" zuciyarta lokaci daya ta kawo mata MUNEERA yake nufi take taji wani fargaba hade da faduwar gaba ya kamata amma sai tayi shiru

SA'ADARTY tazo ta zauna gefensu bayan yace "MAMI sannu da hutawa" dake already sun gaisa da safe, kallonta JAD yayi yana yaba baiwar da Allah ya mata azuciyarshi, tare da jinjina irin yanda Allah yasa take da tasiri arayuwarshi, zuwanta kadai har ji yayi kaman kamshi hade da iskan dakin ya canza mishi Zuwa wata ni'ima mara fassaruwa

Sake ware idonshi yayi yake kara kalleta, sanye  take da gown na navy blue material da aka mashi  flowers da turquise blue colour, veil din da ta dora kanta t-blue din ne  da fashion din dankunne da ya kasance mai fadi, gaskiya tayi kyau duk da bawani kwalliya tayi sosaiba in ka dauke oil control da tashafa sai  lip gloss

SA'ADARTY ta takura da kallon da JAD  yake mata, sai dai itama  jefi2 tana kallon side dayake, bata taba ganin yayi mata kyau irin na yauba har wani kwarjini ya kara a idonta,  amma ta alakanta hakan da shiga full na hausawa da yayi, gefe daya zuciyarta na lugude saboda fargabar da takeji yau JAHEED zai zo, hakanan take jin nauyin sanar da MAMI akan zatayi bako

Bayan sungama ta tashi asanyaye takoma daki ta daga wayanta ta kira KAUSAR da MERMA cfrnc call take tambayar  shawara kan zuwan JAHEED

MERMA tace "gaskiya aganina karki hadu dashi cikin  gida, if possible ku hadu waje kaman cin fuskane wajan JAD" jan tsaki SA'ADARTY tayi tace " friend ana maganar serious nefa, kinsan JAD ba sona yakeba so ki tsaya agama magana nan kafin ki sako wasa" dariya MERMA tayi tace "nima ba wasa nakeba, im telling you akwai ranar da zakizo ki fadamin JAD  ya furta maki kalmar nan" kausar cewa  tayi " aganina nuku nuku ba naki bane kawai ki gaya mata, tunda kinsan baki da daman fita yanzu balle ki hadu dashi wani wajan" TEEMAH da tunda aka fara maganar tayi shiru tace" amma MERMA idan maganarki munason muga gaskiyarta sai ta hadu dashi gidan inda anan ne zata gano zai nuna kishi matukar yana sonta" MERMA  tace "gaskiyane kuma fa" sun dade suna tattaunawa daga nan suka kashe lokacin ma azahar har tayi

Tana idar da sallah ta nufi dakin MAMI inda ta sameta tana waya da HAWWA sai da tayi satar ji, MAMI na cewa HAWWA har yau ban fada mata manufata ba amma kuma shi JAD din naji ya zomin da maganar ya sami wadda yakeso, kinga kenan yanzu ne lokacin da yakamata na fada mata saboda kar garin kallon ruwa kwado yamin kafa, daga can dai tana jiyo maganar HAWWA amma bata gane me take cewa sallama da tayi ne yasa MAMI kashe wayar bayan ta cema HAWWA zata kirata anjima

MAMI jiyowa tayi ta kalleta  bayan ta amsa sannu da ta mata tace"  tace mata  naga alama da magana abakinki" cikin sunkuyar dakai da jin kunya tace " dama.. Dama" murmushin manyance MAMI tayi tace "haba SA'ADARTY har yanzu baki daukeni  matsayin mahaifiyaba da bazaki iya fadamin matsalarkiba?  Shiru SA'ADARTY tayi kafin ta samu courage din cewa "dama yau akwai wani dayace zaizo mugaisa" wani irin duka zuciyar HAJIYA SAKEENA tayi tace "Ayya kice kunyace ta saki kasa magana, dan katsina ne?  Sunkuyar dakai tayi tace "Eh dan can ne" dan yake HAJIYA SAKEENA tayi  tace "shikenan Allah ya kaimu idan yazo kisa ashirya masa komi anan kitchen karki  ji kunyar komi" godiya SA'ADARTY tayi  ta juya tafita kasan zuciyarya wayar da taji hade da canjin fuskar HAJIYA SAKEENA din yana daure mata kai duk da ta fuskanci MAMI taso ta boye amma dake  ta karanceta adan zaman da sukayi sai da tagane

Duk da yanzu ba matsayin yar aiki takeba amma most of time takan hada masu abinci mai dadi MAMI da COINS AFFA, shiga tayi kitchen ta hada snacks kala biyu dan daidai ta ware wanda zata kaima JAHEED ta ajiye masu sauran sannan ta hada drink guda daya  sai pepper meat na beef dayasha tumatir da albasa ta ajiyesu gefe tana dan gyara inda ta bata sai ga JADAR ya shigo kai tsaye ya wuce kusada inda ta ajiye kayan JAHEED  ya bude glass bowl na meat din ya bude zai sa hannu tasa kasan serve spoon ta buge hannun tace "wayace wannan da kai aciki" dariyanshi ta rainin wayo yayi yace gashinan kin wareshi daban that means wancan nasu AFFA wannan nawa right? Ya karasa da sigar tambaya dauke tray din  dasuke kai tayi ta fita dashi daga kitchen din, binta da kallo yayi yaga kaman yau bata cikin mood din tsokana

*DA YAMMA*

JAHEED yazo sai da ta gyara kwalliyanta wadda dama da zatayi girki saida ta ciresu, ta shafa lipstick dark purple ya masifan fita akan fuskarta kaman dama haka lips din suke ta zizara eyeliner saman idonta ta kara fesa perfumes  masu  taushin  kamshi  yanda  bazasu  baza kamshinsu sosai ba, kasancewar addini ya haramtawa mata hakan

Ta tafi cikin taku na nutsuwa daga inda yayi parking yana hangota yana godewa ubangiji daya hadashi da SA'ADARTY can gefe ashe JAD yana daga wajan BQ na gidan kan plastic chair yana hango tafiyarta da inda direction nata ya nufa ga sabuwan motar dayasan bana gidansu bane, wani irin radadi yakeji azuciyarshi duk da baida Tabbas kan namiji ke ciki, amma yana zargin hakan

Wani irin ciwone ta soki zuciyar JAD sanda yaga fitowar JAHEED daga motar da irin blushing da SA'ADARTY keyi, ga wani romeo type look da JAHEED kema SA'ADARTY, ba shakka wannan shine wanda take fada masa, tsabar wulakanci agidansu za'azo amasu zance, baisan meyasaba yaji wani mahaukacin kishi ya taso masa ga wani irin bacin rai daya danne masa kirji, tuni idansa suka juye zuwa na kishi  har wani ja suke suna  shekin bacin rai

Bai ankara ba yaga anshige da JAHEED parlourn bakin MAMI, yana tsaye still inda yake  zaune jikinshi  na karkarwa ya rasa ya zaiyi, yaga wucewan SA'ADARTY ta dauko tray mai dauke da abubuwa ta wuce can sai wajan 6 yaga fitowarshi ta mashi rakiya bakin motarshi

JAHEED na jingine jikin mota ya kalleta yace "SA'ADARTY im missing you pls come back to kt" dan hararan wasa ta mashi  tace " ai kaima haka kake zuwa nan ka baroni kt, so i think this is good time da zan rama" murmushi yayi yace " naso ace sanda ina aikin nan kikazo da hakan zaifimin dadi look at you sai wani fresh kike like you dont miss me" ganin JADAR sukayi kawai gabansu kaman wani kububuwa yacewa SA'ADARTY "har yanzu bai ishekuba duk da dadewan da kukayi, wuce cikin gida"

Reaction dinshi ya bata mamaki, shima JAHEED haka amma sai ya mikawa JADAR hannu adan dakile ya mika masa suka gaisa JAHEED yace "babban yaya ayi hakuri kasan masoya idan suka dade basu haduba sai anmana uzuri" JAHEED dayasan maganganunsa kara ruwan dalmane aciwon JAD da baiyisuba ya dago ido ya kalleshi  yace "kodai rashin kunya" dariya abun ya bawa JAHEED saboda yaga JAD din bai wuce tsaran shiba yace "hakane ayi hakuri" ya juya ya shiga motarshi sai asannan SA'ADARTY da ta labe bayan flowers ta karasa cikin gida cike da mamaki action din JAD kansu

HAJIYA SAKEENA da ta dage curtain na  dakinta tsaf komai ya wakana a idonta, wata irin ajiyar zuciya ta ajiye bayan taji hayaniyar da JAD yayi

BY JANNAH JAY

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now