CHAPTER 58

515 32 3
                                    

https://mobile.facebook.com/Eloquence-Writers-266267857577087/?ref=opera_speed_dial&_rd

✨✨✨✨✨✨✨
KUDURI KO MANUFA
✨✨✨✨✨✨✨

BY JANNAH JAY

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

© 2018

Follow me on wattpad@ jannahjay8

*DEDICATED TO MY VERY OWN SIS MERMA*

161-162

Zaman SA'ADATY da JADAR haka yacigaba da gudana cikin gwadawa juna tsantsar soyayya, ayanzu haka JADAR ji yake bayashi asa'ar mace, gashi kusan kowanne lokaci SA'ADATY tana gwadamasa iya soyayya da kulawa sai yazamanto sonta ya kara yimasa kaka gida azuciyarsa, haryana ji tagama masa komi, shi yanzu gani yakeyi komeye zaizo ya tare masa alaka da ita zai tsaya tsayindaka har sai inda karfinsa yakare

Yanzu haka yana zaune cikin restaurant abirnin NEW YORK  tana opposite dinshi, kuramata ido yayi ya kasa dauke idonsa kanta yau gaba daya, saboda wani salon love da SA'ADATY ta mashi adaren abun ya kasa kankaruwa aransa, ganin kallon yayi yawane yasa ta waro ido tace " everlasting meye faru? Ko yau namaka munine? Ta karashe tare da narke ido cikin sigar shagwaba, yace " yau da kinsan matsayin danake kallonki da kin kyaleni nacigaba da kallonki har sai sanda idona yatafi hutu" murmushi tayi tace " saboda me?" bata jira amsarshiba tadauko kiwi afolk ta miko mashi bai ce komiba ya bude bakinshi tasaka mashi,kallon idon juna sukayi na seconds ita kadai tasan me ta hango a idon JADAR, lokuta da dama idan tahango tsantsar sonta da kaunarta a idonsa takanji tausayin sa da kuma ji kamar bata kyauta masaba, take jikinta yayi sanyi bata iya karasa plate dintaba, shikuwa daman ranar sam ba kalar abincinda ke burgeshi yau sai ma kwadaituwa da ita da yayi

Koda suka shiga mota kasa biye zolayarshi tayi, dayaga haka sai ya kyaleta, jingina tayi jikin kofa ta fada tunani wanda rabi kan rayuwartane, da kuma shirinta na gaba saboda mahaifinta, koda dare yayi bayan tasa night wears dinta dukunkunewa tayi cikin blanket,ta rasa inda zatasa ranta kawai taji ta ba daidaiba so take kawai wannan rayuwar da tasa kanta ta kare, yaushe zatace kullum kara sakewa take da halittar da zata bari karfa nan gaba  zuciyarta tamata taurin kai wajan karashe abunda ta fara, kawai sai ta fara hawaye sharrr still tana kwance cikin bargon....

JADAR dayake amsa wayar AFFA yanayi rabin hankalinshi nakanta, baison koya yaganta wani iri yanzun zai fara bata hakuri karyaje ko tana fushine,yana gamawa da wayar yaje ya budeta wanda tuni tayi sauri ta goge guntun kwallar idonta, ya kalleta yace " cutie pie what happen? " ya janyo ta jikinshi kamar wata yarinya ya dorata kan cinya likus tayi jikinshi, ta rufe fuskarta akirjinshi saboda kar yaga yanayin da idonta yake ciki, cikin dasasshiyar murya tace " ban jin dadine" abun yadan bashi mamaki saboda lokaci dayane ta koma hakan, amman saiya ce " subhanallah meya ke damunki? kai?  Zazzabi? " jijjiga kai tayi, yace " ai tambaya biyune ko duka gaba dayanne? "   shafa wuyanta yayi yaji da dan dumi tace mashi " bawani sosaiba kawai dai najini wani irine i think in nayi bacci i will feel much better" tuni ya zaro wayarshi yana searching private  doctor, kamo hannunshi tayi yace " ki bari nasa azo adubaki banganewa bayan bacci ba, sam banason wani abun yasameki" kwace wayar tayi tace " Ka bari ko zuwa darene in banji saukiba sai yazo amman yanzu kam bacci nakeji" ta kara shigewa jikinshi, nan sukayi ta jan magana dole ya hakura aikuwa baccin tayi sosai sai da yaga lokacin Azahar zai wuce ya tadata

"Wai MERMA ni yaushene zaku koma school? " dariya MERMA tayi tace " lallai SA'ADATY hala kin cire kanki a students ne zamu zakice, lallai JAD yana gigitamaki kwanya" itama yar dariyar tayi tace " A'a fa bawai ina nufin banda ni bane kinsan dai kt school batamin dadi idan baku, dazun muka gama magana da HERCULES (JADAR)   kan school wai dole bazan sake zama ahostel ba nikuma nace mashi nafi son can tunda shima bawai lokaci zaike samuba koyaushe koba haka ba? " MERMA tace " to meye in kinbar hostel ai ba prob ai yana kiyaye maki hayaniyane, koni da MAMA zata bari ai barinshi zanyo saboda gulamce gulmace" sun dade suna dan hirarsu tace sai dai sun dawo NAIJA zasu sake magana kan wajan zamansu

Sai da su SA'ADATY suka yawata kasashe 5 sannan sukayi haramar dawowa NAIJA,  yanzu suna LEBNON dan SA'ADATY tagaisa da zuriyarsa ta bangaren uwa, aikuwa SA'ADATY taga kauna wajan JADDATIE sai takara sakankancewa dole aga JADAR da halin kirki, in ya juye yana zabga larabci sai tayi ta mamaki, amma daga baya sai taga ai wajansu yayi wayo duk cimarsu ya iya, an yawata da ita cikin BEIRUT da sauran manyan alkaryoyi na kasar LEBNON, bakaramin dadin zamanda tayi acanba, sunsha tsaraba kala kala, kullum in tana waya da UMMI sai tayi ta bata labarin zuriyar JADAR, suna hira da ita sosai saboda sun iya turanci ba laifi, har dan koya mata girkin da JADAR yafici nasu akayi tare da yan kalmomin larabci

SUN DAWO NAIJA

Suna dawowa  suka wuce gidansu JADAR, anan zasu kwana adakin JADAR, da dare bayan sun dan huta MAMI ta tasa SA'ADATY da yan tambayoyi duk dadi ya kasheta, hak'arta fa fara cimma ruwa SA'ADATY har mamakin MAMI take wannan wane irin son kudine, stores uku gareta banda yan uwanta da COINS yasu sila ta arziki don wasu yanzu haka suna cin gashin kansune bayan ya basu jari bakadan ba

Sai washegari suka koma gidansu, already su BABA SALAMATU sun gyara shi, da dare suka je gaida UNCLE SALEES bakarami basarwa MOMY tasoyiwa SA'ADATY sai da UNCLE din ya dan mata alama, anan suka basu tsaraba,  tun bayan auran SA'ADATY da JADAR basu taba haduwa da MUNEERA  ba sai yau, koda MUNEERA taga SA'ADATY sai da gabanta ya fadi don bakaramin bazata zuwan nasu yamataba gashi SA'ADATY takara wani kyau nadaban, itama SA'ADATY kallon MUNEERA take sai taji dan tausayinta don MUNEERA abar tausayice awajanta tunda tarasa tarbiyya kuma taga yau ba kallon banza is like tayi sanyi don har tambayar SA'ADATY tayi " yaushe zasu koma school kuma level nawa zata shiga? " har JADAR saida yayi mamaki sai yadan wa MUNEERA murmushi, sun basu tsaraba rabi na MUNEERA sai na MUKHTAR dake ta dawo shima last week

Suna zaune agaban mirror yana shafa mata mai cikin gashinta, inyasa kibiya (musulla) cikin gashinta yana yankkawa sai take wani shihsitun iya shege wai yana cakama scalp dinta, shikuma ya takarkare yana sorry  yana yi ahankali, sai da tamashi hakan akaro na hudu ya lura ashe har dariya take, don da duka bai gane tsokana bane, ajiye kibiyra yayi yakama gashin kaman zai mata parking ya ja aikuwa tuni tasaki ihun shagwaba tana " zafi2 kaji yanda nake ji kuwa? " yace " kyaji dashi don nikam na gama  ashe tun dazun wahalar dani kike" haka dai yakarasa mata oiling suna wasanninsu kafin nan ta mike ta kalli kan a mirror ta gyara sakun ribborn din taga oil ya bata mata forehaed dinta,  daddage tayi ta goga goshin nata kan habarshi tare da kwalwalawa da gudu ta mirror yaga aikin da tamashi ya bita shima da dan gudu afalo suka dinga watsarda  pillows yana binta tana zillewa..

Suna tsaka da wasannin ne ringing din wayarta ya tsaidasu yaje ya dauko UMMI ce, barinshi tayi falo ta shiga bedromm dinta yin wayar, bayan sun gaisa da UMMI ne take gaya mata jibi zasuje gaida mahaifinta, taji muryar UMMI adan raunane, sun dade suna jajantawa kansu cin zalin da aka mashi,  anan ne SA'ADATY tace yakamata wannan karon abatashi awaya idan har sunje, bayan tagama magana da UMMI HAJJU takarba itama sukayi wayar, tana gamawa tamasu transfer na 100k a account na HAJJU saboda uzurin ziyarar

Share kwalla tayi sannan ta kirkiro murmushi takoma falo tana zuwa direct wucewa tayi kitchen ta debo popcorn a bowl yana zaune sai ji yayi abun na bin rigarshi azabure ya mike, take ta kyalkyale da dariya cutiehhh.... Ya kirata  tare da binta aguje ta koma bedroom zubewa sukayi kan gado inda wasa yakoma romance.....

#TEAM KKM
#TEAM SAJAD

JANNAH JAY..... ❤

KUDURI KO MANUFAWhere stories live. Discover now