CHAPTER 2

1.4K 71 2
                                    

Cikin dabara y matsa kusa d haydar dake tsaye daf dasu Arfan,magana yake tamkar me rad'a ,da fari takaicine y lullube haydar din amma jin kalaman d ke shiga dodon kunnuwansa yasa shi tattara hankalinsa gare shi,duba y kai ga kafafunnata yagansu sunkuf cikin takalmi,ga zulmeman hijab jikinta,ace yarinya k''ank'anuwa t makashi a yanayin zafin d ake ciki.sim sim sim abokan suka dunga zarar jiki d'aya bayan daya suna warewa.ganin haka yasa kirjin haydar sake bugawa, ganin Arfan y  maida hankalinshi kaicokam ga matashiyr budurwar.

Jiki sanyaye y matsa kusa d Arfan din t yanda yarinyar b zataji furucin nasa ba,yace "babaaaa kalli kafarta da kofato fa".cikin firgici ya kai dubansa ga k'afafunnata ,saboda tsabar tsorata idanunsa k'ofaton suka nuna masa,kan ya yi wani yunk'uri tuni haydar ya arta ana kare ,hakan ya sanya Arfan zare hannunshi daga rik'on d budurwar ta mishi y rufa musu baya,ganin haka itama ta rufa mai baya ,majalisar su y dosa inda suke zaune tunda fari inda abokansa ke zaune.ganin Arfan y nufosu a sukwane yarinyar biye dashi tana kiran sunan data lak'aba mashi na yaya suhail, dan Allah ka tsaya yayana,karka gujeni please kowa guduna yake yi ,ganin haka yasa sauran abokan dake majalisar kowa y nemi hanyar tsira,hakan besa budurwar tsayawa b ,haka ta cigaba d rufa musu baya.suna gudu tamkar sunga aljani.sunyi gudu  mai yawan gaske sannan taji k'afafunta sun sare ,nan t zube t cigaba d kuka,a bangaren su arfan kuwa dayake gidajen iyayennasu basu d nisa d majalisar tasu basu tsaya ko ina b se gida,aguje y shiga palo tare da duban hanya,saura kiris ya bangaje mommansa wadda t futo daga kitchen rike da tray a hannunta

Komawa yayi y tura kofar palon dan kuwa gani yake tamkar tana biye dashi.cikin mamakin yanayin ganin dannata a zabure yasa ta ta tanbayeshi, Arfan dina lafiya haka? Yace mom Alhmdlh Allah ne yau y tseratar dani daga sharrin aljana,wacce irin aljanna kuma? Nan y kwashe labarin tsaf tundaga hangota da yayi har izuwa taimakon d ya bata zuwa gudun d suka tik'a.Adduo'i mom ta shiga yi n  farinciki ketare sharrin aljanar da yayi,tare d adduoin  Allah y cigba da kare mata xuriah daga sharrin mutum ko aljan.duk yanda akai mugun  gamo sukai tace a xuciyarta.tun shigar Arfan gida be k'ara sha'awarar lek'owa koda bakin gate balle yayi gigin zuwa wani guri.gani yake daya futa ze kara cin karo da ita.

A bangaren Aleesha kuwa se data k'araci kukan ta me isarta sannan ta mik'e tare da bin hanyar da zata sadata da kasuwa .duhu y fara rufowa lokacin.cikin sauri t sayi aiken da aka mata , ta nufi hanyar gida.tana zuwa me gadi yace me sunan yan gayu kekuwa ina kika shiga tun dazu hajiya take aiken kina ina? Nace mata tun futarki banga dawowarki ba,ganin idanunta sunyi jajawur y shiga tanbayarta ko lafiya? Cikin shassheka ta shiga yin magana ba yayana suhail nagani ba ,shine y gudu y barni.cikin mamaki yace me sunan yan gayu banasan k'arya ina zakiga wani yayanki keda akace ba yar k'asar nan bace

Zare manyan idanuwanta tayi tare da isa kusa da baba me gadi.baba waye ya gaya ma ni ba yar kasarnan bace?dama ba hajiya bace mamana,Alhaji dadyna? Eyi baba dan Allah ka gayamin kowaye naje n sameshi n tanbayeshi ? Kode wasa kake min.wata irin tsawa d sukaji an daka daga bangaren cikin gidan yasa Aleesha zabura da nufar gun matar,cikin masifa take magana ,saboda kin renani Aleesha shine zan aikeki ki sayan lettuce a kasuwa shine zaki shafe tsawan awanni baki dawo ba,kunnuwanta t kama tare d murdewa,zugin d Aleesha taji yasata k'walla wata uwar kara data firgita Alhaji dake saman bene.

Cikin d'aga murya yace haba hajiya dan meyasa zaki daketa,yarinya yar k'ank'anuwa da batasan ciwan kan taba balle na wani,ai wannan zalunci ne,in d'iyar cikin ki ce ai ba zaki mata wannan mugun dukan ba.cikin mamaki hajiya ta juyo tana kallon Alhj ,kasa magana tayi saboda mamakin lafuzan dake futa daga bakin shi,tun aurensu basu taba samin sabanin d ze sashi daga mata murya balle ta kai ga bakar magana,amma yau akan yarinyar data dakko ta rike dan Allah shine yake jifanta da mugwayen kalamai.batare d furta komai ba ta juya ta nufi cikin gida ko ta kan salad din bata biba.

Ganin haka jikin Alhaji yayi sanyi ,hkn be hanashi k'arasowa ga Aleesha dake zaune tana share hawaye,hannuwanta y riko d nunin ta mike tsaye,shafa kanta y shiga yi tare d cewa Aleeshata meyasa kika dade data aike ki,kuka take tayi ta kasa furta komai kasancewarta irin shagwababbun yarannan d basa so a tab'a musu jiki.nan y shiga lallashinta har se datai dariya sannan ya rike hannuwanta suka nufi cikin gida,dukkan abun y faru a kan idan me gadi.

Suna shiga palo y zaunar d ita a 2 seater tare d kunna mata TV.ji yayi ta ce dadyna wai ba kai ne ka haifeni ba,cikin tsoro y kalleta tare d tanbayarta waye y gaya miki? Tace dazu naji mom n fada.murmushi yayi yace rantane ya baci,amma mune muka haifeki cikin farinciki ta cigaba da kallo ,shi kuma y nufi dakin hajiya.

YAR TSUNTUWAWhere stories live. Discover now