CHAPTER 3

1.9K 95 10
                                    

: *UNQUE WRITERS ASSOCIATION*


*YAR TSUNTUWA*

*WRITEN BY*
*AYUSH ILIASU*

*DEDICATED TO*
*FATIMA TAMBARI*
*ZEEBELLS*
*SHAMSIYYA SALIS*


*WATPAD @ AyushaIliasu*


0⃣3⃣

Daki ya iske meenal kwance a gado tayi rigingine,tunani ta shiga yi tun farkon haduwarta da Aleesha a trade fair ,yarinyar ta taho aguje t rungumeta tana kiranta da Auntyna,take yarinyar t shiga ranta,sauran yaran da suke tare d ita suna kallo suka garzaya aguje suka nufi gurin momy,momy itace matar dake tsaransu a gidan marayun dake garin na Abuja.

Cikin fushi ta nufo gurin da ta hangi Aleesha rik'e d hannu wata mata wadda da gani matan masu fad'a aji ce,Aleesha ta shagala gurin yiwa hajiya meenal surutu,kasancewarta yarinya me tsananin magana wato fadi ba'a tanbayeki ba.azuciye momy t k'arasa garesu tare da shararawa Aleesha marin dayasa t ganin stars.cikin fushi ta fara magana "saboda kunnan k'ashi gareki shine zan gargade ku da kada ku matsa daga inda n barku shine zaki matsa.tare d murde kunnuwa Aleesha, take aleeshan t k'walla k'arar data jawo hankalin mutane d dama,haka momy tai ta ja mata kunne ,aleeshan n biye da ita har suka isa inda t umarcesu d zaman tare da sakar mata rankwashi a tsakiyar kai.hjya meenal n biye dasu har zuwa gurin.ganin kukan d Aleesha keyi ya kara karya mata zuciya.sallama tayiwa matar da taji yaran n kira da suna momy,a zuciye ta amsa waalaikissalm.inba damuwa inasan magana da ke? Hajiya kiyi hak'uri bazan samu lokacin saurararki b ,dan lokaci y k'ure mana,nan ta umarci yaran da su biyota dan komawa gida.Hajiya de batai zuciya ba ta kuma bin momy amma sam momy taki saurararta,ganin haka ta dubi wata matashiyar budurwa cikin yaran ta tanbayeta adress din gidannasu tsoro fal zuciyar yarinyar gudin kada momy ta juyo t ganta tana wa matar magana,cikin rad'a t sanar wada hajiyar cewa gidan marayun garin suke d zama.

Haka suka mika suna tafiya tun hajiya n hangensu har suka fuce daga harabar trade fair din,tunanin kyakkyawar yarinya n makale d zuciyar hajiya ,tarbiyyarta da yanayin da take magana cikin ladabi shi y kara fizgar hajiya zuwa g san kasancewa da yarinya.

Hajiya daren ranar batai cikakken bacci ba,kasancewar ta mutum me matukar san yara musammn yaya mata ,duk yawan yaran b wacce ta tsaya mata arai se Aleesha,dankuwa sunkai kimanin 50dukkansu,sa annin Aleesha kuma su kusan goma ne.da sassafe t tashi,mamaki fal zuciyar Alhj kasancewar yana rigata tashi akullum.cikin k'ank'anin lokaci harta hattama Abincinta n safe,ga tarin farinciki a fuskarta da ka kalli bakinta zakasan da kwai abunda take shirin bayyanawa .haka dai Alhji yayi shirinsa n futa office tare d isa kan dinning danyin breakfast.bisa ga aladarsa duk sailin da y gama shiri xe futa topah kowace maganace baa gaya mishi se de abari in ya dawo hka dokar shi take,koda kuwa abun bukata ne n gida.amma ganin matar tashi cikin yanayin farin ciki yasa shi tanbayarta wifey ,mine sirrin ne naganki cikin annashuwa yau? matsowa t k'arayi kusa dashi dan gabanta faduwa yake,bata san irin karbar d zewa maganar tata b.yan yatsanta ta shiga murzawa tamkar wata k'aramar yarinya,ganin de so take t b'ata mai lokaci y mik'e yace tunda maganar b xata fadu yanxu b innadawo anjima mayita.

Hanyar waje ya bi tare d yi mata sallama hannunshi rike da briefcase,driver y daukeshi suka nufi office,tun futar Alhaji hajiya bata samu sukuni ba,burinta kawai taganta d little Aleena cikin gidan suna tafiyar d rayuwa me tsafta.

Waya t d'auka t kira Aminiyarta ummakulsum,cikin farinciki d yiwa juna kirarin d suka saba suka gaisa,hade d zolayar juna,bayan sun nutsu ,hajiya meenal tace Aminiyas shawara n kira miyi.to Allah yasa t karuwa ce,dariya hjy meenal tayi sannin halin kawartata dan kuwa bata d mgn illa t kudi.hmmm jiya naje tradefair se naga wata yarinya,yarinyar ta bani tausayi ashe irin yarannan ne dake zaune gidan marayu,yarinya t shiga raina shine nikeso mu daukota nida Alhaji mu rike fisabilillah tamkar diyar cikinmu.Allah sarki kawata ,Amma naji dadi hakan yanada kyau,in banda abunki d kinmin mgna ai dana baki guda cikin yarana,dariyar yak'e meenal tayi tare d cewa ba komai qawas ina godiya d wannan karamci ,qawas gwara ki karbi tawa yar ki rike ko banxa kinsan asalinta,amma waccan baki sani ba yar shege ce ko iyayenta mayu ne,mamakin kalaman dake futowa daga bakin qawar tata tayi ,amma sede t share ,tare d cewa to qawas Allah y bar zumunci.inshaa Allah anjima zan gayawa Alhj se muje mu gani ko zasu bamu ita.

A take sukai sallama,ran hjy ummakulsum ne yayi matukar baci,wato shine hajiya meenal ta share batun diyarta datace zata bata,ta gwammace t dauko bare ta rike,saboda tsabar mugun abu.wata kwafa tayi tare da mugun kuduri cikin xuciyarta.maganganu sama sama t fara,inda harta jawo hankalin kanwarta sadiya dake tsakar gida,lafiya Aunty ummakulsum naji kina magana ke kadai,inafa ni kadai Meenal ce ta kunnani ,Aunty me tayi miki? Keda meenal ai baa jin kanku,wani murmushi n yake tayi tare d cewa hkane fa ,nan suka bar maganar.

*Ayush Ilias musa*

Vous avez atteint le dernier des chapitres publiés.

⏰ Dernière mise à jour : Aug 24, 2018 ⏰

Ajoutez cette histoire à votre Bibliothèque pour être informé des nouveaux chapitres !

YAR TSUNTUWAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant