🏵*FATEN DANKALIN TURAWA DA WAKE*🏵
🏵🏵Abubuwan bukata🏵🏵
*dankalin turawa
*wake
*kifi
*manja
*attarugu
*albasa
*alayyahu
*garlic
*ginger
*kayan dandano🏵🏵*Yadda ake hadawa*🏵🏵
1:ki gyara wakenki da kyau ki dora akan wuta ki yayyanka albasa akai sabida tayi saurin nuna kuma tayi haske.
2:ki wanke dankalin turawanki ki fereta ki yankata in cube shape.
3:idan waken naki ya dahu amma ba luguf ba sai ki tsane ta a colender.
3:ki soya jajjagaggen attarugunki da manja kidansa garlic kadan d gurzaggen ginger kadan sabida kamshi d dandano mai dadii,sai ki tsaida ruwan jollof dinki.
4:kisa spices dinki duka wadanda kike amfani dasu,kamar curry,maggi,onga,rayco ya danganta da kalan spices din da kike using.
5:idan ya tafasa ki fara saka waken naki sannan kidan barshi na wasu mintoci sannan kisa dankalinki ki gaurayasu sannan kisa kifinki ki rufe.
6:bayan wasu mintoci idan komai ya nuna ya hade jikinshi ki rage wutan kasa sannan kisa yankakken alayyahunki da albasa wadatacce ki rufe na tsawon minti biyar sai ki sauke.
Enjoy it
Urs xeeydeey9 😘😘
