♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗'''written by.....'''
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*_When Someone Walks Out Of Your Life, Let Them. They Are Just Making More Room For Someone Better To Walk In!_
*PAGE.....95...100*
_QUARTER FINAL_Ma'aruf ne ya shugo ya ganta a kasa, ya girgizata yaga alamar kamar bata nunfashi.
Da Sauri ya dauketa sai asibiti, Akai mata temakon gaggawa sannan daga bisani ta farfado, Ma'aruf ne ya sanar dasu mumy, Sannan yaje gidan iyayan Aminatu ya dakko Su ya Sanar dasu besan meke faruwa baNan dai kowa yai jigun jigun iyayan Aminatu sunsan Komai, bude idonta tai ahankali Tace" Ina Aminullah Dan Allah, Nan ma'aruf ya tsareta da ido be gane me take cewa ba, Mamanta ne tazo kusa da ita tace" Aminullah, Allah yai mai rasuwa, wani rintsa idonta tayi hawaye suka fara zubu mata, da ita kadan tasan me take ayyanawa a zuciyar ta
Ma'aruf ne Yace" Aminatu ganin iyaye sai yasa be ambato sunan da yake kirantaba zinariya ko Sweet baby, Yace" Dan Allah kiyi hakuri, though bansan ya kuke dashi ba kiyi hakuri, Nasan dawainiyar da yakeyi da iyayanki kiyi hakuri, Allah yafi mu sonshi, Nan ta kalle mamanta, Mamanta ta kashe mata ido alamar ta hakura karta nuna komai,
Nan ta Dan tashi daga kwanchan, Da jin kina a jikin gadon, nan mummy tai ta mata sannu, kowa yana ta mata sannu, ana cikin haka saiga murjantu ta fado
Wani kallo Aminatu tai mata da saida yan hanjinta suka kada, Murnajatu, ta gaishe da kowa da kowa tai musu ya hakuri, Kamar Aminatu bazata amsa ba se Kuma tace" Alhamdulillah, Nan murjanatu tace" Su mummy kui tafiyarku zan tsaya da ita nai jinyarta kuje Ku huta,
Sukace" kai amma mungode, Allah sa miki albarka, Murjanatu tace" Ameen Ameen
<> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <>
Bangaren Lubna kuwa, shuru shuru har dare ma'aruf be dawo ba, gashi a dakinta yake, Ta hada mai abinci da juice me dadin gaske, tasha kwalliya kamar Sabuwar amarya, Ga ko Ina na dakin Kamshi yakeyi, har 9 taji shuru, kasa hakura tayi tazo har part din Aminatu ta kwankwas taji ko Ma'aruf na part din, nan taji shuru, zama a kofar part din tayi, Hannu tasa akai tana kuka wannan wani irin tsane Ma'aruf ke mata, da taga bame bata amsawa daki ta wuce ta dakko wayantaKira tayi ringing 1, 2 yai picking, Yace" Lubna, tace" my Dr kana inane najika shuru, Yace" eyyah I wanted to call you bansa ma natsuwa ba, Aminatu ne ba lafiya ta fadi dazu a toilet, So I'm inanan zuwa anjuma, Eyyah tace duk da bason Aminatun take ba seda ta tausaya mata sannan ta kashe wayan tace kuma mtswww Allah ya Kara, se tauyemun hakkina ake akan wannan *YAR MAKAFI*
Ma'aruf yana gama waya Aminatu ta kalleshi tace" ka tafi gida Ga murjanatu nan zata kula dani, Yace" kin tabbata? Murja da katsalandan tace" yap, Aiko yai tafiyarshi, Yace" idan akwai wani Abu a kirashi
Bayan ya fitane, Aminatu ta kalle murja tace" meye ya kawo ki? ba mun raba jaha ba?
Murjanatu tace Dan Allah kiyi hakuri, Wallahi nima mutuwar Aminullah dinnan ya sa na dawo hanya, na gane lalle duniya bata da tabbas, nima INA rokon Allah ya yafemun duk laifukan da nayi, Kuma Nima ki sani a addu'a Allah ya fito min da miji na gari da sauran yan'uwa da basui aure ba, Allah ya hada kowa da miji na gari
ESTÁS LEYENDO
YAR MAKAFI
Fantasíalabarin wasu yarinya ne taso cikin talauci ga iyayanta makafi, A wajen yawon baransu ta hadu da wani saurayi........