Episode 2

3K 184 2
                                    

.
. ❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄¸*✳'☆´-
…¸.¤ª '☆´_____________☾_____________-'☆´-
   💕💞  *MAKAHON SO* 💞

       *Blinded  Love*❤
•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•  ゚ ☆   
¸.¤ª☆“˜¨''''''''¨  *'''_*Written By Beelkeey Shuwerh*_ ''* “˜¨¨☆ª¤
¸ 。 ゚'☆_____________☾_____________'☆´
_________________•☾• ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯…¸.¤ª☆“˜¨¨ ¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯¯•☆•。 ¯•☆•  ゚☆    
¸.¤ª☆“˜¨•。❉ *.¸¸.*✳*.¸¸.*❄*.¸¸*❆ *.¸¸.*❄.¸¸.*✳*.¸¸*❄*.¸¸*❆ ¸¸.*❄.¸¸.*✳ *.¸¸.*❄*.¸¸*❆

® ​​​*REAL PURE MONENT OF LIFE WRITERS*​

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ❤ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers
FANS-459256761123035
# http://
maryamsbello.blogspot.com

   
     Dedicated to my dear one and only Ummu Aysha *Arfat novel writer* no need for long essay you know I so much love you.

     *Don't be a silent Reader tell me how you feel or think about my Novel*

Follow me on wattpad @beelkeey Shuwerh

Episode 2

March, 2018

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Later during the day, gaba d'aya family'n suka had'u dan having lunch, Suwayd ne k'arshen shigowa.

Kallon ko ina yayi yaga bata nan, zuba ido yayi yaga daga ina zata b'ullo amma shiru gashi kowa ya faracin Abinci amma ita bata shigo ba.

Mik'ewa yayi, da sauri Mammy'n shi ta kalleshi tace " Where to? ".

Sosa kai yayi yace " Mammy dama sak'o aka bani na bawa Granny naman ta shine zanje in kai mata ".

Tsab ta gane k'arya yake dan tin yana k'arami indai zaiyi k'arya saiya sosa kai amma tace " ohky buh you have to be fast ".

Abunka da mai jiran k'iris tuni ya fice daga Babban falour'n ya nufi garden dan yasan anan kawai zai same ta.

Inda ta saba zama ya hangota kwance tana bacci tana sauke ajiyar zuciya da alama taci kuka ta gode Allah, tsugunawa yayi yakai lallausan hannun sa kan gashin ta daya kwanta luf_luf a goshin ta yana wasa da shi, ganin ta d'anyi juyi yayi saurin janye hannun nasa.

Sannan ahankali yasa hannu ya d'auketa ya d'au mata teddy'n ta ya nufi part d'in Granny dan anan d'akin 'yan matan gidan yake.

Da sallama ya shiga ganin babu kowa a falour'n yasa ya wuce bedroom d'in su, ahankali yasa hannu dan karya tashe ta ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga sannan ya mayar ya rufe.

Manyan gadajene guda biyu a d'akin, white and purple sai pink and white in each side of the bed there is Wadrop and dressing mirror.

Akan pink bed d'in ya shimfid'e ta sannan yayi kissing forehead d'inta ya bud'i baki ahankali cikin husky voice d'insa yace " Ana asif ya Habibty, am terribly sorry is not my fault, is just that am _Blinded by your love_ insha Allah you will be my everlasting, you are my everything, my love for you is a journey starting at forever and ending at never, da sanki nake kwana nake tashi, sanki yana yawo ajikina tamkar yarda jini yake yawo ajikin b'argo,  without you I feel broke like i'm half of whole, without you I've got no hand to hold, without you I feel torm like a sail in a storm, with out you am just a sad song ".

Hannun ta ya d'ago yana kallon diamond ring d'in daya saka mata wanda yasan haryau batasan waya saka mata ba, brightly smile d'insa ya saki har dimples d'insa suka lotsa yace " S love S, Safwah the moon that will never escape from the star, I am the star and you are the moon Habibty ".

Lallausan bargon ta yasa ya lullub'e ta sannan ya k'ara mata gudun Ac ya fice.

Babban falour'n ya koma inda ya tarar su Mammy harsun gama sun tashi, baice da kowa k'ala ba yaja plate yayi serving kansa, hankali kwance ya fara cin abincin.

Ganin 3:00 pm yayi yasa yayi saurin tashi dan zaiyi bak'i,  Kadsah ce ta tayi saurin biyo shi tace " Ya Suwayd please maths assignment zaka koya mana ".

Cikin had'e fuska ya kalli watch d'in hannun sa yace " 5:00 pm ku same ni a d'aki na, make you guys stuck my rules into that your cockroach heads understand? "

" Yes " ta amsa da sanyin murya.

Cikin zubda kwalla Kuwaysah tace " fuck you sis ya zaki kaimu assignment gun ya Suwayd ko kin manta shine? "

" Karki zo kinji kiga yadda zanyi dake a gidan nan useless , pathetic fool kawai " yasa kai ya fice.

Part d'in Granny suka nufa suka zauna jigum_jigum, suna zaune Ya Haidar yayi sallama ya shigo.

Kallon Kuwaysah yayi dake faman zubda kwalla dan tasan yau mai kwatar su sai Allah, sannan ya k'araso ya zauna ya janyo ta jikin sa abinka da mai jiran k'iris tuni ta fashe masa da kuka, saida ya rarrasheta sannan ya tambayi Maya faru.

Cikin sheshshek'ar kuka tace " ba kadsah ce tacewa Ya Suwayd wai zamu zo ya koya mana assignment ba ".

Tausayin sune ya kamashi dan yasan yau za suci k'aniyan su, sannan ya dake ya shiga kwantar musu da hankali.

Mik'ewa yayi ya fice ya nufi part d'in Ummy'n su, da sallamar sa ya shiga.

Ganin ta zaune a falour shima ya k'araso ya zauna cikin nutsuwar sa yace " sannu Ummy ".

" Yauwa Aliyu na, gadanga k'usar yak'i ", murmushi yayi da a rayuwa yanaso Ummy'n shi ta kirashi da sunan , hira suka shigayi suna cikin hirar Safwah ta shigo tana turo small cute mouth d'in ta ga kyawawan idon nan nata a kumbure.

Kallon ta Ummy tayi tace " ke kuma lafiya zaki shigo mana ba sallama?  Da alama ma yanzu kika tashi daga barci, kinyi Asr prayer? ".

Nodding kanta tayi alamar A'ah, " karki wuce kije kiyi yanzu na kirawo Suwayd ", ai tuni jikin ta yafara rawa ta rik'e kunnen ta alamar bada hak'uri tace " Am sorry Ummy wallahi Aljana zai cemin ", ta fashe da kuka dan sosai kalmar aljana ke ci mata rai.

Tausayin tane ya kama Ummy ganin daga an ambaci sunan Suwayd jikin ta harya fara rawa,  " come on Baby share hawayen ki am just kidding you kinji? "

Gyad'a kanta tayi amma har alokacin hawaye bai dena zuba a idon ta ba.................


  *'Yar Gatan Mhiss_B_Hal Ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now