Abba ne yace da khalifa yaje yace mariam ta fito suci abinci khalifa ya amsa da toh. Yana xuwa bakin kofar ya ganta kulle cikin sa'a kuwa yana murdawa yaji ya bude. Da sallama ya shiga dakin yashiga buga kafarta ahankali amma taki tashi haka yayi ta dukan ta amma ko motsi ba tayi ba haka ya fita yaje ya sami Abba yace mishi taki tashi.Abba ransa ya soma baci yace da Safia ta je ta tadota tana shiga ta ganta kwance kan gado tayi rub da ciki kamar mai bacci tana xuwa ta xauna kusa da ita tace "mariam ki tashi Abba ne fa Ke kiranki" haka taita magana amma ko motsi batayi ba. Aguje ta isa inda su Abba suke xaune ta Sanar dasu halin da ake ciki cikin tashin hankali yanufi dakin mariam ya na xuwa ya nufi inda take ya shiga jijjigata amma taki tashi. Hankalin shi bakaramin tashi yayi ba duk ya bi yarikice ya dauketa ya nufi mota anty na ganin sun fito rike da Maryam ta saki wani ihu kamar da gaske tanakuka tana cewa ta shiga uku nan ko cikin xuciyarta kukan dadi takeyi kamar an xuba mata ruwan sanyi axuciyarta takeji. Saida yakai bakin mota sannan ya tuno baima dauko mukullin motar ba yace ma anty baby taje ta dauko. Cikin yan mintuna kalilan ta dawo da mukullin mota ahannunta ta mikawa Abba ya saka ta a back seat. Anty naxaune agaba sai anty baby dake rungume da mariam Abba kuma na tuki. Agigice suka isa asibitin suna shiga likitoci suka karbe ta sukai emergency da ita. Sai bayan 30 minutes sannan likitocin suka fito. Dayan likitan ne ya ceh yana bukatar ganin Abba,jiki a sanyaye ya tashi ya bi bayan likitan Har cikin office dinshi. Likita ne ya Dan yi gyaran murya yace are u her father? Yes I'm her father cewa ar Abba likitan yace ur child is in serious problem saboda tana dab da kamuwa da hawan jini. Abba ya mike tsaye ya ce hawan jini kuma yace yeah of course hawan jini kuma sai kunyi takasatsan da lafiyar ta in bahaka duk abunda ya biyo baya kukuka janyo. Haka likitan yai ta bashi shawarwari ya kuma cemishi da ya tambayi Ita mariam yaji mey Ke damunta kana da ga bisani yai mishi godiya ya fice daga office din. Ya na fitowa yaga su anty da anty baby su na ta rusar kuka suna ganinshi suka taso da sauri suna tambayar shi meya sameta Abba dai bai ce musu komai ba yashiga ward dinda mariam take . kwance yaganta kan gadon asibitin ta na bacci hankalinta kwance, kujera yaja ya xauna kusa daita ya kamo hannunta ya shiga murxawa ahankali wasu xaxxafan hawaye ne suka shiga yimishi xarya a idanu ahankali ta bude idonta ta na kokarin tashi xaune yai maxa yamaida ta yayi mata alama da ta kwanta. Abba ne yai karfin hali yace Maryam mey Ke damunki Har kike kokarin jawo ma kanki hawan jini, eye Mariam. Mariam bata ce komai ba saima sadda kanta da tayi Abba yace mariam magana nake mikifa.tace Abba ba komai kawai dai.......bata karasa maganarba Abba ya katseta da cewa mariam nifa mahaifinki ne idan baki gayamun damuwarki ba toh waxa ki gayawa ahalin yanxu eh mariam kina kokarin jefa kanki cikin wani hali da wane ido kike san na kalli ubagiji ranar gobe qiyama a matsyina na mahaifinki eye mariam, kidubi girman Allah ki gayamun damuwarki. Mariam tace cikin sarkewar murya Ab... Abba kawai maganan exams dinane kasan yanxu ss3 Nike kuma exams din mu na kusa shine narasa yadda xanyi. Abba yace karya kikeyi akan exams ne xaki tadaa hankalinki? Mariam tayi rau rau da ido tace Abba ka yadda dani ba karya na Ke makaba. Ba Dan ya yardaba yace toh Allah ya kyauta. Duk wannan abun duk a idon anty da anty baby Dan su basu Masan sun shigoba. Abba na juyowa ya ga su anty da anty baby kamar waenda ruwa ya ci ganin Abba na kallonsu yasa anty saurin karasowa ta rungume mariam Dakae kan gado ta na kukan munafurci tana cewa haba mariam kinga yadda hankalinmu ya tashi kuwa? Ta sake ta tana kallon ta ta ce mariam i've told u times without number stop bothering itself akan karatunnan naki duk kinbi kin rame kwanakinnan takare maganar tareda xubar da crocodile tears tasake rungumeta. Ahankali tashiga yi mata magana cikin kunne batareda tabari kowa yajiba tanacemata "idan kika bari abbanku yasani sai na ci uwarku gabaki dayanku. Ita dai anty baby tana kallon su sai dai batace musu komai ba danta San datayi magana yanxu xata komo kanta, kuma ita tasan rashin lafiyar da mariam keyi bana komai bane sai na rashin ganin mahaifiyarsu kusa dasu da kuma irin kuntatawar da anty Ke musu bayan idon mahaifinsu.
Anty baby ce takaraso inda mariam Ke kwance itama tarungumeta tace mariam sannu yaki Ke jin jikin naki? Takarashe maganar Dauke da damuwa a fuskarta mariam tace jikin Alhamdulillah. Anty baby ta dago takalle mariam tacemata yanxu kinga kin hanamu xuwa islamiya kin kuma hana Abba xuwa office Maryam taxumburo baki tace au haka ma xakice? Anty baby tace were u just pouting? Takarashe maganar with all seriousness mariam ta rufe baki tace Allah nadena dukansu sukai daria lokaci daya ban da anty daketa dallo musu harara sukam yima sukai kamar basusan daita awajenba.Don't forget to drop ur vote
YOU ARE READING
Komai Daren Dadewa
General FictionWannan littafin yana dauke da darussa masu yawa akan zamantakewar rayuwa. Sannan banyi wannan littafin Dan ci zarafin wani ko wata ba