🥀🌺🥀 *FAHIMTA*....🥀🌺🥀
*XINNEE SMART*
4........ Cikin zafin naman da shikansa baisan yana dashi ba ya naushi rogi dake kanta kafun yayi wani yun'kuri yasake kaimasa duka a ciki nan fad'a yakaure inda da'kyar kb yarabasu,
Sukam su giban dama tunda suka ga anrufu wa ogansu sukayi ta kansu, rogi dayaci bugu baimasan Inda kansa yake ba dan bakinshi jini kawai yake fitarwa, da hancinsa,
Gun yarinyar yanufa wacce tuni tadad'e daficewa a hayyacinta, zaninta dasuka d'aure mata hannu suka ya warware, ya yafamata, d'aukarta yayi yafita da sauri yanamaicewa, kb yi sauri ka janyo mota yi sauri dan ganin yake idan aka 'bata lokaci zata iya mutuwa,
Dan yadda take Sam babu alamun numfashi atare da ita,Kb da gudu yakoma cikin club d' in dan sossai tausayin yarinyar yakamashi, dan shidai duk iskancinsa baita'ba tunanin yida kamar yar wannan yarinyar ba haba mai mutane suka zama ne? Yai wa kansa tambayar da bashi da amsa, shi kansa dan haka yakawar da zancen a ransa,
Direct asibitin Aminu kano suka nufa da ita, duk da cewa darene amma hakan bai hanasu samun likita ba, take aka fara duba ta sungane cewa fargaba ce tasaka ta dogon suma wanda a kowani lokaci zata iya farkowa, ajiyar zuciya yayi bayan likita yagamai masa bayani, dubansa yakai Kan kb yaga Shima shi yake kallo,
Murmushin ya'ke sakarmasa, kb yace wai ya akayi kafito nifa nusy ce tacemun wai inlalla'ba mata Kai wai kashareta shine take cemun wai kafita nasha mamaki da na hangoka a gurin, numfashi yaja yabawa kb labarin yadda akayi... Sossai kb yajinjinawa al'amarin, sunyi shiru suna jiran tsammani sai ga likitan yazo yashiga d'akin, binsa sukayi, ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tsabar zazza'bin dake jikinta, still har yanzun idonta a rufe alamun bata gama komawa daidai ba,
Yan gwaje gwaje likitan yadad'a yi,umarni yayi da su bishi office dinsa,
Dubansu yayi yace....... Garku damu insha'Allah zata koma daidai kawai razanace tayi,... Ma'aruf ne yadubesa yace... But doctor please inason aduba adubata sossai sabida akwai wanda yayi attempting 'bata mata rayuwa bansaniba ko da wani matsala shiyasa nake son adubata.... Kallonsa kb keyi cike da mamakin maganarsa, dan shi aganinsa tunda dai yataimaketa kuma likita yace ba wata damuwa ai shikenan Koda dai baisan dalilin maganarsa ba dakuma yayi wani tunanin sai yafahimci da gaskiyarsa,
Likitan ya tabbatar masa da zasu bincika idan numfashin ta yadaidaita,
Asubar farko wayarsa tayi 'kara gurin aikinsa ne kenemansa, da gaggawa, dan haka yanayin sallar asuba, yaje yai bucking jirgi izuwa Thailand, wanda zaitashi 7:30 na safe dan haka awa d'aya da rabi yarage masa yatafi, a gurguje yadawo gidan su kb yayi wanka yashirya, kb ne yajashi a mota zuwa asibiti dan sossai yake son sake ganin yarinyar Sam yarasa mai yasa ta tsaya masa a rai, kawai sai yaba kansa amsa da tausayinta yake ji, Koda sukaje tana kwance idonta a rufe da alama bacci take dan nose tasanar dasu tafarka tun jiya,
Fuskarta ya'kurawa ido yana kallo sossai taimasa kyau duk dacewa yarinyace wacce komai na halittar budurci bai bayyana mata ba amma kyakawace ta kwatance, duk darashin wadatar dake tare da ita wayar kb ce tayi ringing, yafita waje domin ya amsa ganin kb yafita ne yasa yasaita wayarsa yafara snapping d'inta pictures, sunkuyawa yayi daidai fuskarta, yafara yimusu selfie ba'ka'kautawa harsaida yaji alamun za ashigo yayi saurin matsawa had'i da 'ko'karin saita kansa, kb ne tare da likita suka shigo duban likitan yayi yace doctor I hope anyi binciken ba wata matsala gyad'amasa kai yayi had'i da fad'in nasanya nose tayi mun binciken kuma ta tabbatar munda ba abunda yasameta in fact ma she is still virging, wata ajiyar zuciya yasauke, wanda saida kb yadubeshi, doctor kam murmushi yayi yace...... Garka damu insha'Allah ba wani matsala I can see that you love ur sister so much so don't worry everything will be fine ur sister will be fine ok? Just keep caring of her, likitan ya'karasa da bubbuga kafad'ar sa, murmushi yayi yace nagode sossai doctor, gyad'amasa Kai yayi yafita,
Shima agogon hannunsa yaduba, kb muje time natafiya, juyawa sukayi suka fita waje, kb yadubeshi abokina ko kasan kulawar ka akan yarinyar nan yayi yawa? kana nema fa kaza'ke, duban kb yayi yace mai kake nufi? No ba wani abu nake nufi ba kawai dai gani nayi kana over acting akan matsalar ta, mtss kb dan Allah mutafi idan baso kake inyi missing plite ba, abunda nasani kawai dai ina tausaya mata ne, ya fad'a cike da gundura da maganar, Kai kb yad'aga shikenan Allah ya kyauta, Amin.,Ma'aruf ya fad'a had'ida fara tafiya mota suka shiga kb yaja sai airport,
Tunsanda suka fita tafarka 'kamshin da taji akan pillown datake ne yasa ta lumshe idonta dan sossai ' kamshin yamata dad'i, bud'e idonta tayi a hankali, Jin magana sama sama dan sam bata fahimtar mai ake cewa tana daijin magana juyar da Fuskarta tayi saitin da take Jin maganar, maza ne su biyu d' ayan kawai ta iya ganin fuskarsa, tayi 'ko' karin hango fuskar d'ayan amma takasa tana ganin sanda yatafi, haka kawai taji haushin rashin ganinsa da tayi,mai da kanta tayi taci gaba da sha'kar kamshin turaren wanda batasan na waye ba, a ranta kuma tana godewa Allah da azzaluman basuci nasara a kanta ba, hawayene ne yafara gangara a gefen idonta, tana mai tuna Tata kalar rayuwar wazai Fahimci halinda nake ciki, FAHIMTA ta sai Allah, ya Allah ka kawomun d'auki kaji'banci lamurra na, wani kuka mai ban tausayi ne yasar'keta, haka taita yi ba mai rarrashinta harsaida tagaji tayi shiru dan kanta, *wannan kenan*...........
.......................................................Isarsu filin jirgin baifi minti goma ba aka soma Kiran fasinjoji, Ma'aruf, yadubi kb, kb.... Yakira sunansa da alamun serious magana zamuyi, dubansa kb yayi had'i da amsawa,
Kb Amana dan Allah ka kula da amanar nan yarinyar sossai nake tausaya mata wanda ni kaina narasa dalili, abunda zan iya cewa kawai 'kan' kantar shekarunta nasa ina dad'a tausaya mata, kb katabbatar tasamu lafiya da kyau sannan kayi 'ko' karin sada ta da gidan iyayenta, ri'ke hannunsa yayi duka biyu, promise me that you will do this for me? I promise you Ma'aruf zanyi duk yadda kake so insha'Allah baza asamu matsala ba, nagode kb, zanturo Maka wasu kud'in a account d'inka, kayi duk abunda yadace please... garka damu komai zai tafi daidai kaidai Allah yatsare, yakai ka lafiya, Ameen nagode sossai abokina, suka cafe had'i da rungume juna bayan juna suka d'an bubbuga, sanan suka saki juna suna murmushi daidai lokacin aka Kira Ma'aruf nan yanufi cikin jirgin suna masu d'agawa juna hannu, cike da kewar junansu,Tunda Ma'aruf yashiga jirgin yafidda wayarsa yana mai sake kallon hoton yarinyar wanda yad'auketa d'azu hoton yayi kyau sossai dan lokacin da yad'aukeshi dai dai lokacin da tayi dariyar 'kuda, irin dariyar da mutum kanyi bai saniba idan yana bacci yawanci jarirai sukafi yinsa amma manya ma suna yi,
Kallonta yake yi yayin da kowani second wani abu kebin' kafarsa izuwa, 'kirjinsa, to meye wannan? baibawa kansa amsa ba jirgin su ya Lula,*Safe tripe MA' ARUF MUHAMMAD*
_Waye MA'ARUF_??
_Xinnee smart_
*Comments d'inku 'karfun* *guiwata* 💃🏻