🥀🌺🥀 *FAHIMTA*.... 🥀🌺🥀
_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life......._
*XINNEE SMART*
13......ganin tayi shiru ne yasa yadaka mata razananniyar tsawa wacce tasake tsorata ta,
Kin amince ko kuwa? yatambayeta, a tsorace tace na... n... a.. Amin... ce, hhhhhhh shegiya shu'uma dangin shaid'an, puuhhhhhhaaahh, haka yaita sakin dariyarsa sai da yagaji dan kansa,
Sannan yayi shiru,
Wata iska yahura mata a jiki take kayanta suka yaye, nan fa yahau sukurkud'ar abun banza tamkar wata jaka,
Itakam Rukayya tun tana gane mai yakeyi harta daina fahimtar sa, dan bama tasan a wace duniyar take ba tunani take a mace take ko asume...?
Yau duk jarabar Rukayya tashafawa kanta lafiya dama ance gaba da gabanta.... (wai aljani da ya taka wuta yace gaba da gabanta)
Saida yad'auki tsawon awanni yana sukurkud'ar ta sannan yaqyaleta had'i da kecewa da mahaukaciyar dariya, yarinya kinmun yanda nakeso ya fad'a yana lasar baki,
sannan yakece da mahaukaciyar dariya, Rukayya kinsamu mijinki yadda kike soooooo...... Muryarsa na fitar da amo har ya'bace,
Rukayya kam batama san inda kanta yake ba, dan bata farka ba saida sanyin asuba yatasheta, cike da wani irin ciwon jiki ta tashi lokacin da taja numfashi tasha'ki warin da yabarmata take tafara yun'kurin amai, amai take sossai,
Wanda yun'kurin sa ne yadakatar da Ma"aruf dake shirin fita zuwa masallaci, dasauri yanufi d'akin, ta, a dur'kushe yasameta, tana ta faman yun'kurin amai aikuwa haka taita she'ka aman kamar zata amayar da hanjinta,
Shikuwa sai sannu yake zuba mata mi'kewa tayi a wahalce zata shiga toilet jikinsa na rawa yad'auketa yakai ta toilet d'in, Saida ya wanke mata jiki tas, yace tayi alwala, sannan yafito da ita, doguwar riga ya zura mata da hijab, sannu zantafi masallaci amma bazan jima ba zandawo kinji? Allah yabaki lafiya, sannu har yafita yana jera mata sannu kamar Kar yaje masallacin, itakuwa da ido tabishi cike da mamakin wannan kulawa dayake bata amma da ta tuna abunda yafaru jiya sai tasaki wani murmushi,
Amma duk da haka tana jin fargaba saidai kuma ta 'kudurci gwada shi domin ta tabbatar da zargin ta............dan haka yana dawowa yasameta a kwance kamar mai barci dan haka sai yazauna yana gadinta,
Itakuwa da wutsiyar ido take kallonsa, can dai tabud'e ido kamar wacce ta tashi daga bacci, da hanzarinsa ya'karasa, gareta, sannu ya fad'a jikinsa na rawa.... A gwatsine tace.. Hmm,
kina bu'katar wani abu ne? Ya tambayeta, cike da isa tace a ina zansamu pepper soup d'in talo talo,? Jimm yayi kafun yace, amma da safennan?
Au bazaka samomun ba kenan ko?
No ba haka nake nufi ba, haka ne mana kawai dan ban isaba, shiru yayi yasunkuyar da kai, itakuwa sai masifa take masa kamar wata uwarsa, saida tagama yashiga bata ha'kuri daga baya yami'ke... Yace bari inje inemo miki... dasaurinsa yami'ke, har yakai bakin 'kofa, tace barshi ma nafasa ci, tom yace mata had'i da dawowa yazauna cewa tayi jeka d'akin ka zan kwanta cike da bin umarnin ta yace Tom, yana fita ta mi'ke tahau kwaso shoky cike da farincikin ha'karta ta cinma ruwa,.........
.......................................................
Rukayya fa duniya sabuwa a gunta, dan sossai take tsula tsiyarta, a gaban Kowwa na gidan yimasa abu take ko ajikinta, hakan ba 'karamun ciwo yakewa Mum ba dan har kuka take zama tayi sai dad ne yake rarrashinta had'i da nunamata cewa kukan ta a gun Ma"aruf bala'i ne addu'a yakamata taimasa ba kuka ba,haka taita addu'a ba dare ba rana,...tafawwa lawa Allah lamarinta, domin tasan shine zai kawo mata d'auki,
Yauma Yar mulkin ce akan d'aya daga cikin kujerin parlour, hannunta ri'ke da tuffa, tana ci, yayin da take canza duk tashar da taga dama, zainab ce tazo gabanta tace Aunty, na kammala aikin, shiru bata amsa ba, har saida tasake maimai tawa, cikin masifa tace....
kekam wannan ya mijinki yashiga ukku, haba yarinya sai shegen surutu da rashin nutsuwa? Mtss kin tabbatar kin wanke toilet d'in da kyau?
Zainab jiki na rawa tace Eh.....
Gud,
maza jeki had'a mun kunun gyad'a..... cike da inda inda, zainab, tace... AUNTY yaufa da islamiya kuma gashi gurin after 4ban tafi ba malam zai tare ni la.....bata 'karasaba tasauke mata yatsunta biyar, au ji iskanci, ni Zaki fad'awa islamiya, ubanki mai dattin hula yaci ta kazakazarsa bare kuma ke, to wlh kikaimun iskanci kindaina zuwa islamiyar kenan sai inga ta tsiya,
Tunda ba ubanki ke biya miki kud'in makarantar ba, kuma maza da zafi kitafi kiyimun abunda nace tunkafun raina yagama baci a kanki, banza dabba kawai....kuka kawai zainab keyi cike da tausayin kanta, haka tanufi kitchen d'in tasoma had'a mata abunda ta Sakata, tanayi tana sharar 'kwallah,
Mum datagama ganin komai daya faru ne ta'karasa saukowa dama tana sama ne,
Kai tsaye gurin Rukayya tanufa bata'bata lokaci ba tasaukemata tafi, nuna ta tayi da yatsa, kishiga taita yinki fa, duk abunda kikeyi wlh ina sane kuma ina lura dake, zainab ba baiwa bace, dan haka Kidaina Sakata aiki idan ma Zaki sa ayimiki aiki baga masu aiki nan ba? dole sai ita? to daga yau sai yau Kar inkoma ganin kinsaka ta aiki,
Ai idan kina da wayau nan gidan mijinki ne kamata yayi ki mi'ke kiyi aikinki ba dole wasu abubuwan sai mai aiki ta Miki ba musamman abunda yashafi bedroom d'in ku,dan haka nidai daga yau na hana, abari itama idan taje d'akin ta tayi.........Wa d'in??
Rukayya da tunda mum ta mareta take ri'ke da kunci ce tai wannan tambayar, mum, bata bata amsa ba takira zainab, maza jeki kiyi shirin makaranta kitafi, to zainab tace cike da fargaba dan tasan saitayi abunda yafi kunun gyad'a,idan ta tafi saidai kuma bata da za'bi dole tabi umarnin mum,
Ganin mum bata kulata ba baihanata cigaba da maganarta ba,
Ai wannan ita da aure sai a lahira, dan babu namijin da zai iya auren wannan dangin matsiyatar,
Sossai kalamanta suka daki mum, amma hakan bai hanata ce mata, Allah ko?
to kuwa zan baki mamaki dan zainab sai ta auri mijin da zai girgizaki...... Sallamar ma'aruf ce takatse mum daga Maganar datake,
Ai Rukayya najin muryarsa tasaki wani kukan muna furci, da saurinsa ya'karasa gabanta, a kid'ime yake tambayarta, mai yafaru mai yasameki? Mai akai miki?tambayoyin da yake ta jero mata kenan,
Cikin kukan kissa, takwashe 'karya da gaskiya tafad'a masa had'i da cewa.... Nikam dai idan baka d'auki mataki ba gidanka zan bari tunda mahaifiyarka bata sona ..... Tana gama fad'in haka tafita,.... kiranta yake amma bata ko juya ba,
Juyawa yayi yadubi mum, shikenan mum kin rabani da mata ta burinki yacika, yana gama fad'in haka yabi bayan Rukayya, wacce ba yadda baiyyi da itaba amma saida ta tafi gidansu,
Mum kam takaicine yacika mata zuciya, addu'ar dai data saba, takeyi, zuciyarta cike da tunanin mafita, zuciyarta ce tashiga sa'ka mata wani abu saidai tana tsoro dan tana ganin kamar da cutarwa acikin al'amarin, koma dai Maine ne? zata nemi za'bin Allah acikin al'amarin..........................
*Keep following*
*Yanzun muka fara shiga cikin labarin*🤗_Xinnee smart_
*Follow me on Instagram* @xinnee smart