F.W.A

3.3K 86 19
                                    

LABARAI UKU DA KU KE SO A NAIRA 500 KACAL

A ZATO NA
Tare da alkalamin *Jeedderh Lawals*

"Ke dai kawai ki ce, tsoron matan Yaya kike yi. Kina tsoron kiyi hadaka dasu, ki dinga challenging dinsu, suna challenging dinki, kina tsoron may be, you'll lose...".

Nayi dariya da daga jin ta kasan bata kai zuci ba, nace "Jan kenan. Kin sanni sarai da tarar aradu da ka, sai dai wannan aradun tafi karfina, idan na dauketa tarwatsa ni zata yi. Maganin kada ayi, kada a fara. Gwanda in zauna a inda Allah Ya ajiye ni, kada in kai kaina inda zan hallaka!".

Da alamun ta fara gajiya da kokarin sanya ni fahimta da take ta kokarin yi tunda zancen wannan ya taso, tayi kwafa, "shi yasa zaki gwammace ki cuci kanki kenan akan ki bi zuciyarki? Cause let's face it, kina son Yaya Hilal, ni nasan wannan. Yanzu kin gwammace akan wani dalili naki na daban, wanda ba na Allah da Annabi ba, ki tauye zuciyarki?".

Na daga kai na kalleta sosai, cikin girgiza kai, "baki san abinda na gani ba Jan, baki kuma dandana abinda na dandana ba, ba zaki taba fahimta ba... Ina kallo kiri-kiri ba zan jefa kaina inda nasan takaicin miji ko kuma na matansa ne zai kashe ni ba. Ba zan iya ba!!". Na kara maimaita mata, don tasan cewa da gaske nake, kuma ba zan canza maganata ba.

"To amma idan fa shi wanda kika kafe zaki aura din, shima yazo zai kara aure?".
Nayi shiru cikin tunani, lokaci zuwa lokaci ina irin wannan tunanin, sai dai har yau akan mafita daya nake sauka, "sai ya zaba ko ni, ko ita!". Maganar ta fito tun daga kasan zuciyata har cikin bakina, babu wata tantama ko fargaba.

Ta zare ido cikin mamaki, ta daga baki zata yi magana, nayi gaggawar katseta, "na san abinda kike kokarin yi Jan, maganar gaskiya zan fada miki, itace ki daina bata yawun bakinki. So kike yi kiyi provoking dina, ko kiyi convincing dina, koma dai wannene daga ciki ba zai yi aiki a kaina ba. Kin san hali na sarai. Zama da kishiya daya ma bai cikin tsarina, Allah ya gani, balle kuma mai mata har biyu? Not a chance! Ba wai ba zan yi bane, ba zan iya ba! Don haka gwanda ma kiyi hakuri kawai, mu canza magana, kafin rayukanmu su zo su baci a banza!".

Maganar da nayi ta sosa mata rai, sai dai tasan kamar yadda nace, idan ta kafe akan wannan maganar, lallai rayukanmu zasu baci. Don haka ta girgiza kai kawai, "Allah ya ganar dake" kadai ta iya furtawa.
Nayi murmushi ina kai gorar yoghurt din dake hannuna baki, "Ameen".
Ban nuna mata na kula da kallon da take min ba na takaici da ban haushi, abu daya na sani, ba zan taba canza magana, ra'ayi, ko tsari na ba. Ba zan taba zama da kishiya ba!!.


*******

Na'ilah, kyakkyawar matashiyar budurwa ce da take tasowa.

Tun tana yarinyarta taci wani alwashi, kan cewa ba zata taba aure gidan kishiya ba!. Hausawa suka ce wai 'in gemun dan uwanka ya kama da wuta, shafawa naka ruwa'. To itama din sai ta shafawa nata. A wayonta, idan ta auri saurayi kamarta, ba zai taba karo aure ba, to amma wa ya sani?.

A cikin haka sai ga Bilal Qaseem ya fado cikin lamarin. Shi ba mata daya ba, biyu ma gareshi. Duk da cewa ta kamu da son mutumin cikin rashin sani, hakan bai sa tayi tunanin saddakarwa ba.

Sai dai, abinda matashiya Na'ilah bata sani ba, shine, sau tari abinda muke gujewa, shi yake bibiyarmu a baya, a duk inda muke kuwa, cikin ko wani yanayi ko hali muke ciki. Duk guje-gujenmu, zamu zagayo mu same shi dai.
Kamar yadda wani baya auren matar wani, wani baya haifar dan wani, ba'a taba kaucewa abinda Allah ya riga ya rubuta.
To me zai faru, idan abinda matashiya Na'ilah ta ki jini, tafi tsana, take kuma ganin babu ta yadda za ayi ya faru da ita, ya farun Kwatsam!? Bata kuma da halin guje mishi? Shin, zata iya kuwa??

Ku fado cikin duniyar littafin 'A Zato Na' domin jin yadda wannan chakwakiya zata kaya.


*******

A ZATO NA...! Where stories live. Discover now