One

1.1K 52 6
                                    

Episode one
WAYE SHI(shaffik ko Ahmad)
Na: Bintnagz (Hasna mansur nagoda)
Wattpad @bintnagz

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"

**********
Wata katafariyar mota mai kofa 6 ce ta shigo cikin main building din galaxy cosmetic company, daya daga cikin bodyguard din motar ya fito ya bude kofar seat din baya, wata yar dattijuwa mai kimanin shekaru 55 ta fito daga cikin motar sanye da glasses a idon ta,tayi shiga ta alfarma,kana ganin ta kasan irin dattijen nan ne da suka jiku da kudi suke kuma ji da kudi, nan da nan security's din wajen suka hau yi mata barka da zuwa cikin girma tana amsawa, har ta shiga ciki tayi office din CEO kai tsaye.

Yana zaune kan kujerar sa yana bude bude takardu yana sa hanu yana ajiyewa sakataren sa ya shigo tare da sanar masa da cewa PR ta iso,ya gyada masa kai alamun ya ji, shikuma ya fita, yana fita suka hadu da ita shima har kasa yayi yana barka da zuwa rankin ya dade..
Ta amsa da barka kadai sulaiman ya kokari.
Sannan ta shiga office din CEO din.
Cikin murmushi da kunya ya taso yayi hugging dinta tare da fadin welcome ranki ya dade,
Tayi murmushi tace thank you my son,
Yayi murmushi yace, wallahi har kinsa naji kunya, ya akai kika fito cikin wannan ranar fah is almost 40 degrees, da kin sani kin mun waya...
Ba damuwa....ya ja mata kujera ta zauna, ya dau waya ya kira assistant secretary yace ta kawo musu lemon tea...
Ya zauna shima tare da fadin mummy ya akayi...
Ta kalli agogo tace ina so ka kira urgent meeting yanzu a conference hall da higher staffs din mu, tare da architect Attahir da architect salih nan da awa daya...
Mummy lafiya dai ko...?
Lpy lau idan sun hadu zaka ji.
Cikin awa daya kowa ya halara, sai da kowa ya shigo ya sami guri ya zauna sannan PR HABIBA da danta CEO shafik suka shigo....
Bayan shaffik ya bude musu taro da addu'a sannan PR habiba tace akwai wani abu da take so ta gabatar musu wanda abu ne da take son yi da jimawa bata samu ba sai yanzu.
Nan ta basu bayani akwai wani tsohon fili da company din ya dade yana ajirsa saboda haka tana so tayi expanding galaxy cosmetics ya zaman to an sami karin branch guda daya a wajen gari.
Architect Attahir ya daga hannu alamun tamabaya, ta bashi izini
Ya tambaya a ina site din yake, sannan wane irin fasallin gini za'ayi
Ta amsa masa da site din yana garin gero bayan rugar fulanin dake kauyen gero
Ina son kuma na wakilta director shaffik da kuma architect salih da attahir, company zai basu kwangilar gini da tsari da shirya komai a sabon branch din da za'a tasa.....
Shaffik yabi mahaifiyar tasa da kallo dan ko a wasa bata taba yi masa zance ba...

Ya raka mummyn tashi har mota ta koma gida sannan shi kuma ya koma ciki....

Waiwaye
Shekarun baya da suka wuce

Alhaji Ahmad attajirin ne sosai domin kuwa duk abin da dan adama zai nema a duniya babu wanda alhaji ahmad bashi da shi.
Ta inda allah ya jarabe shi shine yā daya ya malaka masa a duniya, gashi mutun ne mai bala'in son yaya, bashi da wani buri a duniya face ya malakawa yarsa guda daya da allah ya bashi komai da ya malaka.
HABIBA ita ce yar da ya haifa tare da matarsa AZARE wada allah yayi wa rasuwa lokacin habiba tana da shekara daya a duniya, toh tun bayan rasuwar azare, allah ya dorawa alhaji ahmad mugun son yarsa habiba, bashi da wani buri sai ya reni habiba ya faranta mata ya kuma aurar da ita ga hannun namiji na gari, bashi da wani makiyi a duniya da zai wuce wanda zai bakantawa habiba,ya kuma bata mata rai, hakan yasa ko aure bai kara ba tun bayan rasuwar azare har yau, gudun kada ya samo wada zata muzantawa yarsa.
Jin dadin duniya babu wanda habiba bata ciki, so da kauna da take bukata wajen uwa babu wanda abban ta baya numa mata, shi yasa kwata kwata bata da kewar uwa a a rayuwar ta.
Masu aiki kala kala babu wanda babu a gidan,duk abin da take so su suke mata.
Tana da shekara 19 ne direban ta da yake kaita makaranta da dukanin unguwoyin ta ya rasu, tun da ta taso a gidan ta san malan isuhu, hakan yasa basu ji dadi ba ko kadan .Cikin sati aka kawo mata wani sabon direba mai jini a jika dan saurayi da bai fi shekara 27 ba...
Cikin lokacin kadan habiba da Ibrahim suka saba, ya zama tamkar abokinta duk inda zata shiga ko zata da Ibrahim take zuwa, shima babu abin da yake so face ya faranta mata rai, ya kuma ganta akoda yaushe cikin farinciki yanda baban ta yake so.
Mutane da yawa kance Ibrahim yayan ta ne wasu kuma har mamakin yanda suke shiri suke, sanda batada makaranta kuma batada wurin zuwa sai su zauna suyi ta hira.
Ran alhaji ahmad ba wai dan yana so ba kawai dai dan yaga abu ne wanda habiba ke so hakan yasa ya kyale ta.....

Kan kuce mai soyyaya mai karfi ta kulu tsakanin habiba da Ibrahim, so kamar su cinye junnan su, kamar a kansu suka aka fara soyyaya har sai da alhaji ahmad ya kama su...
Randa ya kama su kuwa ranar habiba bataji da dadi na, ta sha fada ta inda ya shiga ba tanan yake futa ba, ya zata yi masa haka tarbiyar da ya bata kenan abun da zata saka masa da shi kennan, mazan duniya sun kare ne da zata ce direban ta take so, wannan ai zubar da girma ne da zubar da mutunci..
Wannan abu ne da bazai taba yuwuwa ba..

Kamar an tunduma habiba da lbrahim cikin wuta dan kuwa lamarin bai zo musu da sauki ba...
Haka alhaji ahmad yasawa habiba takunkumi, babu inda take zuwa makarantar ma shi yake kaita baya bari kowa ya kaita.
Wata rana da daddare ta faki idon abba khalid kanin babban ta da suke zama tare ta abban ta, ta yi ban garen masu aikin gidan ta shiga dakin Ibrahim, a daren ranar suka aikata abin da yafi karfinsu, cikin so da shaukin junnan su suka nuna wa juna so da kauna.

*****************************************************
To be continued on Sunday insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Where stories live. Discover now