Thirty one

122 12 0
                                    

Episode thirty one
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Gudun kar ta kara taba shi yasa ya bude idon sa a hankali.....
Gannin ya farfado tayi surin sa hannu ta share hawayen idon ta,
Ahmad.....!
Ta kira sunnan shi cikin sanyi da nutsuwa,
Ya mike zaune da kyar ya jingina da wani dutse dake bayan sa.
Ido kawai ta bishi da shi....
Ya kalle ta yayi murmushi da kyar dan zafin buguwar da yayi ya ishe shi....

""Wato gayen nan kashe mu yayi niyar yi, akan wannan yarinyar"" ya fada a zuciyar sa.

Ganin bai yi magana ba har yanxu yasa ta kara kiran sunnan shi...
Ya dadafa da kyar ya mike tsaye tare da fadin muje in raka ki gida.

Ba musu ta mike ita ma ta bishi a baya....

Tafiya suke basu cewa juna komai ba sai kuma  shaffiq ya juyo tare da fadin....
Ashe haka kike son shi da yawa....
Ta kalle shi, cikin mamaki tare da fadin shi kuma waye shi....??
Ahmad ya fada a gajarce....!!
Bata ji wani abu ba hakan yasa kawai tace
Ni dai banason irin wannan mugun wasan dan allah, ka dena, yanzu daka mutu ya zanyi da kai.....
Yayi murmushi tare da fadin baki da takaba, tunda bamuyi aure ba....
Ta danyi dariya tare da fadin
Ka bige sosai ko?
Ya dan gyara tafiya yace, eh bakomai ama
Ya kalli sarkar dake wuyan ta, ya tuna da yasan sarkar, dan Ahmad ya dade yana ajiyar ta dan boyeta ma yakeyi...
Shima garin bude buden sa ya gano ta...

Har gida ya rakata, sai da ya rakata yaga ashe da mota yake, nan ya shiga motar ya ware.
Lalle ahmad nason yarinyar nan, kuma itma tanason shi, so na hakika suke yi ma juna, toh shi yanzu ya zaiyi da wannan alamari, yaya wannan alamari zai kasance, yaya zai bullo wa da wannan alamari....???

Lalle dole ya nemi magani, dan gudun abun da zai iya faruwa nan gaba....

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt