Twenty three

137 11 0
                                    


Episode twenty three
WAYE SHI❓(shaffik ko Ahmad)

"Da sunnan allah mai rahama maijin kai
Ya ubangiji duk wanda ya karanta wannan litaffi nawa allah ka sama albarka da shi da ahalin sa baki daya ubangiji ka kiyaye shi daga dukanin wani sharri na shedan,aljanu da maqiya....
Amin ya rabbi samawati"
ㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡㅡ

Attahir ya ajiye cup din hannun sa yayi ajiyar zuciya, ya jinjina kai yace...
Fairy tail dinka yayi dadi sosai,ya fada tare da tafa masa hannun ,
tashi ka tafi ni yanzu wajen lawisa zani....

Shaffiq ya doka table din kamar zai mai hauka cikin zuciya, ya dago ya kalli  Attahir cikin jajayen idon sa da zuciyarsa ke tafarfasa yace...
Attahir zan maka karya, na taba zuwa na tsara maka labari irin wannan, ina kyautata zaton wanda ya hadu da lawisa ba ni bane Ahmad ne.
Wai kake kiran sa ahmad, shaffiq kai ba sunnan ka ahmad ba, ba sunnan dad din mummy ne da kai ba, ko ka mata sunnan ka ahmad....
Meyasa kake complicating kanka ne?

Attahir for God sake listen to me and understand the situation am in, wallahi da gske nake duk abun da nake fada maka, babu wanda ya sanni da Ahmad duk duniya idan ba mummy da kai da abba khalid da umman ku ba, da shaffiq nake amfani school dina throughout da shaffiq nayi using, ni kaina ina manta cewa sunana Ahmad, kai kan ka kana mantawa..,
Ko ba haka ba???
Attahir something is wrong...
Something is differently wrong....
Wasu zafafan hawaye suka zubo masa da yayi saurin sharewa....

Ganin situation din is worsts hakan yasa Attahir ya ce
Kaga cool down,
Wannan babar magana ce, ama ka sanar wa da mummy.....??
Ya share idon sa da tissue din da ke kan table din yace...
Bazan iya sanar da ita ba, hankalin ta ne kawai zai tashi, gwara kawai muje ayi masa ruqiya ya tafi in huta.......
Alright fine, akwai wani da abba ya san shi, yana zariya, yanzu zanje in tambayi abba labarin sa idan yana raye sai muje wajen sa gobe idan allah ya kaimu.....
Toh amma kar ka fada masa wannan please.
Alright fine....
Yanzu dai cool down please.
Har zai fita ya juyo yace
Kadai wannan yarinyar shi ta sani ba kai ba, shi yasa ta kira ka sa Ahmad
Ya gyada kai yace eh, taso kama shi, shi yasa yace mata ai mu yan biyu ne...
Yanzu a haka ta dauka mu yan biyu ne....
This situation is terrible....
*****************************************************
Washe gari da sassafe suka dau hanyar zariya, suna isa suka isa guri mallam Nata'ala,
Aka yi musu iso, basu dade ba mallan Nata'ala ya fito aka shifida musu buzu suka zauna.
Mallam Nata'ala yayi musu karba ta shinfidar fuska.
Nan shaffiq ya kwashe labari ya fadawa mallan Nata'ala...
Mallan ya bude qurani ya jero ayoyin alqurani mai girma bayan nan ya ja charbin mai dubu , sannan ya ta ya kara jeri wa shaffiq karatun alqurani.
Ya bude ruwa a jarka ya zuba a dan murfin ya karantawa shaffiq ayiyin tsari yace da Attahir ya matsa, ya watsa masa har sau uku, haka yayi tayi har wajen minti 30 ama shiru...

Mallam nata'ala ya kamala da yin hamdala ya kalli shaffiq yace,
Dan samari ka godewa allah...
Babu wani aljani da ke tare da kai, a tsarkake kake dan samari babu abun da zai doshi inda kake, ka cigaba da ibada kana kulla da addini ka...
Zancen abun da ka fada kuma ina kyautata zaton kokonto ne ke damun ka saboda haka, ka cigaba da addu'a, kana neman tsari.
Shaffiq yayi ajiyar zuciya yace toh nagode mallan allah ya saka da alheri, suka bada na sadaka sannan suka taso suka dau hanyar gero.
Zuciyar shaffiq cike da rudani, ya za'ayi ga abu na damun sa ace lafiyar sa kalau toh idan ba aljani a tare da shi to me ke damun shi???
Shima dai Attahir cike yake da nashi rudanin ama haka sukayi shiru kowa yana ji da abun da ke damun sa.
Suna isa gero suka wuce gidan shaffiq, suka zube kan kujera, shaffik ya mike yace zo muje kaga kayan da ya siya,
Suka haura sama, ba walwala a tare da su...
Suna hawa Attahir yaga yanda gidan yake a hargitse abun da shaffiq bazai taba yi ba kennan,
Juyawar da zaiyi yaga shaffiq na faman nukurkusu yana rike kai, idon sa yayi jajir kamar garwashi tsananin ciwo, chan sai duhu ya ziyarce shi sai kuma dufffff ya dauke....

Kamar kiftawar ido sai gashi ya mike, wani sabon mutun ya fito daga jikin shaffik, Attahir ya kalle shi cikin tsananin mamaki yace, kai meke damun ka lafiya....
Hada idon da sukayi yaga an sakar masa murmushi tare da fadi Attahir,,,,
Cikin tsananin farin cikin ganin Attahir din yasa ya mike yana mika yace, yaushe kazo ne....
A zabure Attahir ya matsa zuciyar sa na faman bugawa....
Murya na rawa yace....
Ahh....madddd.........
Yayi murmushi yace ashe zaka gane ni dama ina takaicin shaffiq din nan da kake kira na,

Ji yayi ya kasa tsayuwa, wannan wane irin sabon alamari ne???
Ya sami guri ya zauna da kyar dan zai ita faduwa...
Kayan sa ya hau neman kayan sa da ya siyo...
Inna wannan ya saka mun kaya na ne,yana yi yana mita....
Chan ya bude wata wardrobe yaga inda shaffiq ya cun kusa masa kayan sa, yayi tsaki ya juyo ya kalli Attahir tare da fadin dan allah ji yanda ya chunkusa mun kayana sababi yanxu idan shi nayi wa haka zai ji dadi...
Attahir dai tsananin mamaki, da mutuwar zaune da yayi ko uffan kasa cewa yayi, yana zaune yana kallon ikon allh dan yayi namijin kokari...
Sai da ya shirya tsafff cikin sababin kayan sa sannan yasa SIM card a sabuwar wayarsa ya kunna yaga tayi sannan yace, su je kasa yayi masa girki suci sannan su fita ya nuna masa gero dan yafi shaffiq sannin kan gero...

Hannun sa ya ja suka sauka kasa ya doea musu girki kala kala gidan ya gauraye da kanshin girki,
Tsananin mamaki Attahir ko motsi baya iya yi, shaffiq mutun ne wanda ko indomie bai iya dafawa ba bale wannan shagalin, shaffik ko kitchen baya shiga dan gudun girki da yake yi....
Innalillahi, waina illahi rajiun....
Meke damun dan uwansa SHAFFIQ KHALID

*****************************************************
To be continued  insha allah

Mai muku fatan alheri a koda yaushe
Hasna mansur nagoda (Bintnagz)

Make sure to vote 🗳
Comment
Like and share
Much love and stay blessed 🙏🏼

𝐖𝐀𝐘𝐄  𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ