RUDANI

4.1K 117 11
                                    

[2/2, 10:07 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫 🌞
Story
&
written by
Lashminzy

💥GÔLDÈÑ"S WRÎTÈRS_
_ÀSSÔÇÌÁTÎÒÑ_💥

Komai yayi farko zaiyi karshe Allah nagode maka daka nuna mun na kawo karshen littafina na RAYUWAR UMMIEY. Allah yasa kamar yadda naga farkon wannan littafin yasa naga karshen shi, Masoyana ina mika sakon godiyata zuwa gareku
🙏🙏🙏

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 1_2

mummy! mummy!!!Tun shigowarta take faman kwala wa mummynta kira, mummy dake cikin dakinta duk hankalinta ya tashi da jin irin kiran da Amatu_rahman keyimata da sauri ta fito tayi hanyar sauka palour

Cin karo sukayi da ita cikin tsoro da firgici mummy tace Amatu meke faru dake?? Fadawa jikinta tayi tace wallahi mummy naga Abdul a waje yanxu yanxu nan kuma ina son iyi mashi magana sai bata karasa fadar abunda zata fada ba sakamakon tsawar da mummy daka mata aikuwa da hanzarinta ta daga kanta data dora saman kirjinta

Tsuki mummy tayi tace amma dai Amatu kinyi asara yanxu akan wannan abun neh zakiyi ta faman kwala mun kira haka?? Ai na dauka ko wani abunne ya sameki Ashe akan wannan neh toh wallahi kibi a hankali karki zauce, tana gama fadar haka ta kara gaba

Kuka Amatu tasa gami da haurawa sama, dakinta ta shiga ta fada saman gado tana zubar da hawaye ta rasa dalilin dayasa ta kasa cire Abdul a ranta. Tana cikin kukan neh wayanta ya hau ruri

Dubawa tayi taga aunty hajara ce ke kiranta, ba bata lokaci ta amsa kiran daga bisani kuma ta tashi ta fita kodata fito palour mummy ta tarar sai data sanar da ita kafin ta wuce

Tafiyar minti biyar tayi se gata a cikin wani Dan karamin flat mekyau, kai tsaye ta shiga cikin gidan, a palour ta tarar da aunty hajara tana cin abinci kallonta tayi tace Amatu lafiya naganki a haka?

Dan jimmm kadan tayi sannan tace aunty yauma na sake ganin Abdul a banki amma kafin inyi mashi magana harya wuce shine dana fadawa mummy ta fara yimun fada

Ohhhh Allah me iko gaskiya Amatu ya kamata ace kin rabu da Abdul hakanan kusan shekara biyu kenan babu labarinshi kuma ma idan yana sonki ai duk inda yaje ze iya nemanki amma kawai kinsawa ranki damuwa kila ma yayi aure ya manta dake

Saurin isowa wurin aunty hajara tayi ta rufe mata baki da hannuwanta tace Allah aunty Abdul beyi aure ba saboda yayi mun alkawarin baze taba auran wata ya' mace idan bani ba kum.........

Dakatar da ita aunty hajara tayi tace anya baki fara tabuwa ba kuwa ko an fadamaki kowani dan Adam neh keda tabbaci?? Nidai shawarata kawai ki manta dashi ko kya hutawa ranki

Badan ta gamsu da maganar tata ba tace toh, zama tayi suka faracin abincin tare, bayan sun gama neh Aunty hajara tace tazo ta tayata gyara dakin baki kanwarta ameera ceh zatazo

Ba karamin dadi Amatu taji ba tace aunty bari inyi sallah inzo

Daga nan ta shige toilet tayi alawla tayi sallah bayan ta fito neh ta tarar da aunty harta fara kakkabe dakin. Hira suka shigayi inda aunty ke bata labarin ameerah duk da cewar Amatu ta Santa amma bata taba ganinta ba sai a hoto shiyasa take zumudin ganinta

Suna cikin aikin neh sai ga mijin aunty hajara yazo, gaishe shi Amatu tayi taci gaba da aikinta aunty kuma jan mijinta tayi zuwa dakinshi.

Bayan ta dawo neh sukaci gaba da aikinsu basu suka gama ba sai kusan magariba, suna gamawa Amatu tayiwa aunty sallama ta wuce

Tafiya take a nutse cikin kwanciyar hankali nan kuwa ba'asan tunani neh fal cikin ranta ba

Tunanin maganar da aunty hajara ta fadamata takeyi na cewar datayi kila ma ya manta da ita tana cikin haka neh taji an damkota da karfi ansa cikin mota, zata kurma ihu kenan taji an....................

RUDANIWhere stories live. Discover now