RUDANI

1K 32 1
                                    

[2/16, 4:59 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

I love u so much ummu arpat, ngd da irin soyayyar da kike nuna mun amma karki manta nima fah ina kaunarki din kuma ina yinki 💯💘

     Page 41-42

Kwalla ce ta zubo mata kafin ta share tace "bayan na koma gida washe gari gobara ta tashi a gidan mu a lokacin kuma nida maryam kanwata munje gidan halima matar kawunmu, toh muna can ne mukaji labarin gobara ta kama a gidan mu.

Kuma duk mutanen gari sun aza harda mu dan tunda mukaji labarin haka bamu dawo ba sai mukayi zaman mu can daman kuma kawunmu kadai muke dashi shiyasa bayan wannan gobarar bamu dawo ba.

Bayan sati d'aya da faruwar haka sai kawu bala wato mahaifin halima yace ni tunda mijina na nan kuma ga abunda ya samemu inyi mishi kwatancan garinsu yaje ya sameshi dan a mayar da auren mu. "batare da nayi wata jayayya ba na amince saboda ko nan da muke zama ba wani dadi mukeji ba danshi ma baida hali sosai.

Bayan yaje garin ya dawo ne yake fada mana wai kun samu gobara kuma duk kun rasu wasu kuma sukace kabar gari. Daga nan nikuma na shiga damuwa, nayi kuka harna gaji daga karshe na dangana ga Allah.

Bayan wasu lokaci da faruwar haka ne Allah ya hadani da Ibrahim waton mijina na yanzu, a lokacin ina yin panke ina kaiwa wani shago ana siyarwa sai Allah ya hadani dashi kuma tun daga lokacin daya bayyana mun yana sona na amince. Ba'a dauki lokaci me tsawo ba aka daura mana aure inda yace maryam ta dawo gidan mu da zama, dan yana da hali sosai dan ko lokacin bikin mu ya dauki nauyin abubuwa da dama.

Haka rayuwar mu ta kasance inda muka dawo nan abuja da zama dan nan yake aiki, maryam kuma yasata a makaranta taci gaba da karatu nikuma yana kula dani yadda ya kamata. Abdulraheem kuma ko sau daya be taba nuna mashi bashi ya haifeshi ba dan haryanzu Abdulraheem besan Ibrahim bashi ya haife shi ba sai yanxu da wannan al'amarin ya faru.

Ajiyar zuciya ta sauke tace Aliyu kaji yadda akayi muka tsira. Hamdala yayi ya kalli Abdulraheem yace dana zo kusa mana. A hankali Abdulraheem ya tako har zuwa inda yake ya zauna.

Abba yace toh alhamdulillah munji dadi da Allah ya bayyana wannan lamarin, yanxu sai kowa ya gode ma Allah. Daddyn Amatu yace kwarai kuwa ai yanzu matsalar data kunno yanzu zamu kasheta tunda abun ya zama haka.

Daddyn Abdulraheem yace eh kwarai kuwa amma yanxu wannan ya rage a tsakanin su tunda yan uwan juna ne yanzu sai daya yabar ma daya ko??

Gaban su ya fadi rassss a tare suka juyo suna kallon juna. "Cikin zuciyar  abdulraheem ko cewa yake lallai akwai chakwaki, amma nifa bazan taba bar mashi ita ba. Abdulrahman kuma dadi yakeji dan yasan duk yadda za'ayi shi za'a barma Amatu.

Suna cikin zancen zucin su mummy ta katse su ta hanyar marairaicewa tana kallon ammie tace Aisha nasan cewa kina bukar duka ya'yanki a kusa dake amma dan Allah kiyi mun alfarma kibar Abdulrahman a wurina saboda na shaku dashi banason yayi nesa dani Dan Allah...... Ammie ta katse ta tace haba ke kuwa ai bazan rabaki dashi ba tunda haihuwar shi kawai nayi amma ke kika kula dashi tuna yana karami har zuwa girmanshi kinga ai kema danki ne dan haka kici gaba da zama dashi kuma kici gaba da bashi matsayin shi na danki.

Murmushin jindadi mummy tayi ta karaso wurin ammie tana zuba mata godiya dan ba karamin dadi taji ba. Saboda ko ya'yan data haifa bata musu irin sonda takewa Abdulrahman ba" wani sa'in samha har kuka take tana shagwaba wai mummy tafi son Abdul.

RUDANIWhere stories live. Discover now