✍🏽ŧყקıŋɠ............
💸💵SAI NAYI KUDI💸💵
_Story and written_
ɮʏ
๓A๓eeʙし㉫Ŵ 💙Wattpad👉Mamyblew2
*✍🏿ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*
I ɖօռ't ʝʊst sċʀɨɮɮʟɛ tօ ɛռtɛʀtaɨռ aռɖ ɛɖʊċatɛ ɮʊt aʟsօ tօʊċɦ tɦɛ ʀɛaɖɛʀs ɦɛaʀt
_Deɖɨċatɛɖ to ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION_THANK YOU SO MUCH FOR YOUR GAINSTAY KUNA RAINA😘
'''Chapter 2'''
Washe gari muka tafi gidan sirrin Alhaji Faisal Tanko,gidane babba dauke da sashi babba guda daya babu stairway amma zai kai plot3 ,ba mai gadi a gidan balle tanan side din gateman,da kuma Parking space achan gefe na motoci guda 3 kachal saboda baki basau yawan zuwa gidan sae abokan aikin shi suma ba kullum suke zuwa ba akwai lokacin haduwan su,twice in a week every sunday and thursday.
"Toh malam Mato ya kaga gida ya hadu ko" Alhaji tanko ne mae magana tare da duban inda Mato yake."Gsky Ranka ya dade gida yayi"
"Toh madallah,mu shiga ko" inji Alhaji tare da nunawa mato kofan gaba wanda zata sadasu cikin parlour direct.
Palo ne babba dauke da kujeru set biyu,baki da red,bakin yana hannun da'ma jan kuma yana hannun hagu, a'tsakiyan parlour kuma between d two set sofa's babban center table ne black and red dauke da babban flower vase chan bangon tsakiyan kuma babban plasma ne meh dauke da tv stand black da zanen star ja,gefen tv kuma flower ne a vase bayan plasman wato bangon an kawatashi ne da wallpaper red da zanen toy (baby)🤦♀sae kace dakin yara,komai dae na palo is unique saf yake.Waiwayo wa mato ya fara yi yana raya a rashin
"Gaskiya gidan nan ya hadu sae kace Aljannah dunya huhuhu,yasiin ina zama kudi zan gina wanda yafi wannan komae na daban yake da na sauran Alhazawan,😼yanzu inba rainin hankalin Alhj ba kenan nan gidan aiki ne ikon Allah"Katse mishi tunani Alhaji faisal yayi tare da cewa
"Yauwa mato mu wuce ciki ko in nuna maka masaukin ka sannan ka kintse""Toh Alhaji amma inada tambaya"
Ajiyar zuciya Alhaji yayi sannan yace
"Kai mato ka fiye tambaya wlhy,ka bari mana i'dan ka gama kintse wa sae na warware maka duk abinda ya daure mah ka"Bai sa k cen komai ba kawae kallon shi tare da shiga kofa da Alhaji ya shiga wani virenda ne kamar ginin hotel dauke da dakun kuna guda 6,na shidan yasa key ya bude musu sannan suka shiga ciki.
Dakine babba dauke da babban set din Italian da katon royal bed,da babban wardrobe sannan 42inches plasma gefe daya kuma toilet ne babba akwae komai wanda dan adam zaiyi amfani da shi cikin toilet dangin su brush,sabulun wanka d.s."Toh mato nan shine dakin ka akwae kaya acikin wardrobe sae ka dauki duk wanda yayi maka,tun kafin xuwan ka garin kano nasa Auwalu ya siya maka su"
"Toh Alhaji godiya nake"
Batare da ya amsa ba ya fita daga dakin yaja mishi kofan,shikuwa mato jikin shi ya gama mutuwa yana rayawa ah ranshi
"toh taya Alhaji yasan cewa zanxo garin kano da har zae siyamin kaya kin sawa sannan kuma waye wannan Auwalu hmmm toh ni ina ruwana ba kudi nakeso ba"
Yana gama tsake tsaken shi ya wuce toilet yayi wanka sannan yazo ya bude wardrobe kayane zasu kai set 100 shi kanshi yana mamakin yanayin kayan dan bai taba mallaki kaya ko set 5 na kanshi ba,ba kallan da babu dangin su jeans ne,getzner,shadda ,jallabiya komae dae komae dae wanda yake cikin kayan maza akwae su boxes da vest mah zasu kae ashirin2. Shi dae mato ganin su kawae yake kafin ya zare wata jallabiya brown ya sanya yakai minti 5 a wajen,ba tareda yasan wanda yake magana baisan inda muryan ta fiti ba tana cewa,"karka saka jallabiya Alhaji yace akwai bakin da zakuyi kuma yau lahadi ka bude chan kasan gadon zakaga wani ja da bakin shadda ka sanyashi turaren kuma ka fesa black (for men),sannan hulan ka sanya dinkin yan kauyen (Bama) kauyen da ke garin maiduguri
Diffff😳naji zuciyan mato ya fadi yace
"Kutt zan iya aikin nan kuwa""Zaka iya mana mato karka damu kaji"wata murya ya sake ji chan kasan gado😨
kafin kace meh mato yayi fitsari awajen da yake tsaye,tare da tambayen waye ne bakin shi na rawa
"Danallah k wacece ki fiti in ganki mana""Hahhaha mato kenan ba kace duk wani irin aiki zaka iya ae karka damu zaka ganni amma ba yanzu ba ,kai dae ka shirya kafin Alhaji ya gaji, dan kai suke jira ah parlour"
"Toh toh Hajiya Amma taya kikasan ni suke jira bayan nasan bai shigo nan ba"
"Hahhaha mato kenan ka duba chan gefen ka"
Juyawa mato yayi ya duba gani yae Alhaji da wasu mutane guda 4 sanye suke cikin iri kayan da ta gaya mishi ya saka,kafin yace meh bat sun bace😆tsuma ne kawae mato baiyi ba."Toh ka gansu ko mato,bari na tayaka ka shiryawa kafin su gaji"
"No ki barshi kawai Hajiya wlhy zan iya da kaina"agurguje ya gama shirrin shi sannan ya sanya takalman shi ya nufi kofa sae dae kashh kofan arufe ta k.
Chan kasa ya sa k chin muryanta ta"Yauwa mato kayi kyau bari na bude mah kofan"kafin ya bata amsa gani yae kofan ta budu da kanta,ba tareda tunanin komai ba mato yasa kai ya fita.
Yana fita daga dakin ya kasa gane kofan da suka shiga shida Alhj dazu haka yake tsaye kamar statue🕴,sae kawai gani yae wata kofa ta budu da kanta,ba tare da tunanin komai ba ya fita,yana fita yaci karo dasu alhaji da sauran yan aikin shi su 4 ,suna tattaunawa akan aikin su.
Gurin xama Alhaji faisal ya nuna mishi tare da gyara murya da gabatar mishi da abokan aikin nashi..#Comment
#Vote
#ShareMARYAM ABDULRAHMAN💙