WATA SABUWA-32

1.8K 176 52
                                    



Da k'arfi yarinyar ke aikinta, yayinda da ta tuno maganarta da maigidan sai tai murmushi, duk sai ta dad'a k'amewa saboda ta kauda duk wani zargi agun matansa har burinta ya cika. Shi'isa tama daina fitowa idan har ramadan yana nan, hakan ya sanya lad'ifa hankalinta ya d'an kwanta. Wanda ita laila takanta take dan cikin na d'an bata wahala, shiisa duk ta ma kasa ankarewa da wasu abubuwan.

Wanda ba su san cewa ramadan ya kan bi yarinyar da daddare ba yayi hira a ita duk da ba ya tab'a ta, duk da cewa tarin sha'awar yarinyar yakai mai intaha. Wanda yake ji kamar ya afkawa yarinyar musamman da shed'an ke gefe yana dad'a k'awata masa hansatu, amma kuma yakanji tsoron yin hakan , duk da cewa Allah ya halitto shi acikin mazaje masu yawan buk'ata sosai! Sai kuma ya tsani zina, masu yi ma addua ya ke musu. Ya gwammace ace yayi ta aure akan ya yi zina. Sosai ya ke k'ok'arin a wajen nan. Musamman yakan tuno wani zamani da ya wuce. Tun yana mai farkon shekaru.

Hajiyarsa kan ba shi labari kala-kala akan illolin zina da dangoginta. Wanda ita bibiya ta ke, idan ka yi sai anwa na ka, kullum nasiharta ya nesanci zina ya katange idanuwansa da kallon haram! Ya ji tsoron Allah aduk yanayin da ya samu kansa. Koda ace shaid'an na rinjayarsa ya yawaita ambaton Allah a zuciyarsa aduk yayinda ya ga wani abunda yake rinjayarsa. Wanda wannan nasihar ce yake yawan tunowa, saboda hajiyarsa ba ta gushewa wajen tunatar da shi a kullum, sai kuma Allah ya halicce shi cikin maza mabuk'ata . bai sani ba ko mahaifiyar tasa ta gano irin halittar tasa, ya sanya take mai yawan nasihar. Shi dai bai sani ba. Yasan dai yana amfani da nasihar sosai. Yasha wahala sosai akan hakan. Tabbas ya san adduar mahaifiyarsa ke bibiyarsa da shi kansa da yake yi, kan Allah ya kare shi da aikata zina, ba zai so yayi abinda za a zo aiwa yaransa ba, sannan uwa uba mahaliccinsa da yayi hani da haka.

Amma muddin ya ga yarinyar sha'awarta ke damaimaye shi, bai san sanda yake rik'e  hannunta ba akullum idan ya silala d'akinta ba. Har alokacin bai tab'a cewa yana sonta ba, sai dai yakance za ta aure shi,Wanda alokacin ita tai zurfin cikin kaunar Abu fuad.

(to fah ayi dai mu gani hansatu)

Al'amura haka sukai ta gudana suna tafiya ciki harda fara nak'udar laila atsaitsaye.

Wanda alokacin kuma mari ta zo tafiya da hansatu, dan za ai bikin d'an uwan hansatun na dangi. Babu wanda yakai ladifa jin dad'i, saboda tasan ko babu komai ramadan zai daina wannan satar kallon, dan ita gwanda ace ya aureta da ya dinga wannan kalar kallon, ta b'angaren laila kuwa ba ta so ba. Haka ba, saboda yanzu ayyuka zai dad'a tarar mata, ramadan ma bai so ba ,haka ta bukataci a bata kud'in aikin ita hansatun na iya watan da tai, nan aka ba ta suka tafi k'auyensu.

Tafiyar hansatu da kwana uku laila ta fara nak'uda.  Zaune ladifa ta ke a falon k'asa misalin sha-biyu Na rana tana bawa Fuad custard yana sha, sai ga laila ta fito tana dafe baya. Lad'ifa ta ce da sauri "jikinne?."

Laila ta kasa amsawa sai matse fuska take. Ganin hakan ya sanya taiwa ramadan waya kan laila ba ta da lafiya.

Babu dad'ewa ya zo. Lad'ifa ta goya fuad suka tafi asibitin. Haka aka sha gurmuzu, da kamar lailar ma ba za ta iya haifuwa da kanta ba, ana shirin yi mata aiiki sai kuma gashi ta haihu inda ta samu baby girl.

Murna suke sosai. Ba a salllameta ba sai washegari  suka tafi gida, inda ita iyayenta suka ce ta zauna agidanta za wanka.
  Ramadan sai hidima ya ke, sosai yake farin cikin samun babyn wadda suke d'an yanayi da fuad saboda kamanin Ramadan d'in da ta d'auko. Sai dai fuad ya fita kyau sosai da haske.

Sai wata 'yar uwar baban laila tazo ta zauna mata wankan jego. Suna zaune a d'akinta anaiwa baby wanka, ladifa ta shiga ta zauna ta ce "kai wai wannan babyn dawa take kama ne?."

NA YI GUDUN GARA-2019✅Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt