41_50

1.4K 82 1
                                    

Duk dakin akayi shiru aka xuba mata ido cike da
mamaki, ganin haka yasa ta qara fashewa da
kuka ta girgixa kanta ta qarasa gurin momy dake
tsaye ta riqo qafafuwanta tana wani irin kuka mai
narkar da xuciyar mai sauraro nan da nan jikin
momy nayi sanyi,
umma ta dubeta cike da mamaki
tace hamida har ynxu ban gane inda kika dosa ba
inaji kin daukomune dan mudaba marar lfy ko?
Hamida ta dago manyan idanuwanta dana rine
xuwa ja tana kallon mahaifiyarta
tace harda auren hassan umma, yana sona yana
son halaka kansa saboda ni dan Allah ku
tausayamasa,
nan da nan ran umma na baci ta murtuqe fuska
cike da takaici ta fisgota daga tsugunne datake
itama hamida ta tsorata da ganin yanayin da
umman nata take ciki
[4:54PM, 11/30/2015] pherty: Mekike fada ne
hamida qara maimaitawa inji inajin kunnuwana
basuji da kyau bane,
hamida ta tsorata ta xare idanuwanta tana
kallonta tana girgixa kanta cike da tsoro,
42
umman ta sake saura qiris ta fadi ta juya ga
kawun hamida
tace bn amince da wannan auren ba ban yarda
hamida ta auri mutanen da basu da kirki basu da
tausayiba,
lokaci daya xuciyar momy da hussien ta buga duk
suka dubeta a raxane,
umma tacigaba da fadin hamida ya'ta ce jinina
ce ban yarda ta auri ko daya daga cikinsuba
saboda mahaifiyarsu batada mutunci tunda har ta
iya toxartamu ta wulaqantamu saboda Allah bai
bamu ba, hakama ya'yanta..........hussien
ya katseta da hanxarinsa,
yace umma kimin adalci kinfi kowa sanin yanda
nakeson hamida, wlhy ina sonta dalilinta nadaina
aikata duk wani abu marar kyau, sannan
mahaifiyarmu bai kamata ki jefeta da wannan
kalamaiba idan kikayi la'akari da irin halaccin
datayi maki a rayuwa bawai gori nake maki ba,
43
mai gari yayi gyaran murya kafin
yace Asmau(umma) ba iko xn maki ba abinda na
fahimta anan duk su biyu suna sonta kibarta ta
auri wancan da baida lfy ina ganin hakan shine
dai dai,
umma ta girgixa kanta cikin tashin hankali
tace bana son hamida ta auri hassan nafi yimata
sha'awar hussien shine yafi sanin darajarta shi
nakeson ta aura,
wasu xafaffun hawaye suka xubowa hamida
bawai batason hussien bane tana sonsa amma
xuciyarta tafi rinjaye akan hassan din,
ahankali taja qafafuwanta daga dakin ta fita tana
fitowa ta tsinkayo Dr.merah na fitowa theater
yana tafe yana xare handgloves cikin isa da
qasaita ga fadawa birjik a asibitin, guards dinsa
suna biye dashi a baya,
yana tafe yana yatsina fuska ma'aikatan asibiti
sai xubewa suke suna gaisuwa nurses da likitoci
sai dai ba wanda ya kula ballantana ya amsa,
cak suka ga ya tsaya harabar asibitin suna ganin
haka fadawan da guards suka san akwai matsala
tabbas akwai abinda ya fadi daga hannunsa
daman hakane duk abinda ya fadi hannunsa baxai
taba magana ko ya nunaba sai dai ya tsaya
masu more masa baya suje su duba ,
haka kuwa akayi da yawa suka juya suga ko
menene ya fadi suna isa cikin asibitin suka sami
turban dinsa ne har wata nurse ta dauka xata
kawo masa da sauri suka karba suka fito ,
hamida na tsaye na kallon sarauta wannan tor
dame yake taqama MULKI KO SARAUTA?
tana kallo aka bude masa mota ya jima tsaye
kafin acire masa labcoat din jikinsa aka musanya
masa da alkyabba suka nada masa turban dinsa
kana ya shiga motar sukajata ahankali kamar
masu tfy a hanya,
kusan motoci biyar suka morama motarsa baya
suka fice, ta sauke ajiyar xuciya ta tuna cikin lbr
da aka bata
akwai wani lokaci da sarki merah ya sauka daga
sarautarsa aka nada Aiman, saboda tsabar
sarauta da ji da kai a daren ranar yana tare da
mai dakinsa Affiya xasuje
[4:59PM, 11/30/2015] pherty: Lambu,
kunama ta cijesa a dan yatsan qafansa, amma
saboda qarfin mulkinsa bai fada ba ko raxana ko
wata alama da xai nuna illah tsayuwa da yayi
cak a xaton fadawan ya yarda wani abinne sai
suka shiga dube dube anan suka ci karo da
qatuwar kunama dai dai inda yake tsaye nan take
suka kasheta hankalinsu a tashe suka juya suna
kallonsa yana tsaye inbanda xufa ba abinda yake,
44
iya rudewa affiya ta rude ta rungumosa tana
tambayarsa inda kunamar ta cijesa amma yaqi ya
fada hassalima dauke dubansa yayi daga garesu,
fadawan cikin rudani suka xube qasa suna
roqansa ya fadamasu amma fafur yaqi tankawa
saboda gani yake idan ya nuna rakinsa tabbas
girmansa dana sarautarsa ya fadi,
Affiya nan take ta fashe masa da kuka ganin
kunama ce fa ta cijesa ta juya xatabar lambun
sai ya riqo hannunta yasa dayan hannunsa ya
xare space din idanun sa da idanu yayi masu
alama da yatsantsa......
Cabdi wani mulkin,sarauta da qasaita sai kun
duba littafin MULKI KO SARAUTA?shima littafin
fertymerh xarah ne.
kukan salma ya dawo da hamida daga xurfin
tunanin da take, sai a lokacin ta tuna halin da
take ciki tadawo da kallonta ga salma idanunta
sunyi rau rau ta koma cikin asibitin gab da xata
shiga dakin taji muryar momy cikin kuka tana
fadin
abar hamida ta auri hassan, hussien xai iya
haqura da hamida amma batasan ya rayuwar
hassan dinta xata kasance ba idan ba hamida,
umma tace nafison hussien akan hassan, nafi
ganin girmansa mutuncinsa tarbiyarsa sosai akan
hassan saboda haka na xabawa yarinyata hussien
ta aura,
ta juya a raunane tana kallon limamin idanunta
taf da hawaye
tace ga wakilin hamida shine kawunta tunda baa
sanarda yan uwan hussien ba inaso mai gari ya
xamo wakilinsa a daura auren hermyderh da
hussein yanxu ba sai anjima ba tunda TAGWAYEN
MAXA baxasu auri hamida dukkansuba dole
dayane xai xamo mijinta kuma hussien,
nan take hamida na xube da gwiwoyinta qasa
tana rusa kuka mai tsananin gaske.
Hausa novel
16 December 2015 at 08:05 路 fertymer
[4:39pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [4:57PM, 12/22/2015] Pherty: 45
TAGWAYEN MAXA
Na ferty xarah
A raunane hussien ya matsa yana kallon hassan
da har lokacin bai farfadoba,
yana tausayin dan uwansa yana son dan uwansa
kuma komai xai iya akan dan uwansa,
tabbas yafison rayuwar dan uwansa akan hamida,
mace baxata taba xama sillar rabuwar
xumuncinsuba,
yau gashi duk kudinsu kyawunsu da ajinsu suna
neman rasa abu a duniya, komai na hassan
nashine, kuma komai nashi na hassan ne tor idan
hakane dan me baxai iya barwa dan uwansa
jininsa abinda yake soba,
ya rumtse idanunsa yanason hamida tamkar
ransa kuma yaxama wajibi yabarwa hassan
shikuma ya karbi salma a matsayin matarsa,
ya girgixa kansa yana hawaye ya kalli umma
yana share hawayen fuskarsa sai kuma ya juya
yana kallon liman kafin yajashi gefe sukayi wata
magana batare da kowa yajiyosuba kana hussien
ya dubesu
yace xaije ya dauko uncle dinsu dole shi xai xama
wakilinsa saboda shine ubansu a yanxu,
ya juya ya fice yana fitowa yaci karo da hamida
tsugunne a gefe kallo daya yayi mata ya dauke
dubansa gareta tana ganinsa ta taso da sauri ta
taryesa, ya murtuqe fuskarsa, hakan yasa jikinta
yayi sanyi ta langabar da kanta tana hawaye,
tace nasan tunaninka xai baka cewa bana sonka
wlhy ina sonka hussien, tausayin hassan da
kasancewarsa dan u.... Ya katseta ta hanyar
daga mata hannu
yace qaryane hamida qarya kike kice kina sona,
maganarki ba gsky bace duk hasashe ce ba tun
yau nake ganin soyayyar hassan atare dake ba
idanuna na kanki hamida, kada kidamu hassan
din da kikeso xaki samesa sannan duk wata
kulawa da damuwa da kika nuna akaina nagode
ya juya ya fice ransa a bace tabisa da kallo cike
da tashin hankali da rashin fahimtarta da baiyiba,
46
kusan minti talatin da fitarsa sai gashi tare da
iyayensa maxa kusan uku sun shigo asibitin kai
tsaye aka nufi dakin da hassan k kwance,
sun raxana da halin da suka sami hassan dan
basuda lbr hr sun juya xasu rufe momy da fada
ganin suna raye Dan' yayansu yana neman rasa
rayuwarsa basuda labari yasa momy tayi saurin
katsesu muryarta a sarqe tana kuka ta koro masu
bayanin komai
[11:18AM, 12/1/2015] Pherty: Nan da nan iyayen
maxa suka juyo da kallonsu ga umma suka dubi
hassan matsayinsa kudinsa kyawunsa da ajinsa
amma ace shine ya koma hakan saboda mace
macen ma yar talakawa to menene amfaninsu a
duniya idan baxasu iya samawa TAGWAYEN
MAXA abinda suke so ba,
amma abin tambaya da mamaki anan yanda duka
xaratan maxan suka kafe akan mace daya kuma
kowane daga cikinsu na buqatarta duk da basuga
yarinyar ba, sannan basajin ta ummanta saboda
sunada kudin da xasu nuna mata FIN QARFI akan
yarta(chabdi)
hussien ya katse tunaninsu xuciyarsa a raunane
yace a daura auren amma duka iyayen mata su
fita daga dakin,
47
uncle ya katsesa yace wane irin daurin aure ne
wannan hussien sai kace bakuda gata a duniya,
wane irin aurene xaa daura a asibiti kamar wasu
marar galihu, bamu yarda da wannan daurin
aurenba,
tabbas kamar yanda duniya tasan da mahaifinku
kafin ya rasu tasan da xaman kyawawan maxa
kamarku dole sai kowa yasani kuma ya shaida
auren TAGWAYEN MAXA a doron qasar nan,
bamai gari ba hatta liman da kawu sai da jikinsu
na dauki rawa wato abin na manya ne,
uncle ya cigaba da fadin kuma xaa cigaba da biki
baxaa dakatar ba saboda munada tabbacin
yaronmu yana raye da ixinin Allah kuma xai tashi,
Alhaji jafar da Alhaji ismail sukayi murmushin jin
dadi lokaci daya kafin su fita a tare uncle na bi
bayansu,
umma jikinta a sanyaye takalli kawun hamida
tace kada ka manta hussien na bawa hamida
dashi nakeson tayi rayuwa,
kawu ya gyada kansa kawai suka fita gabaki
daya hussien ya juyo yakalli dan uwansa har
lokacin baisan abinda ke faruwa ba ya girgixa
kansa kawai yana hawaye ya juya ya fice
[11:26AM, 12/1/2015] Pherty: Gidajen radio, t.v,
jaridu e.t.c aka shiga yadawa da sanarda daurin
auren TAGWAYEN MAXA,
hassan da hussien, cikin mintunan da basu wuce
arba'in ba qatoton harabar gidan
Alhaji jafar ya cika da mutane iri iri kala kala
tundaga yan uwa, abokan arxiki, qawaye ba
wanda bai hallara ba, nan take aka daura auren
HUSSIEN DA SALMA, HASSAN DA HERMYDERH,
wanda hussien ne ya nemi wannan alfarma ,
48
An dade ana kacaniyar daurin auren kafin su
qaraso asibitin hr lokacin matan basu san ya
daurin auren ya kasance ba illah hankalinsu dake
tashe saboda farfadowan hassan yana aman jini,
Dr.merah naganin yanayinsa yasa aka shiga dashi
emergency da gaggawa, yana tafe da sauri ana
cire masa alkyabar jikinsa tunda baxai iya cirewa
dakansa ba dole sai ancire masa saboda girman
qasaitarsa,
gab da xai shiga dakin emergency suka gama
sanya masa labcoat dinsa suka bude masa qofar
ya shige duk suka tsaya a waje suna jiransa,
hankalinsu a tashe sunyi tsaye cirko cirko ko
wane xuciyarsa bugawa take kamar xata bullo
qirjinsa tafito,
da sauri duk suka juya suka bar asibitin suka nufi
masallaci, arwallah sukayi suka shiga domin kai
buqatarsu da kukansu ga ubangiji talikai,
Allah ka biya mana buqatanmu ya rabbi!, awa
biyar cur suka dauka kafin su sami numfashinsa
ya dawo dai dai Alhmddlh komai ya dai daita sai
dai yasami barci,
kai tsaye aka nufi aminity dashi qafafuwansa duk
daure da bandage, ganin komai ya lafa yasa mai
gari ya tarasu duka yayi mgn da tattausan lafaxi
tareda bawa kowa haquri akan yanda auren ya
kasance dan shima a ganinsa hakan yayi dai dai,
umma kamar ta hadiye xuciya taji, wuf ta tashi ta
fice daga asibitin ta nufi ingawa,
salma kuwa dadi kamar ta mutu dama batada
gwani aciki kowanensu tana so, yayinda fargaba
tasa hamida a gaba jikinta sai faman rawa yake
har wani xaxxabi takeji ganin ummanta batayi
maraba da auren ba.
49
Sati biyu jikin hassan ya soma sauqi sai dai har
lokacin daga kallo bai furta ko wacce kalma ba
hassalima baisan meke faruwa ba illah ya tsani
kowa a asibitin ba kamar momynsa da hamida ba
wanda yake ganin ta dalilinsu ya tsinci kansa a
wannan halin,
ganin samuwar sauqinsa yasa Alhaji jafar da
Alhaji ismail suka tada mgnr bikin aure ,
anata shirye shiryen biki anyi biki kala kala
ankashe naira,
ranar da xaa kai amaren xuwa gidajensu uncle
yayiwa hassan bayanin komai sai dai ga
mamakinsa hassan bai nuna wata alama tajin
dadi ko rashinsa ba illah lumshe idanuwansa da
yayi kawai,
daren ranar da xaa kaisu ake dinner taro yayi
taro a qaton hotel din kaya iri daya amaren suka
sa wanda uncle yayi masu kayan biki
shikuma Alhaji jafar ya gina masu qatoton gidaje
guda biyu komai iri daya ciki da waje hatta kayan
dake ciki duk iri dayane sai banbancin kala wanda
anan ra'ayinsu ya banbanta,
gidajen suna kallon juna basuda tserayya mutane
har xuwa kallon tagwayen gidajen ake masu
matuqar kyau da tsari,
Alhaji ismail shi ya dauki nauyin auren tun daga
kan sadaki,lefe kayan aure da sauransu duk shi
yayo odarsu a waje,
taro yayi taro suna xaune su uku sun sanya
hussien a tsakiya duk acikinsu salma ce kawai k
farinciki yayinda xuciyar hussien a dagule take na
rashin dan uwansa a kusa dashi ana hidimar ba
hassan,
hamida ajima ajima take sharar kwallah
musamman idan ta daga kanta ta dubi hussien
da tashi amaryar ita kuma banata angon bugu da
qarima ance baxai iya tfy ba,
ta fashe da wani matsinancin kuka dai dai lokacin
taji wurin ya dauki shiru lokaci daya taga hussien
ya miqe tsaye tare da salma,
sai ta janye hannunta daga fuskarta itama ta
miqe ta maida kallonta dai dai inda taga jamaa
na kallo,
yana tsaye kishingide a mota hannunsa riqe da
sanda irinta masu mulki idanunsa boye acikin
dark space ya xare madubin fuskarsa ba yabo ba
fallasa,
hussien ya isa wurinsa da sauri yana dariya ya
rungumesa yayinda hamida ta rasa yanda xatayi
lokaci daya tasaki kuka da dariyar farinciki.
Hausa novel
[5:00PM, 12/22/2015] Pherty: [5:09PM,
12/12/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
A hankali ya dauke dubansa gabhamida yamaida
kallonsa ga hussien dake rungume dashi
hussien ma kallonsa yakeyi
yace hassan meke damun kane meyasa kake bata
rai, yau ranar farinciki ce kasami lfy kuma hamida
ta xama matarka
hassan ya bata fuska yana yatsinata
yace ashe dakai xaa hada baki aci amanata
hussien ya saki baki cike da mamaki
yace ban fahimci inda ka dosa ba
[5:27PM, 12/12/2015] Pherty: yace meyasa aka
aura min hamida, meyasa aka bani ita bayan
ance bnda mutunci bnda tarbiya bata dace dani
ba,( hawaye fal a xuciyarsa ya nuna qirjinsa da
dan yatsansa)yana fadin
ni ake wulaqantawa akan mace, macen ma yar
talakawa wadda nafita da komai, ni ake
gorantawa tarbiya ake cimin fuska dan kawai
nace ina son yar aiki, tor na fasa bana.......huss
ien yayi saurin toshe masa baki cike da bacin rai
idanunsa sunyi jawur yake kallonsa,
tun kafin yayi mgn hassan ya janye hannunsa
daga bakinsa a fusace cikin tsawa yace kabarni
nayi magana ina ruwanka dani ne?
cikin fusata hussien yace na barka kayi magana
ka fadi duk abinda kakeso ka fada, ka toxarta
aurenka a idon jamaa, ka nunawa duniya cewa
dole akama ba raayinka bane.....

TAGWAYEN MAZAWhere stories live. Discover now