Page30

1.6K 131 9
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA*
       _(hattara yan mata)_

    *Whatpadd @xinnee_smart1*

*Page.... 30*
A zaune yasameta ta zuba tagumi,, ta bayanta ya zagaya had'i da kwantar da kansa kan kafad'arta, wanda hakan yasa ta farga dashi,

    d'an murmushi tayi zata tashi, ya mai data.

Ina zakije? Ya fad'a cikin muryarsa mai rud'ar da tunaninta.   a sanyaye tace, serving d'inka zanyi...

   Fuskarsa yagoga a gefen nata, wani yarrrrrr... taji a Jikinta, bata gama dawowa daidai ba taji wani sabon salon,harshensa yasaka a kunninta yana karkad'awa,

    dasauri ta dam'ki kujerar da take Kai had'i da sakin siririyar dariya,, dan jitayi tamkar yanai mata cakulkuli,,  saida ya tabbatar ta saki ranta kafun ya 'kyaleta yaja kujera yazauna,
  Itakuwa mi'kewa tayi tashiga serving d'insu abinci,,

    Bayan sungama lunch d'in ne suka koma parlour.

rage sautin TV yayi, janyota jikinsa yayi, itakuwa sai sunne Kai take, dariya yayi yace matsala ta dake kenan kunyar ki tayi yawa,, kuma ni gaskiya cutata kike da wannan salon naki dan ni Idan danni kike to kidan rage kinji matata? ya'karasa fad'a kamar wani baby,

     Itakuwa dad'a shigewa jikinsa tayi kunyar na sake kamata,  surayya... yakira sunanta in a serious tone, wanda hakan yasa takasa amsawa sai hankalinta data bashi,, yayinda 'kirjinta yashiga bugawa.......

                 Zuciyarta tashiga tsalle,, dan yanayin Fuskarsa sai ya tuna mata shi can baya.

Magana yasoma yi kamar haka....... Na tabbatar kinsan komai mu'kaddari ne daga Allah, abunda zai sake tabbatar miki da hakan kuwa shine kasancewar mu a matsayin miji da mata, wanda"ba dabarar mu bane ba kuma iyawarmu bace.... Iko ne na Allah,, kamar yadda a da can da Yaya na kikayi burin zama wanda kinso kasancewa matarsa Allah bai nufaba ashe nine wanda zaki rayu dashi a matsayin miji.......... tunda yafara magana take kallonsa 'kirjinta na sake duka.... ci gaba tayi da sauraran sa,

             Haka nima banta'ba tunani ko zaton zamtowarki mata a gareni ba, amma Allah cikin ikonsa sai ya zartar da hakan, kuma Alhmdllh ina godiya a gareshi da irin za'bin da yamun, tunda nake dake banta'ba samun wani abu na ashha a tattare dake ba wanda ke kanki kin gamsar dani kuma ina tunanin nima ban munanta miki ba,,

   Dan haka ina fatan zakiyi wa maganata Kyakyawar FAHIMTA,.......... Shiru tayi tana sake juya maganganun sa a ranta, hannunta duka biyu taji yari'ko, hakan yasa tadubeshi... cigaba yayi dacewa....bazan 'boye miki ba, kafun insan zancen aurena dake akwai wacce nakeso....dammmm.....gabanta ya buga duk da zuciyar ta tafara bata Satan amsa akan abunda yakeson fad'a mata kenan, hakan bai hanata jin mummunar fad'uwar gaba ba. had'i dajin wani iri a ranta.... take wasu irin marayun hawaye na tausayin Kai suka silalo mata wanda bama tasan da hakan ba,

            Shikuwa ganin halinda tashiga ne, yasa ya sassauta fuskarsa ba kamar farko ba, share hawayen yayi, kafun yasoma Rarrashinta da kalamai,

Surayya"Allah yasani inason Aisha, kuma aurena da ita ba yana nufin cin zarafin ki ko wula'kantaki bane a a kawai zan auri Aisha ne dan inasonta a matsayin matar aure na kamar yadda kike, ki fahimce ni please?

    Sake rungumota yayi itakuwa kamar jira take tasake masa dan marayan kuka, nanfa yashiga aikin rarrashi da kalamai irin na sanyaya zuciyar mai saurare. Allah yasani ba son surayya yake ba, saidai yana matukar mutunta ta musamman yadda takasance Macce ta gari burin ko wani da namiji,, wanda yasan watarana zai soma sonta ne,

    Hakan yasa Sam dayaga tashiga damuwa sai baiji dad'i ba dan haka yashiga lalla'bata.

    Har yasamu tasauko kuma takar'bi auransa had'i da neman alfarmar Kar yace zai wula'kanta ta idan ya auri za'binsa,, al'kawari yayi mata na babu abunda zai faru sai alkhairee,, haka ya kwashe wunin ranar yana lalla'bata had'i da sake shagwa'bata.

******************
Yau itace ranar dasu Aisha suke zana jarabawar 'karshe na shiga aji3 dan haka Koda suka fito wani hamdala tayi ga Allah cike da fatan samun nasara,

   A cafeteria"suke zaune itada Aisha action suna tattauna yadda jarabawar tayi, daga bisani Action ta dubeta Fuskarta d'auke da murmushi tace..... Beb wai yanzun idan Ayman yafito kuyi aure ya zakiyi da karatun ki?

   dariya tayi,, kafun ta d'ora da fad'in,, ehmm tom a gskiya idan dai zai barni in'karsa zanfison Hak..... kafun ta'karasa fad'a action ta katse ta, ta hanyar cewa..... Ke ina nufin fa yace kiyakiya... aure Kar yawuce 1month.... ta'karasa fad'a tana Kure ta da ido,, dariya Amishty tayi had'i da fad'in wlh sai inbar karatun in aure abuna mushige d'aki...... cike da dariya ta'karasa fad'a, itama Action dariyar tayi tace dama Bea wlh nasan abunda kika matsarwa kenan kiyi kiyi aure Asa miki wutsiya kiji yadda akeji hmmmm..... A a 'kawata karmuyi haka dake, amishty ta katseta... Wlh idan Ayman zai aureni ya soni yabani kulawa to ko bashida.... Zan iya zama dashi, Son da nakewa Ayman"so ne mai cikakkiyar daraja Aisha... Wlh ba wai son Ayman kawai nakeyi ba'kaunarsa nake.... sake baki action tayi dan itakam batasan akwai banbanci a tsakanin so da 'kauna ba....... gyad'a mata Kai Amishty"tayi kan taci gaba da cewa,'kwarai kuwa Action shi so lokaci d'aya yake shiga haka kuma idan yatashi fita lokaci d'aya zai fice yabarka da zugarka....... Itakuwa'kauna a hankali take bin gurbi lungu da sa'ko jini da tsoka tazauna,, ta yadda bazata ta'ba barin gangar jiki ba,  wlh Action a SO DA 'KAUNAR danakewa Ayman,, banaji da akwai abunda zai mun da zaisaka nabarshi,, ina matu'kar son Ayman...... Ayman bugun numfashi nane Aisha Ayman zuciya ta ne Aisha Shi d'in wata irin jijiya ce a sassan jiki na wanda idan babu shi zan iya Rayuwa idan kwana na bai 'kare ba saidai kuma bazan ta'ba moruwa ba..... Aisha ta'ba zuciyata kiji irin bugun da takeyi akan Ayman,......... hannun Action tajanyo ta d'aura kan zuciyarta,, Action kam Suman zaune tayi tana duban'kawar tata wacce da dukkanni alamu tasha giyar so tayi tatul dan kuwa gashi sai tangad'i take,,

     Batasake tsinke wa da al'amarin ba saida taga hawaye na Sauka a idonta yayinda take cigaba da cewa..... Aisha daga ranarda Ayman yajuya mun baya tofa  zan iya mutuwa...........

    Kife kanta tayi kan table had'i da sake sheshekar kuka mai cike da fargaba wanda shau'kin so da 'kauna ke gadarwa mai yinsu.....

      Baki Action tasaki had'i da fad'in this is serious....... da'kyar tasamu Amishty ta sai saitu tadawo hankalinta suka tafi gida,,Action na ci gaba da al'ajabinta.


*Wannan kenan*

A yan kwanakin Ayman sai tattala surayya yake dan garta bashi matsala, itakuwa tuni tagama amincewa da zata masa biyayya dan sonsa da take ta yadda take ganin babu abunda zai bu'kata bata goya masa baya ba.

Hakan da take nunawa sosai yake 'Kara mata'kima a idonsa.

Zaune yake a garden d'in gidansa bayan yadawo daga yin submitting projects d'insa, waya yake da abar sonsa cike da shau'kin'kauna. Inda yake tabbatar mata da baifi sati d'aya ba zai dira a'kasar Naija

Sosai tanuna farincin ta da jin daddad'an zancen dan sosai take mararin ganinsa,  jin kiran sallah yasa taimasa sallama da zummar zatayi sallah,
*****
       Kwanciya yayi a gefen matarsa bayan yagama komai na al'adarsa ta kwanciya, janyota yayi, yayinda itama tasake sakin Jikinta a faffad'an'kirjinsa.

       shafan ta yashiga yi daga bisani yahad'e bakinsu guri d'aya, tamkar yasamu wani sweet haka ya dinga lailaya harshensa a bakinta itama ta yasa tayi cike da irin nata salon data koya daga gareshi yamutsa juna suka shiga yi bakajin komai sai saukar numfashin su,, length d'insa yasaita cikinta,, yau sosai yake murzata, cike da ta yarda hankali...... Saida suka samu natsuwa kafun ya sarara,

      Bayan sunyi wanka sun kwanta yasake rungumota, had'i da fad'in, surayya.. Amsawa tayi cike da natsuwa, ina son zuwa Naija cikin sati mai zuwa idan Allah ya yarda, shiru tayi masa tamkar bataji mai yace ba, jin shiru ne yasa yace ko bakiji mai nace bane? a hankali tace Allah ya kaimu ya kiyaye hanya..... tana gama fad'i hawaye nasauko mata, yalura da yanayinta dan haka yace ko kinada matsala da tafiyar ne? Uhmm??

   A ranta tace... ji sai kace idan nace yafasa fasawa zaiyi? Uhmm

A zahiri kuwa cewa tayi.... nidai inason zanbika inga mommah, murmushi yayi yashiga shafar bayanta had'i da fad'in shikenan ki shirya inyaso Sai mutafi,..... da farinciki tace... Really? dariya yayi had'i da hura mata iska a kunne, itama dariyar tasaki had'i da gantsaro 'kirjinta wanda batasanma tayi ba..... Saida yace uhcchhhhh beb.....had'e bakinsu guri d'aya tayi, tana aika masa da zafafan wasanni,, tuni suka koma ruwa.




Xinnee smart 👌🏻💋

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now