KO BAZAN AURESHI BA...
(hattara Yan mata)
XINNEE SMART
whatpadd @xinnee_smart1
Page 3....
Ran yaya'Ali, ne ya dad'a 'baci ganin bata da niyyar fad'in gaskiya ne yasa yajanyo wayar rechargeable, yasoma zuba mata, tun tana, daurewa, har tasoma ihu,
Shikuwa ko saurara mata bayayi yi yake yana had'awa da shurinta da'kafa Fuskarta kuwa tasha Mari harsaida ha'bo yafashe mata, sossai yakejin haushinta irin yadda Suda suke maza basu janyowa iyayensu magana ba, sai ita mace macen ma,'karama,...
Kuka take wanda ran umma'baci yakeyi dajin kukan nata, saidai gwara a horata kotasan mai takeyi,
Abba, ne yayi sallama a'kofar gidan dan dama d'abi'arsa ce sai yayi sallama tun'kofar gida kafun yashigo, mamaki ne yakamashi najin kukan mamansa, kasancewar sunan mahaifiyarsa ne da ita, kuma auta,.
Dasauri ya'karasa cikin gidan, Umma yagani tsakar gidan tana duba littafin, muwad'd'a,
Wanda Sam bata fahimtar mai take karantawa, tsabar damuwar datake ciki,
Kallonta yayi, baice komai ba yanufa d'akin dayake jin kukan nata,Shikuwa, Ali, zuciya nacin sa sai dad'a hauhawa yake gashi d'azun yanaji wasu samarin anguwar suna firanta da irin bad'alar datakeyi, gabin 'kawaye,.... Caraf yaji anri'ke hannunsa, Abba yagani, dan haka yaja baya yana huci,
Kallonsa Abba, yayi yace haba gadanga? duka baya gyara, saidai ma yasake tunzura zuciya, adai dinga nasiha ana had'awa da addu'a, yana gama fad'in haka, ya'karasa gurin da, Aisha ke dur'kushe tana faman kuka, d'ago da ita yayi, yaja hannunta zuwa waje, ruwa tad'ebo a buta yami'ka mata, kar'ba tayi tanaci gaba da sheshekar kuka,
Zuwa tayi gurin rariya, ta wanke fuskarta, had'i da kuskure bakinta da sai jini yakeyi, tana gamawa Abba yaja hannunta zuwa d'akin shi, ledar daya shigo da ita yabud'e naman rago ne gashashe wanda akaiwa gashin ruwa ruwa,
Tura mata gabanta yayi, mamana ci kinji? Sai kisha magani,
To tafad'a kafun tasoma ci, saidai tagama yami'ka mata paracetamol, tasha, Saida yaga tanutsu, yasoma yimata nasiha,
Kai kawai take d'agawa kamar 'kadangaruwa, sossai tayi fuskar amsa, kamar tad'auki nasihar, yana gamawa yace taje ta kwanta,
Mi'kewa tayi tanufa d'aki....Tana shiga ta kwanta kan katifar ta, tana sauke ajiyar zuciya da tsaki, sa'ka yadda zata rama wannan duka da yaya'Ali yayimata take, kuma yanzun tasoma,
Wlh ba fashi, ko zai dinga yankan naman jikina bazan daina abunda nake ba, mts tafad'a tana janyo wayarta,
Barima inhau Facebook ko zanga Amdad, yadan ebe min wannan takaicin na 'kauyawan Yan gidanmu,
Shiga Facebook tayi tasoma chart d'inta kamar bayanzu tagama shan duka akan ireiren abunda takeyi ba,....
Washe gari,
Umma, dama tana zuwa islamiyyar goma atashi sha'biyu, tana ganin umma tafita yayyinta, duk sunfita, itama ta tashi tayi wanka tasaka doguwar rigarta, tayane kanta da d'ankwalin rigar sossai tayi kyau kasancewar abu, yellow a jikin farin mutum,
Kallon kanta tayi a madubi, 'kyacci tayi ganin kumburin Fuskarta,,
Plat shoe tasaka, tad'auko, Gucci eyeglasses d'in ta tasaka, wayarta tajefa cikin side bag, d'in t,Dasauri sauri, tabar layinsu, gudun Kar d'aya daga cikin yayyinta tsautsayi yasa yadawo su had'u, adaidaita tasamu, tashiga,
Gidansu Nierjer, tanufa kai tsaye,
YOU ARE READING
KO BAZAN AURESHI BA.........
FantasyLabarin budurwa mai rayuwar Kwad'ayi da buri, cike da rashin godiyar Allah,........................