KAMBUN SADAUKANTAKA

2.7K 118 6
                                    

WRITTING

BY

MS Kutama

WHAT'SAPP NO

08102979121

FACEBOOK

Mohammed S Abubakar Kutama

INSTAGRAM

RealMSKutama

G MAIL

mskutama89@gmail.com

AREWA WRITER'S ASSOCIATION

{Arewa ginshi'kin al'ummah }

https://www.facebook.com/104534761033461

godiya ga duk members na wannan gida mai albarka sai dai nace muku much love 😍

bama kamar ku

Autar Arewa
laurat M Bello
Ummu Affan
Ummu Intisar

_____________________________________________

Daddadar Iskar dake kad'awa cikin birnin na damascar shiya 'karasa mutanen birnin cigaba da tafiyar da harkokin su cikin annashuwa.

Duk wanda kagani sha'anin gabansa yake yi cikin walwala

Wani kyakkyawan matashi ne shi kad'ai a cikin wani 'katon fili ri'ke da wata zabgegiyar wu'ka yana kai sara da suka

Wohoho irin yanda yake yin katantanwa asama yana kawo Sara sai karantse bataliyar runduna yake ya'ka alhalin ko mutum d'aya babu a filin ya'kin

Lokaci daya kuma sai ya tsaya cak sakamakon tahowar mahaifinsa da ya gani zuwa garesa fuskarsa fad'ade da murmushi ya dubi dan nasa ya bude bakinsa yace " madallah da abin alfaharina dirkar birnin damasca na gobe, lallai duk cikin zuriyar mu kaine ka gaji kakanka

Saurayin yayi murmushi tare da tura takobinsa tare da rungume mahaifin nasa suka juya suka nufi cikin gari.

Wani katafaran gida na alfarma suka nufa wanda aka kawatashi da shuke shuke dakaru na ta kai kawo duk inda suka ratsa bayi da barori sai faduwa suke suna kawo gaisuwa

Kai tsaye wani kasaitaccen bangare suka nufa wanda akayi masa ado da marjani

Suna shiga ciki wata kyakkyawar mata tafi to wadda suke da tsananin kama da wannan saurayi nan naga inda ya gado asalin kyau

Cikin nuna matukar kulawa ta dubesu tace "sai da kaje ka taho dashi kenan nasan muddin idan ba kai kaje ba bazai taho ba"

Mahaifin nasa ya dubi fuskar dan nasa da yake murmushi yace kaji abinda maman ka tace koh

Yace ai dama koda da kake tafiya dani filin ya'ki ba'a son ranta kake tafiya dani ba

Kallo daya mutum zai yiwa sarkin yaki ya tabbatar da cewa ya kasance sadaukin sadaukai domin da gani ba tambaya kasancewarsa dogo mai murdadden jiki.

Duk da kasancewar a yanzu sun haura hamsin kasancewar akwai sauran kuzari a tare dashi, kuma komay takamar jarumi zaiyi shakkar yayi masa shigar farat! daya saboda kwarjininsa

Asalin Sunan wannan saurayi Sub'am, mahaifinsa kuma mukarram wanda shine sarkin yakin birnin damascar kuma 'kani kwaya daya tal ga sarkin birnin damasca wato zaid ibn i'kbal

Mahaifiyarsa kuma husainat ita kuma itace abokiyar haihuwar matar sarkin

Kafin zaid da mukarram suyi aure sun kasance TARWATSA MAZA kuma gobara daga kogi.

Domin duk birnin da suka tunkara sai sun mayar dashi abin tarihi a duniya sun mayar da sarakai bayi kuma sun shafe birane da yawa.

Sarakuna da dama na wannan lokacin suna matukar tsoron wannan runduna ta tagwayen fama da su kayi mata lakabi da guguwar annoba.

Duk Sa'adda Zaid da mukarram suka jagoranci runduna ba'a ta6a samun akasi ba sai dai nasara.


Al'amarin da yasa yasa kasar damasca tayi shuhura a duniya kenan ta bangare daban daban musamman gasar da ake sawa duk bayan shekaru goma ta KAMBUN SADAUKANTAKA na duniya wanda ake gabatarwa akasar ta damasca

Tun sa'adda zaid da mukarram suka taso da kuriciya sarki i'kbal ibn sabit yasa aka killace su a gidan na sarautar birnin damasca ya zamana ana basu horon ya'ki a wannan lokacin da mahaifinsu ke sarauta

inaso na 'rin'ka yin post da yawa amma babu lokaci
amma please dears take note ana mugun tare

KAMBUN SADAUKANTAKAWhere stories live. Discover now