🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
*ᗰᗩᖇᗪIYYᗩᕼ*
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳~Fiction~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984
🤝🏻 *ᎪᏁᎪ ᏆᎪᏒᎬ ᎳᏒᎥᏆᎬᏒs ᎪssᎾᏟᎥᎪᏆᎥᎾᏁ* ✍🏻
*_Not edited_*
1⃣
بسم الله الرحمن الر حيم
Hijab ce ruwan ƙasa sanye a jikinta wadda ta kai mata har saman ƙafafunta domin sharar hanya kawai hijab ɗin keyi, sannan kallo guda za kayi ma hijabin ka gane ta gaji da rayuwa domin tsananin koɗewa da tayi, kallo guda ba zai sa ka fahimci ita ɗin daga wane jinsin mutane ta fito ba, domin duk da cewa rayuwar talauci da wahala ta ke ciki, fara ce tas mai asalin kyawon halitta a fuska, tayi kama da *Buzaye* haka kuma tana yanayi da *Larabawan Labanon* ita kam mamallakiyar hijab ɗin zuba zauri kawai take har ta ƙarasa bakin wani ƙaramin gida ginin lakka wanda kallo guda za ka yi mashi ko daga waje ka fahimci ya jima da aka gina shi, in bai kai shekaru saba'in ba toh zai wuce hamshin..
Domin kuwa katangar gidan ta lakka duk ta gama ɓaɓɓangarewa ta koma kwata, wanda yasa kana iya hango wani sashi na cikin gidan, sallama ta rafka cikin gidan dake da ƴar ƙaramar tsakar gida sai ɗakuna guda biyu jallin jal a jere tare da ƙaramar baranda da akayi masu, sai kuma can gefe guda makewayi ne irin na gargajiya da aka kewaye da langa-langa, gefe guda kuma daga yamma ɗan wajen da suke ɗora girki ne komin rana, ruwa da sanyi anan ne wajen girkinsu.
Ɗaki na farko matashiyar budurwar ta shiga inda ta iske wata matashiyar mata wacce da kaɗan zata girme mata, sai kuma wata tsohuwa akwance tanata faman nishi matar dake zaune da ita tana mata fifita da mafeci, Antee na dawo sai zuba sauri nake na kawo ma Magajiya abincin nan, matashiyar budurwar take faɗi lokacin da ta cire dogun hijabin jikinta wata koriyar roba mai murfi ta bayyana.
Wacce aka kira da Antee ɗin wanda ainihin sunanta Bilkisu, doguwa ce siririya wankan tarwaɗa tana da cikar ƙirji da dogun hanci sai manyan idanuwa da ƙaramin baki, bata da muni amma kuma ba zaka kirata mai shahararran kyau ba, shekararta biyu kenan da auren Yayan matashiyar budurwar nan mai suna Zayyan, sauke ajiyar zuciya tayi karo na farko tun zamanta cikin ɗakin ta kalli budurwar tana ɗauke wasu ruwan hawaye dake neman saukowa daga idanuwanta tace " Mardiyyah anya Magajiya zata iya cin komai yau kuwa, jikin nata fa ya yi tsanani yanzu Zayyan ya fita kyamis ɗin bakin kasuwa neman magani domin wuni tayi amai da wannan nishin..".
Mardiyyah ta zauna kusa da mai jinyar tana faɗin Antee jekiyi wanka ki kintsa bari na zauna da ita tunda na dawo, Allah ya baki ɗiyan da zasu kula dake haka yadda kike kular mana da Kaka baki taɓa gajiyawa ba, Bilkisu bata ce komai ba miƙe ta fice jikinta amatuƙar mace, Mardiyyah ta matsa tana buɗe wannan roba ta abinci tana faɗin Magajiya tashi ga abinci kici ko kya samu ƙarfin jiki, abincinki ne shinkafa da wake da mai da yaji, Magajiya ta ɗan buɗe ido kaɗan cikin tsananin jin jiki tana magana ahankali wanda da kyar muryar ke fita.
Mardiyyah a yau ba abinci nake buƙata ba, na gama cin iyakar rabona, a'a Magajiya bari na miƙar dake ajikina na baki ko yaya ne kici yafi zama da yunwa, girgiza kai tayi tana faɗin ki saurareni Mardiyyah, domin bani da ishasshan lokaci, abinda zan gaya maki ke kaɗai ce baki sani ba, Yayanki ya sani, tunda da wayanshi wasu abubuwa suka faru.
Ni ɗin kamar yadda kika sani Magajiya ce amma sunana na asali Lamunde, cikakkiyar ƴar jahar Barno ce, na samo sunan Magajiya ne saboda ni ce magajiyar *KARUWAI* ta wancan lokacin, ni ɗin bansan asalina ba na tashi kawai na tsinci kaina a gidan karuwai ne, ahannun Magajiya ta wancan lokacin, ance mahaifiyata karuwa ce a gidan tayi ciki na anan kuma ta haifeni, ta haifeni da wata uku ta rasu sakamakon matsiyaciyar jinya data sha, uba na dama dai babu wanda ya sanshi.
YOU ARE READING
MARDIYYAH
FanfictionRabi Buzuwa ce, rabi kuma Balarabiyar Saudiyya, Tun tana cikin zanin goyonta ta tashi ta tsinci kanta a gidan magajiyar karuwai, daga nan ƙalubalen rayuwa ya risƙeta...