🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳
*ᗰᗩᖇᗪIYYᗩᕼ*
🕳🕯🕳🕯🕳🕯🕳~Fiction~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984
🤝🏻 *ᎪᏁᎪ ᏆᎪᏒᎬ ᎳᏒᎥᏆᎬᏒs ᎪssᎾᏟᎥᎪᏆᎥᎾᏁ* ✍🏻
*_Not edited_*
Barkanmu da sallah ƴan uwa musulmai.
2⃣
بسم الله الرحمن الر حيم
Kano ta dabo tumbin giwa, Kano garin kasuwanci garin da ko dame ka zo anfika...
Layin kanshi inka gani zaka san na masu hannu da shuni ne, saboda tsaruwarshi da kuma ƙarancin gittawar jama'a da ababen hawa na masu gidajen cikin unguwar, a can tsakiyar layin bayan dogayen bishiyoyin itacen dogon yaro ƙaton get ɗin gidan yake.
Ƙaton gida ne ginin zamani irin na masu kuɗin wannan zamanin, baya ga ainihin babban sashin gidan akwai ƙananun sassa har guda huɗu, biyu na ma'akatan gidan ne maza da mata sai ɗaya mai ɗan girma yana daga waje guda, sai namu wanda aka bamu dake kallon ƙaramar ƙofa ta bayan gidan, wanda ya wanci ta wannan ƙofar ma'aikata gidan ke shige da fitarsu.
Ɓangaren namu duk da yake ƙarami amma ya tsaru ya kuma haɗu, akwai falo madai-dai ci mai haɗe da ɗaki sai kum ɗaki ɗaya a gefenshi sai kicin ƙarami da kewayen wanka dana bayan gida da ban da ban, sai kuma ɗan ƙaramin tsakar gida, duk kannin gidan akwai kayan su gado da kujeru kicin ne kawai babu komai, dan haka gadon Bilkisu sai dai aka tsaidashi saboda ba wajen sanyashi, Zayyan shi da matar tashi Bilkisu sune suka ɗauki ciki da falon sai aka ba Mardiyyah mai ciki ɗaya.
✨✨✨✨✨✨✨
Kwanansu biyu da dawowa Kano, tunda suka shiga gidan ba wanda ya fita sai Zayyan da mai gidan Alhaji Idris Bilyaminu daya yi mashi hanyar samu, domin cikin shagunanshi na kasuwar kwari yake mai tsaronshi wanda ya sanyashi shi ne babba awajen, abokin kasuwancin Alhaji Idris da suke harkan noma a can Charanchi Malam Balarabe, shi ne Alhaji Idris ya taɓa mai ya cigito mai wani ɗan matashi da ya yadda dashi, domin yana neman wanda zai zauna mashi a sabon shagon ɗaya kama na atamfofi da lesuna da sauran danginsu.
Malam Balarabe bai tunanin komai ba sai Zayyan domin yaron yana da natsuwa da kuma ilmi dan har matakin Diploma gareshi, to shi ne fa ya haɗashi da Alhaji Idris, su kayi magana jin cewa yana da iyali yasa yace yana da wajen zama zai bashi ba tare da biya ba, sannan kuma zai bashi albashin shi.
Alhaji Idris Bilyaminu aɗuk garin Kano an sanshi mutun ne mai mutunci da tausayin talakawa, gida da ofis koda yaushe ala mashi layi dan neman taimako, yana iya ƙoƙarinshi wajen taimakon nasu kuma, shiyasa dukiyanshi koda yaushe ƙara haɓaka take, ɗan kasuwa ne sosai, baya ga tarin ilimi da yake dashi duka biyun, sai bai rataya samunshi a aikin gwamnati ba ya shiga kasuwanci nan gida da kuma ƙasashen ketare, yana da mata guda ɗaya jallin jal da 'ƴa'ƴansu uku biyu mata sai ƙaramin namiji, yana da matuƙar sauƙin kai da haƙuri.
Mardiyyah ce ta ɗago labulen falon tare da sallama tana faɗin na gama gyaran kicin ɗin Antee, Bilkisu ta sanya hijabin dake hannun kujera tana faɗin mu tafi toh kada suga rashin hankalinmu kwana biyu da zuwa masu gida bamu shiga ba, Mardiyyah tayi murmushi tana cewa aikuwa dai.
Gaba ɗaya ƙauyawa suka zama lokacin da suka gansu cikin tamfatsetsan falon gidan Alhaji Idris da aka shaƙe da kayan jin daɗi na more rayuwa, suna santin nasu sassan sun zo ainihin inda aka kashe daula, Hajiya Mariya tana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana cin 'ya'yan itatuwa tana kuma murmushi ganin yadda su Mardiyyah suka takure waje guda aƙasa, kamar ma cikin tsoro suke.
Karo na biyu ta kuma cewa tunda kunƙi zama kan kujerun kusha ko ruwa ne da aka aje maku mana, girgiza kai Bilkisu tayi tace, Hajiya haƙuri muka zo bayarwa bamu shigo gaisheku ba sai yau, wani murmushin tayi tace kai haba aina san hidimar tashi da kuma tarewa.
Ta canza alaƙar firar da cewa, wannan ƴar budurwar ƙanwarki ce? Dariya ta ɗanyi Bilkisun ta ce a'a ƙanwar shi ce, masha Allah Hajiya ta faɗi, meye sunanki ne? Mardiyyah Hajiya, Mardiyyah tayi saurin bata amsa, nan taci gaba dayi masu ƴan tambayoyi har suka ɗan saki jiki suna hira sama-sama.
Koda suka dawo sassansu hirar Hajiya Mariya suka dingayi saboda matar akwai sanyin hali da mutunci, tun daga wannan rana Mardiyyah sai ta shiga wajen Hajiya Mariya tana yi mata ƴan aiyuka duk da tana hanata saboda akwai ƴan aiki amma sam bata bari ba, ana haka ɗiyar Hajiyar ta fari ta dawo daga hutun sati guda data je wajen dangin babanta mai suna Saudat.
Mardiyyah da kanta ta shiga ta gyara ma Saudat ɗakinta ya yi fes sai ƙamshin turaren wuta yake, lokacin da Saudat ta shigo ɗakin Mardiyyah ta gama ƴan goge-gogenta tana shirin barin ɗakin ta shigo.
Da farko kallon juna suka tsaya suna yi, Mardiyyah tayi saurin cewa barka da zuwa Hajiya, Saudat dariya tayi tana aje handbag ɗinta akan gado, tace wace irin hajiya kuma dan Allah, ina jin ko zan girmeki baifi na baki shekata biyu ko uku ba, kirani da sunana Saudat kawai, Umma ta bani labarinku yanzu, ni har ina na samu ƙawa danaji tace budurwa sa'ata, amma shi ne zaki wani ce hajiya ta idasa maganar tana ɗan mata hararar wasa, murmushi kawai Mardiyyah tayi tana faɗin bari na baki waje ki huta toh, ta fice Saudat na binta da kallo tana murmushi, haka kawai lokaci guda gani na farko taji Mardiyyah ta kwanta mata arai, taji ƙaunarta kamar yadda take ƙaunar ƙanwarta Zubaidah dake ajin ƙarshe a makarantar secondary dake Abuja.Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, sabo, shaƙuwa da kuma ƙaunar juna ta wanzu tsakanin Saudat da Mardiyyah, a halin yanzu ma dai Saudat ta hana ace mata wata Mardiyyah wai sunan Charanchi dan haka ta yanke sunan ya koma *Mardy*, tafiya ba tayi nisa ba suka zama ƴan gida kai harma da gari gaba ɗaya, Saudat tana ajinta na ƙarshe a nan *University ta Bayero* tana karantar *Political Science*, dan haka lokaci bai yi nisa ta fahimci Mardy ta gama seccondary ɗinta tuni, da kanta taje har falon Babanta Alhaji Idris ta roƙeshi alfarmar ɗaukar nauyin Mardy daga aji ɗaya har inda taji zata tsaya.
Shima da yake mai son taimako ne ba ɓata lokacin ya amince ya damƙo kuɗi ya bata yace taje a siyawa Mardy jamb ta zana ta kuma sanya duk irin course ɗin da take so...
Labari na isar ma Mardy mamaki da ƙaunar Saudat ya cika zuciyarta lallai ta amince ita ɗin mai ƙaunarta ce da zuciya ɗaya, dan haka Zayyan na shigowa ta labarta masu komai, a cikin dare su duka uku suka je yi ma Hajiya da Alhaji godiya dasa albarka.
To ita rayuwa dama haka take, yau daɗi gobe maɗaci, inka rasa farin ciki ta wani fanni, sai kaga ka samu ta wani wajen kuma, rayuwarsu Mardy a garin Kano rayuwa ce da koda wai basu taɓa hasashenta ba iya tsawon rayuwarsu..
Ta fannin komai ya samu canji a garesu, Saudat ta ɗauki Mardy kamar ciki ɗaya suka fito, bata taɓa siyan abu ba, ba tare da Mardy ba, tun daga sutura kayan kwalliya man shafawa da sauran tarkace na mata Saudat tana masu, haka kazalika iyayen Saudat basu banbantasu ba suna iya ƙoƙarinsu wajen kyautata masu har su Bilkisu da Zayyan ɗin.
Babu laifi Jamb ɗin Mardy tayi kyau dan haka ta samu abinda take nema wato *Internationl relation* , lokacin da suka fara ɗaukar lacca Saudat ta kammala nata karatun Inda babu jimawa ta ɗora da Masters ɗinta Mardy ana 200L ita kuma Zubaidah ta shiga 100L dai autansu yana aji biyar na secondary mai suna Mas'ud.
*Machika Novels*
YOU ARE READING
MARDIYYAH
FanfictionRabi Buzuwa ce, rabi kuma Balarabiyar Saudiyya, Tun tana cikin zanin goyonta ta tashi ta tsinci kanta a gidan magajiyar karuwai, daga nan ƙalubalen rayuwa ya risƙeta...