page 3-4

458 28 0
                                    

🕳🕯🕳🕯🕳
*MARDIYYAH*
🕳🕯🕳🕯🕳

~Fiction~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984


🤝🏻 *ᎪᏁᎪ ᏆᎪᏒᎬ ᎳᏒᎥᏆᎬᏒs ᎪssᎾᏟᎥᎪᏆᎥᎾᏁ* ✍🏻

( *We are the best writers among all writers*)📚

*_Not edited_*


3⃣⏩4⃣


بسم الله الرحمن الر حيم




Sanye take cikin wani jan leshi mai ratsin zare golden, dogowar riga ce akayi mata har ƙasa da ɗankwalinta inda ta kafa ɗauri ta turoshi agoshi, irin dai wanda ƴan mata da matan aure ke yayi a yanzu, ƙananan ƴan kunne ta sanya masu madai-daicin tsayi , ba komai ga fuskarta sai pink lipstick da jar hoda sai kuma baƙin kwalli da ta zizara ma idanuwanta masu tsananin haske.

Lokaci guda kuma ta tsaya tana ƙarema kanta kallo, tun daga fuskarta har zuwa yatsun kafarta a jikin dogon madubin dake ɗakinta, tana mamaki duk da cewa Allah ya yi mata tsarin halitta mai kyau, domin siririya ce doguwa mai madaidaitan cikar ƙirji da mazaunai, fara ce tas irin farin nan mai kyau ba gau ba, sumar kanta har kusan mazaunanta baƙa suɗik mai santsi da laushi da kuma cika, sai wasu ƙananun gashi da suka kwanta a goshinta har zuwa kusa da girarta miƙaƙƙiya baƙa, tana da dogon hanci siriri da ƙaramin baki inda lips ɗinta suke pink masu kyalli...

Kallo guda zaka yi mata kasan ita ɗin bata haɗa jinsi da kowa ce ƙabila ta Nigeria ba, tana kama da *Buzawa da kuma Larabawan Labenon*, ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gama ƙarema halittar tata kallo tana yafa gyale golden ta zura takalmi flat tana surar jakkarta domin jin Saudat ta soma danno mata horn ɗin mota, tunda suka shiga makaranta suka kama su uku Saudat da Mardy sai Zubaidah, Alhaji Idris ya sai mota ya danƙa ma Saudat domin rage masu hawa motocin haya..

Tun daga nesa Saudat ke galla mata harara Zubaidah na murmushi ƙasa-ƙasa, ta ƙarasa da sauri ta shige mazauninta agaban mota yayinda Zubaidah ke baya ita kaɗai dama haka suke tsarin zamansu kullum, ta mayar da fuskarta kalar tausayi tana kallon Saudat, pls Sis kiyi haƙuri na tsaya kallon kaina a madubi ne ina yaba halittar rabbi...ta idasa maganar tana ƙunshe dariyarta, dogon tsaki Saudat ta saki tana jan motar suka fita gidan...

Ke dai Allah ya sawwaƙe maki ace mutum bashi da aikin yi sai kallon kanshi a mirrow, kuma ni naga duk wannan shahararran kyan naki har yau banga gwaninki ba, ta ɗanyi murmushi kalar na mugunta, Yaya Zayyan zan zuga ya samo wani ɗan buzu ya haɗaki dashi kawai muga ƙaryar iskanci, Mardy ta ja dogun numfashi ta fesar lokacin da yanayin damuwa ya wanzu a fuskarta, tayi shiru tana tuno yanayin da suka shiga kan manema auranta can baya saboda rashin asalinsu...tasan abu ne mawuyaci idan zata yi aure a duniya, domin babu wanda zai auri macen da ba'asan asalinta ba balle wani dangi nata, ta ɗauke kai tana kallon window lokacin da ta ɗauke wasu ƙananan kwalla ba tare da kowa ya fahimce ta ba.

✨✨✨✨✨✨

Wani irin waje ne mai matuƙar sha'awa da kamar lambu kamar wajen shaƙatawa, tana zaune kan wasu korayen ciyayi masu taushi da ƙamshi tana shafasu da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana tanats yawo dashi saman cikinta da yai wani irin girma na ban mamaki, ta shige tunanin haihuwar yara har biyu da aka ce mata zata haifa a haihuwar fari...

Jinjina al'amarin take cikin damuwa da fargaba, a hankali taji wasu hannaye masu taushi sun rufe mata idanuwa sannan wani ƙamshi mai daɗi ya ziyarci hancinta, ɗan murmushi ta saki damuwar cikin ranta ta washe, ba tare da mamallakin hannun ya baro bayanta ba ya zame hannayenshi yana zama a bayanta yayinda ya ɗan kwanto da bayan nata kan ƙirjinshi yasa hannu guda yana shafar gashin kanta ɗayan kuma ya ɗora kan cikinta yana faɗin Mardy inkin haifa mana duk maza sunan mu zan maida kamar yadda muke twinx, in kuma mata ne toh ɗaya Sunan Saudat za'a sanya, ɗayar kuma sunan Umma...

MARDIYYAHWhere stories live. Discover now