page 5-6

668 40 16
                                    

🕳🕯🕳🕯🕳
   *MARDIYYAH*
🕳🕯🕳🕯🕳

~Fiction~

© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ

w̲̅a̲̅t̲̅t̲̅p̲̅a̲̅d̲̅~a̲̅y̲̅s̲̅h̲̅a̲̅m̲̅a̲̅c̲̅h̲̅i̲̅k̲̅a̲̅ 1984


🤝🏻 *ᎪᏁᎪ ᏆᎪᏒᎬ ᎳᏒᎥᏆᎬᏒs ᎪssᎾᏟᎥᎪᏆᎥᎾᏁ* ✍🏻

( *We are the best writers among all writers*)📚

https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/

*_Not edited_*

5⃣⏩6⃣


بسم الله الرحمن الر  حيم


Kafin ƙarfe ɗaya Mardy har ta gama haɗa snacks ɗin gaba ɗaya ta koma shirya mai tsabtataccen lemo na kayan marmari wanda ba algus a cikinshi, ko sugar bata sanyata ainihin fruits ɗinne kawai ta markaɗesu, juyesu tayi cikin jug na glass ta sanya a fridge domin ya yi sanyi, ita kuma Saudat tana can daga gefe tana haɗa abincin da zasu mai kala biyu, dan haka Mardy ta matsa tana idasa haɗa potato surp mai kayan haɗin carrot, green beans da kuma ƙananan yankakkun nama da ƙoda a haɗe, kicin ɗin gaba ɗaya ya kacame da ƙamshin girkin nasu.

Hajiya Mariya ta shigo tana shaƙar ƙamshi murmushi saman fuskarta take cewa wannan irin better haka Mardiyyah, da fatan dai ba ƙamshin kawai zamu ji ba za'a sammana mu ɗanɗana, Mardy na dariya take faɗin haba Umma ai ko kowa baici ba dole ne na kawo maki naki, Saudat ta ɗan tura baki gaba tana cewa uhm..hmm...gaskiya Umma kaɗai za'a dan indan kika biyema ƴan nan gidan toh su zamuyi ma wahalar, dan ma auta bai nan Mas'ud aida komai sai yaci, Umma taɗan harareta toh du dai tsiyarki sai munci, inkikai wasa ma yanzu na ɗaga waya na kirashi ya zo shi Mas'ud ɗin...

Saudat ta ɗaga hannu sama alamar tayi saranda gaba ɗaya suka sanya dariya, Umma ta juya ta fice su kuma suka ci gaba da girkinsu, duk saurinsu sai da ƙarfe 3 suka kammala komai suka shirya shi a falon sauƙar bakin sannan ko wacce ta wuce tayi wanka..


*LEBANON* *(BEIRUT)*

Brown suit da farar longe sleave tare da nect tie brown mai ratsin fari sai takalmanshi suma light brown sosai da silver agago ɗaure a tsintsinyar hannunshi, a haka yake takawa cikin dogun coridor ɗin da zai sada shi da ainihim falon shaƙatar *Haroon Abdul-Shams ibn Abdul-Rahman*, matashin namiji ne wanda ba zai wuce shekaru 28 ba, kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane ɗan yankin Africa ne ɗan Nigeria kuma Hausa/Fulani..

Fari ne ba irin dau ɗin nan ba, irin dai farinmu na Hausa/fulani, yanada tsawo da kuma siranta ba can da yawa ba, a fuskarshi kwayunshi kadaran-kadahan ne amma skin ɗinshi glowing yake irin na hutu da jin daɗi, akwai saje daya zagaye fuskarshi ya zo ya haɗe da ƙaramin gashin bakinshi,  bakinshi bai da wani wadataccen girma amma yana da ɗan tudun laɓɓa *Haysam* kenan, yana cikin shekarunshi na takwas aƙasashen larabawa inda yake karantar likita a fannin kwakwalwa...

Haysam muskilin mutum ne na gayawa sarki, bada kowa yake magana ba sai inta kama, yana da sanyin hali da himma ga abunda yasa a gaba, sai kuma Allah ya bashi baiwar karatu wanda a yanzu haka shekarar data wuce ya ƙare course ɗinshi amma har ya soma ɓare kawunan bil'adama domin gano matsalolinsu, larabci abakinshi kamar can aka haifeshi in yana feso maka turanci kuma saika rantse da Allah jikan sarauniyar ingila ne...

A hankali bayan ya isa inda ƙofar shiga take ya sanya babban ɗan yatsanshi jikin wani glass inda aka soma scanning finger frint ɗinshi, sai kuma ya gwalo idanuwa ajikin wani glass transferent shima aka yi scanning idon sannan ƙofar tayi wata ƴar ƙara kaɗan sai ta bude tana faɗi da larabci "Marhaba Ya Shereef Haysam", ya tura ya shige sannan ƙofar ta rufe kanta.

MARDIYYAHWhere stories live. Discover now