💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*written*
-by-
*Deeja one love**🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆
*Dedicated*-to-
*Maryam khamis**deeja one love hausa novels thanks for your support ga naku nan na sadukar muku dashi*.
*Anty fatee kuma ina godiya sosai, comments din ku na kara mini shauki kuma ina jin dadi sosai*.
69-70
suna shiga cikin daki,Hafsat ta kalli Ikhlas tace"Dama wai Saifullahi shine zuman ki? ",Murmushi Ikhlas tayi.
Suna shirya kaya Ikhlas tace"Ki ga wai shekara wajen nawa rabo na da mahaifiya ta amma wai ba za'a bari na zauna wajen ta ba".
Iman tace"Hakan fa cikin gata ne, Kada ki manta shekara nawa kina da burin zuwa dangin ki, Yau Allah ya cika miki ba sai kiyi murna ba, Ni ba gani ba ban san wacece mahaifiya ta ba ban san waye mahaifi na ba ballantana dangin su,Kuma ina rayuwa cikin farin ciki, Kin san saboda me? ".
Ikhlas ta girgiza kai, Iman tayi murmushi tace"saboda ina godewa Allah a duk yadda na sami kai na".
Sosai maganar ta ta yiwa umma dadi wacce tazo shigowa dakin,Haka suma su feenert.
Umma tayi sallama ta shigo,Kasa suka yi da kai bayan sun amsa mata,Hannun Ikhlas ta rik'e ta zaunar da ita.
"Haba Ikhlas babu abinda yafi dangi dad'i, Ban fahimci hakan ba sai yanzu, A lokacin da 'yan uwan mahaifin ki suka sako ni a gaba, Haka dan uwa na ya yarda d'an shi ya aure ki ba tare da sanin ina kike ba,Wallahi Ikhlas bakida gatan da ya wuce nan".
Muryar Ikhlas na rawa ta amsa da"Hakane Umma tabbas 'yan uwa suna da matukar girma, To amma Umma bana son Maleek tun ba yanzu ba,Shima haka baya sona".
"Kada ki damu da wannan idan har kika je kika zauna a kusa dashi zaki so shi haka shima zai so ki, kinji", Daga kai kawai tayi ba dan ta yarda ba.
Karfe biyu dai-dai jirgin su Ikhlas ya daga zuwa kaduna,ko a cikin jirgi babu wanda yayi wa wani magana.
Maleek ya kwantar da kan shi a jikin mummy, Mummy ta balla mishi harara tace"Ai wallahi zaka gane kayi kuskure ne".
Turo baki gaba yayi yace"To mummy so kike nayi karya nace ina son ta", Daga mishi hannu tayi tace"Magana kuma ai ta kare Maleek".
Suna landing motoci suka zo dibar su, sai gida,Iman kuwa dama jirgin da zai wuce bauchi suka hau.
Da idanu take bin gidan,Domin gidan babu karya ya hadu,Lallai dole saifullahi yayi mata barin kudi.
Sai da suka yi wanka suka huta, Hafsat ta dubi Ikhlas tace"To yanzu sai yaushe zan gan ki? ",murmushi Hafsat tayi tace"Sai nazo gashi tukunna".
Wanka ta shiga,tana fitowa Ikhlas ta tsantsara mata kwalliya,riga gown fitet brown colour ta saka.
Ikhlas ta daura mata rigar saman wacce ta kasance net light brown mai haske,Turare ta feshe ta dashi.